Sashe 90
Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kaka kuwa bayan sunyi Umrah dukkansu Cele tace suzo su wuce Riyad yace a Dan Jira yaje wajen abokansa na garin Makkah su gaisa,Cele tace kuyi sauri Kaka Dan Allah muna jiranku a masallaci harami, Kaka da Amarya Zuwaira Mama suka fito suna tafiya cikin nutsuwa Basu san wani kazamin kame ake yi ba,har gida gida ake bin ko wanne takari a kama su,gidan da Cele ta taba zama su Meenal har gida akaje duk an kamasu an kashe musu passport baza su sake shiga kasar ba an dawo dasu Nigeria sabo da haka ko sun dawo Makkah ana Shigar da passport dinsu computer zai nuna an dakatar da su daga shiga kasar,duk Wanda suka kama da laifi a kasar haka suka masa,sabo da haka takari da yawa duk an tsince su,Suna tafiya Kaka ya hango gungun askarawa shi ya San kwanan zancen Mama ce dake bata taba takarci ba bata San komai ba,ya juya da gudu ya bar Mama sai da yayi nisa ya kwala mata Kira Zuwairaaaaaa tashi injin kafarki, bawa kafarki wuta ki taho a millionnnnnnn,Mama taga askarawa sun dumfarota gata da kiba sai gudu, tabi Kaka sukub sukub da kyar take gudu Allah yasa suka Dan buya a wani lungu sai da Askarawan suka koma sannan suka fito suka koma wajen su Cele suna basu labari,Kaka yace Zuwaira ga kiba inda kisan tana taka soson katifa sai ki rantse akan soson katifa take gudu sukuf sukuf,Cele da Ahsan suka dinga dariya,yace ai baza su kama ku ba da Kun nuna musu wannan abin,Kaka yace Kai rabu Dani haka kawai tsautsayi yasa ance masu shedar zama ma a kasar duk sun kame su,Ahsan yana ta dariya yace su tashi anzo daukansu,Driver Yazo da mota aka kaisu Airport suka wuce Riyad. Ahsan a gidansu ya fara sauka a dankareriyar farar mota driver na jansu daga airport,gidane hadadde Yan uwansa larabawa maza da mata suna ta murna ana tarensu,wasu a ciki Basu so ya auri ba Yar kasar ba wasu Kuma ba ruwansu,Cele tana rike a hannunsa suka shiga katon Palo ya gaji da tsaruwa,ga girki kala kala an shirya, masu son auren sai rungume Cele sukeyi da Ahsan suna musu pics,Bayan anyi gaisuwa irin ta larabawa Ahsan ya gabatar da Cele ya Basu labarin abinda duk ya faru tsakaninta da Maheerah har auren Cele,Wanda basu so aka auri Cele ba ma a nan suka narke suka koma Sonta,ya gabatar da kowa nasa a wajen Cele sannan aka ci aka sha duk da cewa Kaka,Mama da Cele ba komai suka iya ci ba,Basu Saba ba suna haka sai ga Maheerah ta shigo tana balbala masifa anci Amanarta,Cele ta mike tsaye tace sai ma an Kore ki daga aiki Zaki San an ci amanarki ta fada da larabci,Maheerah tazo ta cakumi Cele,Cele ta kwasheta da gigitatten Mari ba shiri ta saketa,Larabawa sai Subhannallah Subhannallah suke furtawa,Ahsan yaji dadin hakan da Cele tayi,ya rike hannunta dama a tsaye take ta mike zasu tafi ya jata zasu shiga mota Maheerah tana kuka ta zube a kasa ta rike kafafun Ahsan tana bashi hakuri,Cele ta hankadeta suka shige mota da su kaka suka wuce gidan Ahsan sabon gidan da ya canja a wani layin daban na masu hannu da shuni,gidane na gasken gaske yaji kaya komai me tsada,Cele tana ta uban murna,yana shafa cikinta yace gidan yayi? tace komai perfect,sai me aiki Cele tace a'a ni zanyi komai da kaina Ina wani aiki a nan garin da ba kura, daukanta yayi suka wuce Bedroom suna soyewa,Cele tace Antena Dadi,yayi dariya sosai yace amma da kince zafi,Cele tace na tuba dama a farko ne nace yanzu na gane gaskiya na tuba ranki ya Dade karya nake wane mutum,Kaka kuwa yana bedroom din da Ahsan ya Basu shi da Mama yace da Mama azo a Adana ni,Mama tayi dariya yace amarci zanyi a Saudi yau sai na ajiye tarihi. Bayan haihuwar Wise da wata Daya Star ta haifi yarta mace taci suna Nawwara wai sabo da Wise tayi Nawwar shine ta Saka Nawwara,Ba a dade ba Seraline ta haifi Namiji itama yaci suna Ahmad,Yar Zabil da Mandula kuwa sai bayan wata biyu Mandula ta haifo Mace taci Sunan mamanta Aisha suna ce mata Waheeda,Sai Yar Zabil bayan sati biyu da suna ta haifo Namiji itama aka Saka sunan babanta Usman suna ce masa Aabeed. Salma kuwa cikinta yana ta girma sosai sai gani akayi ya fito a hakan ma boyewa take yi Idan zata je unguwa hijab har kasa kowa yasan da cikin amma sai boyo suke ita da Auta,Yau Auta yana wajen Mami tace Idan kun gaji da boyon ai cikin ya tsufa sai ka dawo da ita gida nan ta haihu,Auta yace wlh ni bazan iya barin Mamatata ta dawo nan ba,ni na karbi haihuwar,Mami ta kalle shi tace munga Rabi ma me boyon nono,Auta yayi dariya yace kawai a raba mutum da matarsa ayi ta gargajiya ni bazan yarda ba,Mami tace Karka dame ni Kuma kaje Allah ya bada sa'a yace Ameen . Salma tana ta tiri tiri da ciki gashi ya tsufa sosai,Auta yace ya dai ya kalleta tana hawaye tace Allah cikin nan ya isheni wlh hakuri kawai nake yi,Auta ya fara lallashinta yace sorry Autana kin kusa ai Yana shafa cikin tayi Turus a zaune tare da mike kafafu. Cele kuwa cikin yana shiga watan haihuwarsa cif cif sai gata sun dira a Nigeria ita da Mama da Kaka sai Ahsan,lokacin an gama musu hadadden gidansu na gagara,Kaka da Mama anyi kiba anyi jajir,Cele da Ahsan ma haka,Kaka suka sauka a Kaduna gidansu har Cele sai da suka zaga dangi sannan Ahsan ya dauketa suka dawo kudu a jirgi,Gidansu nasa Yan aikin sun gyara an zuba furniture da komai na haduwa an shirya musu kawai tarewa suka yi a gidansu abinsu. Kusan kullum Ina ziyarar Cele sabo da cikin ya tsufa,nace gaskiya ya kamata Uwa tazo ta zauna da ku,Cele tace wacce Uwa ga Mama matar Kaka zasu taho gobe,nace Allah ya kaimu ai yafi Idan da manya,nace kinji Omaira tana da ciki Omar dinta ya Bude mata shagon boutique,Cele tace ta fada min. Cele ta budewa Kaka shagon siyar da kayan Masarufi sannan ta sake gyara masa gidansa sosai,sai su Bilkisu ni da Cele mun hada kudi mun Basu jari babba suna juya abinsu, komai Alhmdllh kowa Yana zaune lafiya da yaransa Babu talauci kowa da rufin asirinsa dai dai gwargwado. Mairo ta shirya bayan ta yaye yarta ita da D agaci da Gwaggo da Gaji suka samu Iyayen Najib bayan sun gaisa suka ce yarku muka kawo,Najib aka Kira Yazo ganin Mairo da yarsa sai hawaye ya durkusa a gaban Mairo yace ki yafe min Dan Allah,Mairo tace ba komai na yafe maka Albarkacin yarka gata nan sunanta Madina,Najib ya dauketa sannan ya fara rokon Mairo akan ta aure shi yace wlh Ina sonki Dan Allah ki aure ni,Dagaci ne yayi magana yace sai dai kayi mata gidanta daban sabo da gudun gorin kishiya,Baban Najib yace indai wannan ne ba matsala,Mairo dai haka ta amince gwara ma ta auri Najib din ta huta musamman sabo da yarta Madina. Bayan sun koma gida ba a dade ba suka kawo komai na aure aka sha bikin Mairo itama aka kaita gidanta Dan madaidaici me kyau itama ni na mata kayan daki dukkan su sunci albarkacina Yar tsuntuwar da suka raina tayi musu rana a duniya Maheerah kuwa asibitin da take aiki Ahsan yakai kararta suka koreta daga aiki gaba daya,tayi kuka tayi bakin ciki gashi Ahsan ko saurarta bai yi,kwarton nata ma sunyi fada gashi su can ba a samun Miji da wuri ta rasa Mijin aure sai gantali a gari kawai bata a tsuntsu bata a tarko,in Banda tarin nadama da Dana sani ba abinda take yi a rayuwarta. Yau cikin dare Salma tana kwance ta tashi ta zauna ta tashi Auta tace Auta ka tashi Dan Allah zan mutu kana ta bacci ai gwara na cika a gabanka,Auta ya tashi yace ko dai Nakudar ce ne? Salma tace itace gaskiya ni ban taba jin irin wannan ciwon ba,mu Dan Kara Jira ayi Sallah sai mu tafi asibiti,Salma ce ta sakko daga kan gadon tana rike mara tun tana Dan kokari har ta kasa tace Autaaaaaa da karfi yace na'am kamar abin arziki tace Auta ubanka,wayyo Nawaf zanci Ubanka,Auta yace ba lafiya mata ta zagi mijinta me Antenar ban girma, tashi mu tafi ya dauketa da tarkacen Salma da suka hada abinsu na haihuwa sai asibiti,Auta yaki fadawa kowa Kuma suna asibiti tun asuba har yayi Sallah rana ta fito Salma bata haihu ba,Mami ta kirashi da hantsi amma bai fada ba yace lafiya suke,sai 12pm sannan Salma ta haifo yarta mace katuwar gaske kyakyawa,Sai da aka gyarata Auta ya shiga ya dauki yarsa yana ta jin Dadi yana uban murna ya rasa inda zai sa kansa,sai da Salma ta huta ya fita ya samo mata abinci take away taci ta koshi yamma karfe hudu aka sallame su,Auta yana zuwa ya hada mata ruwan zafi da kansa ta shiga tayi wanka,ta fito ta shirya cikin doguwar rigar material marar nauyi ya Mika mata turaruka yace shafa jego sai da turare tayi dariya,yace gashin nan iceko ya wanku fes tana taje gashin tace wlh bani da karfi komai karfin Hali nake yi kasusuwana sunyi rugu rugu,Auta yace a Kira Mami ko Zaki iya yiwa my Lovely Baby wanka?Salma tace na iya ya hada ruwan suka wanke yarsu mutum biyu akan jaririya daya Auta ya riketa Salma tana wanke ta,Auta yana cewa a hankali karki daye mata fata na shiga uku Yar nan kamar raina haka nake jinta ki goga a hankali,a haka suka mata wanka harda mata ruwa biyu wai tafi fita,Auta ya zubar da ruwan ya sake wanke toilet din,Yazo ya gyaran gidan neat yayi wanke wanke sabo da tun dare suka tafi duk da ma gidan ba dirty sharp sharp ya gama komai yayi wanka ya fito ya shirya cikin jallabiya arsh yana kamshi,Salma ta shirya yarta harda hada garwashin wuta dama sun tanadi gawayinsu,Auta ya dawo ya zauna yace ya kama gawayin? tace gashi yayi Jajir tana fifitawa da littafi,yace a gasa mata cibin,suna ta faman gashi ba ji ba gani Auta yace ayi mata sosai