Sashe 54
Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
suka taru aka daura Auren Cele da Ahsan akan Sadaki Million Daya a kudin Nigeria,Cele kuwa tayi gayya sosai ranar da yamma takari suka dinga layi,Ahsan ya kama musu wani joint an gasa raguna ga su Madara da kayan ci iri iri Kaci iya cinka ka barshi,da kanka zaka eba ka yanki rago a bankare,Takari banza ta fadi bakin kowa da maiko,Cele taci gayu cikin Arusa rigar Amare fara komai fari an mata make up gashi rigar da kalar mayafinta ta musulman larabawa sai tsada,Kidan labarawa na tashi a wanjen ana laftar raguna,Babu Namiji ko daya a wajen tunda walima ce amma Kaka yana wajen shi yaja gefe yana ta kwasar gara ko magana baya yi,Sai dare suka gama Ahsan Yazo da Kansa ya sha kayansu na larabawa harda Dora Alkyabba golden color irin shigar masu kudin larabawa,Sun zuba pics iri iri,Ahsan yana daukan Cele yace yau tare zasu kwana,Cele tace a'a wallahi ban yarda ba ni,ta fututtuke masa ita bata yarda ba,Ahsan yace mene aciki Matata ce fa ke,Cele tace wlh ban yarda ba ni gaskiya azo ayi min kaca kaca na tafi gida da rubabben fada baza ta yuwu ba,lah..lah.Ahsan yayi murmushi yace to ko romancing? Cele tace zero wallah kayi hakuri kazo can mu gama shirya komai sannan,Ahsan harda wa'azi wai ba kyau ta guji mijinta,Cele tace daga baya sai ka yafe min, wallahi Yasin Ina sam Alqur'an bada ni ba,tana nunawa da hannu, parking yayi a kofar gidansu,har tasa hannu zata fita sai Kuma ta fasa ta juyo ta turo masa baki tace ungo yi kaji,ka ganka harda wani komawa maraya da Kai, ta fada da larabci,yayi dariya ba musu kuwa ya tallafi fuskarta a hankali yana tafiya a hankali da fuskarsa zuwa tata,Cele tace ah naga ta kaina komai sai anyi cikin sanyin jiki haba Salihu komai style baza a tafi straight ba,a dinga komai da jiki,na auri iyayen soyayya ya zanyi dole na koya nan ba kaskon suyar Awara bane ba fa,dole Ina komawa na tafi wajen Nazifa ta koya min slow motion Nima,bakinsa ya hade da nata ya fara mata wani irin kiss na mussamman,Cele tace eho kaji kaina wani yammmmm,duk da bai gane hausar ba yanda ta danyi ihun ya bashi dariya,yaci gaba ta sake janye bakinta tace taratsatsi akeyi a cikin kaina ta rankwashi kanta tace muje zuwa Malam Hafizu,a soyayyar ma Kai Hafizi ne ja muje,Ahsan yaci gaba Cele ta sake kwace bakinta ta sheke da dariya harda bugar jikin motar tace Allah Dadi shegu ashe haka ake ji,ta sake conowa Ahsan baki ,yanda tayi sai da ya dinga dariya,tace wallahi Fada wani zuut zuut take ta karbi kidan,suka ci gaba da kiss Cele harda tafi tace yau Ina karbar darasi wallah yo in da wannan ai masifar ma dainawa zanyi,sai da yayi kissing dinta yanda yake so duk Cele ta zurma ta zauce a kiss kawai,zata tafi harda manta Jakarta sai da ya sauke glass ya Kirata ta dawo ta dauka suka yi Sallama yana ta murna kamar an sashi a Aljanna. Cele da gudu ta shiga gida kaka Yace ya akayi har na rigaki zuwa gida tun dazu Ina kuka tsaya ne? Cele tace Kaka soyayya muka yi,Kaka ya Dafe kirji yace ki bari sai an kaiki dakinsa,Cele tace ai dama ta wuce bedroom ta fada saman bed dinta tana ta murna harda tsalle tace wayyo Allah dadi kashe ni,Guy nan ya hadu matsiyaci kaga kiss,jikin mudubi taje ta tsaya tana kallon bakinta tace ya bani ta nan ya bani ta can a'a,Gaskiya kullum sai munyi,boobs dinta ta kalla ta lumshe ido tace sai naji Ina so a taba su,to Kai kuyi hakuri sai next time ku dai abinda nake so da ku shine ku cika masa hannaye kunga dai tsohuwar matarsa tana da su karku bani kunya kunji yawwa, ta baya baya ta ja ta fada a saman bed tace yau bazan iya bacci ba. Washe gari Ahsan shi ya Kai su Cele Airport da kayansu,a mota ma sai da suka Kara kiss amma kadan tace sai kazo suka tafi Yana daga mata hannu ,sai da jirginsu ya tashi sannan Ya koma gida Shima zuwa dare ya koma Riyad,Maheerah ta haukace jin labarin Ahsan yayi aure tace ba a Isa wata ta shiga gidan ba ta dauki alkawari. Mami ce ta shigo da niyyar duba Auta taga ya jikin nasa ta same su a tsaye yana faman lagudewa Salma duwaiwaka tana cewa nan haka nefa,Karar Bude kofa suka ji da sauri Auta ya sulale kasa yana taba kafarsa yana cewa har yanzu kafar nan bata karasa warkewa ba,Salma itama ganin Mami da gudu ta duka tana cewa Sannu ai sai a koma asibiti,Mami juyawa tayi tare da rufe musu kofar su tana mamaki,tana fita Auta yace na shiga uku,Salma tace Kai tafi can dama ba abin kirki kake min ba tunda gashi nan kaji tsoro,Auta ya harareta yana kallon hannayensa yana cewa daga gyara sai ya zama abin tsiya,tace ae Karka sake taba ni bana so,ta juya ta fice abinta. Tana fitowa suka yi Ido hudu da Mami a zaune tare da Miracle,Sosa Kai ta fara tana maurmushin borin kunya tace Mami Auta gaskiya yana jin jiki sai an dage a Kansa,Mami tace au haba?tace uhm ta zauna tana kame kame Mami yaushe za ki min kitson? Mami tace sai gobe tana ganin kinibibi a fili,dariya tayi a ranta Kuma ita Kam taji Dadi,Miracle tace Salma kina da gaskiya kuwa sai wani soshe soshe kikeyi,da sauri tace Wallahi Aunty Ina da ita ba abinda muka yi bamuyi komai ba,Mami tace kawo min ruwa a kitchen,ta tafi da sauri dama kadan take Jira ta fece. Miracle ta dawo gaban Mami da kwana sabo da cikin,Nawwar ya hanasu sakat da sintiri watarana ma a nan yake kwana, yau Monday Nawwar yana Office daga ita sai Mami a Palo tana jin ciwo sama sama tace Mami wallahi kamar nakuda nake yi,Mami tace haka ake nakudar lallai baki San nakuda ba ai sai kin tubure mana tukun,Rabi tace to ta tashi da kyar ta shiga bedroom ta kwanta ciwo ya fara maguzata bayan awanni tun tana daurewa har ta gaza ta fito fakat daga dakin tace Mami har yanzu ban tubure din bane? Mami tace ahhh kin tubure kwarai kuwa nakuda ta kankama bakya hayyacinki tunda kika ce haka muje asibiti,a wajen ta tsuguna ta dafe mara tace wayyo Allah, La'ilahaillallahu kasusuwa na suna farkewa suna budewa wayyooo shike nan kasusuwana sunyi warka warka,Salma ce ta fito ta rike Rabi kamar itace zata haihu wayyihuhu jama'a ku kawo agaji,Auta ne ya fito sanye cikin jallabiya,Mami tana hado kayan haihuwa,Auta yana zuwa ya dauki Rabi cak ya fita da ita har cikin mota Salma ta fito da gudu tace ni zan karbi haihuwa ta shige gaban mota,Auta ya rude ya manta ya tafi ya bar Mami,tana fitowa su har sunyi nisa,Salma ta cikin motar ta tsallaka baya tana dannawa Rabi ciki tana cewa daure,cije,manne,ke kamar ba mace ba Nawwar da kike Kira me zai Miki kyale Nawwar ki Kira Allah. Rabi ta samu Salma ta kankameta tana jijjigata ta buga kan Salma da jikin glass din mota sabo da azaba tana cewa wayyo Allah Nawwar wayyo zan mutu,Salma ta dafe Kai tace ka Kira Mami zata sumar Dani,Auta ya dinga dariya yace uban wa yace Miki ana zuwa a dinga yiwa me nakuda katsalandan,Salma zata gudu Rabi ta riketa Kam tana cewa Idan kika tafi mutuwa zanyi wayyo Allah,Salma Idan kika tafi mutuwa zanyi ki rikeni ta Miko hannu,Salma ta riketa Rabi ta fisgi Salma kamar zata karyata,Salma ta fashe da kuka tace Nima zata aikani lahira,Mami sai driver tasa ya kaita can,Auta ya kirawo su Star kafin kace me duk sunzo har Wise,Nawwar kasa driving yayi sai Auta ne yaje ya dakko shi,gaba daya ya haukace ya rude,Santana har da shi ya wani falfalo yana wayyo miracle yau za a yabawa aya zakin ta,da a baya ne ai nine zan karbi haihuwar lokacin Ina Hajiya Santana ta,yanzu kuwa na koma Kai maimakon ke. Kuyi hakuri wallahi bani da lafiya zabbabi nake malaria da kyar nayi typing. AsmaBaffa 08061929616 'YAR AIKIN KARUWAI 2 MATAFIYA BOOK 2 66-70 Official AsmaBaffa SADAUKARWA GA ZAINAB USMAN Adashin kudi kamar haka 20k kwasa 200k Slt 1 2 4 7 8 9 10 30k kwasa 150kslt1 2 4 6 8 9 10 50k kwasa 500kSlt1 2 3 4 5 7 8 10 10k kwasa 100k Slt2 3 2 4 7 9 10 Mebukata yaneme wannan numbern 09049197049 Munayin adashi kamar haka Kayan daki set na kujera da gado Kayan kitchen Freezer fridge Injin wanki Dasauransu 09049197049 Page naku ne Ummu Minnah Ummu Annur Aunty Nurse Zariah Princess Maman Ahmed Mrym Maman Aslam an Abdul Mamar Bintou Ummey Muhammad Maman Murtalah Sumayya Auwal Ummu Lateefah Mommy Sadiq Ummin Sadeeq Ina gaisuwa Santana sai safa da Marwa yake kamar matarsa,yace yanzu ba dama a shiga,Nawwar ya watsa masa wata uwar harara ba Shiri yayi mukus,Mami har Salma ta Koro waje,duk suna waje,na danji dama dama tace a turo min su Wise, kunyar nake ji suruka zata kalleni ni gwara su Wise,ciwo yana dawowa nace ni bana son surukata ta ganni,Mami tace ashe kuwa sai in baza ki haihu ba su sun San haihuwa ne,Rabi ni dai sai tattale kafafu nakeyi,na mike daga kwanciyar na sakko kasa nayi goho nace a haka zan haihu irin tamu ta gargajiya,naji wahala nace wallahi ta asibiti zanyi na dawo na kwanta akan gadon ina bude kafa,ban San sanda ma na cire kayan jikina ba ina tattale kafa,kan yaro ya taho yaki fitowa sai ya fito ya koma,likitoci suka zo suka agaza har ya fito,sai kuka inya inya,Su Wise suna ji sai shewa yeeeeeeeeeeee,Nawwar ya harare su yace ai Kwa bari dai aji lafiyarta ko, nan da nan aka gyara Miracle ba kayan komai a jikina wahala tasa na cire,ta hada gumi sharkaf duk,na manta ma da suruka na nan,sai da aka gyarani tsaf aka gyara dakin neat nurse tace Hajiya sai a sa kaya ko,kunya ni Miracle naji Mami an goge jariri an nade shi aka Mika mata,ta mika min zani tace gashi maza ki daura daki za a canja mana sai ki wanke jikinki mu tafi,nan da nan aka canja mana daki,abinka