Sashe 36
Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gashin na kanka da ka masa wani aski mu a nan easy dai easy dai abokina Allah wallahi,Auta yayi dariya yace Sabreen tazo ga Dan uwanta wannan ya girmi kanta,Umar Baso yace yawwa wani Deal zamu yi,kai kaga da Alama kana da kudi,ni so nake na samu kudi na alkinta rayuwata gashi gyaran machine nake yi,Dan Allah Oga ko zaka lallaba ka rufa min asiri? Zabura yayi ya sake ja da baya yana gwadawa da hannu yace kaga master asiri zaka rufa min ya sake kankame hannayensa kamar me jin sanyi ya makale a jikin Katanga yace wani taimako zaka min kaga kullum sai na roki kudi wajen me duka kaga na roki trillion dari,billion bakwai,na dawo million talatin, na sauke farashin zuwa dubu dari biyar,dubu dari,dubu hansim har na dawo dubu biyar to abin sai godiya kudin sunki zuwa,jari nake nema Dan Allah ko zaka siyi Salma ni ka siyeta duk yanda zaka yi kayi da ita,Idan ma za a iya maka aure kazo na baka ita ka bani million daya gata nan. Auta yace ba ruwana ya juya zai tafi abinsa amma Umar ya tare masa gaba yana karkace baki yace ya haka yawa kake Oga haba abokina,haba Yayana to ka aureta ka bani dubu dari biyar,kai dubu dari uku ma ya Isa ai baza tayi tsada ba tunda ba a gidan masu kudi ta taso ba,Nawaf yace to naji kawai ya furta sabo da ya kyale shi ya tafi,yace Yayana bani number ka zamuyi Business din ko baka gane bane ey kar ka Yi mini ae yane ka gane,Nawaf ya bashi number dinsa suka rabu Umar Baso yana ta uban murna zai rabu da kaya ya huta ga kudi zai samu,Nawaf Kam Airport ya wuce yana tunanin lamarin Baso shi Kam ba ruwansa bazai iya ba zai Jira dai Sahar dinsa. Bayan ya koma gida da kwana daya Baso ya addabi Nawaf da Kira a waya Nawaf kuwa yaki dagawa abinsa ya share Kiran yaki dagawa Sam. Yana dakinsa a kwance Mami ta shugo tace gobe dai kasan zaka fara zuwa University an gama komai ko? Yace ae na sani Mami,kallonsa tayi tace ko tunanin Sahar dinne? Kai ya daga mata wai ae ya furta please Mami kije ki ji min ko zasu yarda ni nafi sonta,hmm amma Idan naje suka ce a'a shike nan ka hakura? Yace ae na hakura amma kije,to shike nan cewar Mami. Bayan kwana hudu Mami ta shirya tare da Nasira da Sultana suka siyi kayan kwalliya masu kyau da turaruka driver ya tafi kaisu da yardar Baffa. Mami suka ga gidan su Sahar masu kudi suma,iso aka yi musu,Sahar dince ma ta tarbe su tana Palo tana kallo dama Nawaf ya fada mata sun taho,taci kwalliyarta sosai ta sha Atamfa me tsada,har kasa ta durkusa ta gaishe da su Mami tace bari na Kira Hajiyanmu ta haura sama da sauri,tana uban murna Hajiyansu tace sun zo kenan? Sahar tace ae,shi yasa naga kina murna kamar Zaki tashi ki sani wallahi baza ki auri wannan yaron ba yaro karami wani aure zai iya rikewa,ga saurayi na kirki babban mutum me hankali me kudi na Kansa ba Wanda ya dogara da kudin Iyaye ba,wallahi Idris Zaki aura nutsatsen yaro ni da mahaifinki ma ki sani baza mu yarda da wannan yaron ba karki ce ban fada Miki ba. Hajiya fitowa tayi wajen su Mami da fara'a suka gaisa sosai,sunyi hira Mami tace dama akan maganar Nawaf ne da Sahar...kafin ma Mami ta rufe baki tace ai an Riga anyiwa Sahar Miji Idris shi zata aure,ina Sahar ina Nawaf wannan ai yayi kankanta sai dai karatun ai,ya tafi Makaranta wannan ai Gigi ne na Yara haba Kuma sai ku biye masa shirme ne wannan,Baban Sahar ne ya fito zai fita Hajiya tace Mamin Nawaf ce yaron nan da aka dinga rikici da shi yana hurewa Sahar kunne,to...to.to Allah sarki ai kin fada musu anyi mata Miji Ina Sahar ina wannan,Sahar tana gefe ta labe tana kuka wiwi bata da bakin magana face kawai ta kyale Nawaf yayi kokari yayi iya yinsa,Mami ta gama jinsu irin rashin iya magana ta iyayen Sahar tace ba komai Allah ya hada kowa da rabonsa suka ce Ameen suka watse suka bar su Mami su kadai a Palo da ruwa da lemo a gabansu,Sahar ce ta fito tana cewa Dan Allah kuyi hakuri,ba komai wlh baki da laifi ke amma kinji abinda suka ce kiyi hakuri kiyiwa Iyayenki biyayya Dan Allah karki sake Kiran Nawaf ku hakura da juna Allah bai so ba. Sahar tana goge Kwalla ta raka su Mami har mota suka bata abinda suka kawo mata tayi godiya ta koma ciki bata da bakin magana iyayenta sun gama da ita. Mami tana komawa Nawaf ya tareta a Palo yana tambaya Yaya? Mami ta Mika masa waya tace ji da kunnenka shi yasa na maka recording sabo da Karka dameni,Nawaf ya kunna ya gama jin komai a kunnensa Sultana tace sai kaga ma irin wulakanci da suka mana wallahi Auta amma Sahar bata da laifi,Nawaf yace sai na Riga yar tasu aure inshallah auren huce takaici zanyi,Mami tace ko kai fa kayi hakuri ka nemi wata amma tare da bikin su Sultana za a hada da naka tun wuri ka nemo mace wlh ko mu zabo maka ni da Baffanka,Auta yace yanzu Mami ai dai sai ku bari na huce ko ku sanda na hadaku kuka shirya haka nayi muku? Auta zaiyi hawaye yace Mami daga cewa ina son aure shike nan sai kuce ko ban samu wacce nake so ba zaku zabo min Hakan yayi kenan? Baffa Shima ai ba haka mukayi da shi amma Yaya Nawwar shi kuka kyaleshi ya zaba ya darje ni sabo da bani da kudi kune zaku min komai shine ni za a min auren dole,Shut up Baffa ya furta da shigowarsa kenan yana murmushi yace Auta kana bukatar aure bama so ka fada wani Hali ka nemo to mun baka zabi kafin bikin Su Sultana Idan ba haka ba mu munyi maka mata ma,Auta bedroom ya shige kawai abinsa ya bar Mami da Baffa baki Bude Cele tunda ta sauka take garari tana zaga unguwar ta rasa ina zata shiga har gari ya waye inda taji Kiran Sallah nan ta nufa,masallacin bangaren mata tayi tayi fitsari ta fito tayi Alwala tare da Sallah sannan ta fito taci gaba da tafiya har rana ta fito mutane ana ta hada hada,Cele yunwa ce ta ciyota ta shiga wani Dan waje inda ake soya kwai da tea,tana shiga tace da me Kwan a soya mata guda biyar,shi dai yayi mamaki mutum shi kadai haka ya soya biyar ya cinye,tace a hada da dankalin turawa sai bread da tea aka zuba mata komai,inda aka tanada na cin abinci ga me ci a wajen, nan ta zauna taci ta koshi tayi tafiyarta,balaraben yana ta Kiranta da larabci Hajja amma ina tayi tafiyarta sai da ya fito da gudu ya riketa Cele tana juyowa ta mareshi gauuu ta fara masifa da Hausa aikin banza na zaci ma a kawo Kaduna nake,jiya ai ta malali na wuce na shugo ta unguwar sarki ashe nan a unguwar Rimi nake ma Dan wulakanci zaka rike ni Abuja zan tafi,ta kwaso kudi da yawa ta watsawa balaraben tana masifa tace ku dama yan kantin Kwari baku da mutunci indai aka zo sarin kaya sai kunyi wulakanci aikin banza kano dinma zan bari gaba daya tayi gaba,tana tafiya taga masu gasa kaji ta karasa wajen tace akwai kifi na sukunbiya? Ko yan gezu ba Wanda ya kulata,ta dauki hanyar harami tana Maheerah Kiji tsoron Allah,Kaka ya dawo daga masallacin kaabah ya kwana yana addua a hanya yaci karo da mutane sun rufe wani waje wai wata ce a Nigeria ta bata sannan bata da hankali mahaukaciya ce,Bai San Cele bace yayi tafiyarta yace su karanta sai naje askarawa suyi ram Dani yanda nayi kiba nayi jajir Dadi haka nada ni ba. Mutane suna ta zuwa inda Cele ta fadi tana birgima da Shure Shure tace cewa wlh sai na soya Awara. Haka ba Wanda ya saurari Cele sai wata mace wacce ta Dade a kasar ta dauki Cele tana zagawa da ita gidajen takari mata da maza ko an Santa har ta zo laying su Kaka,lokacin Kaka juya baya a layin yana siyen kwai dafaffe wajen takari suka ga Cele ta kwace da gudu ta nufi wajen Kaka ta rukunkume shi ta baya tana murna tana cewa Kaka, Cele da karfi Kaka sabo da bai shirya ba ya fadi a kasa wanwar sabo da karfin Cele gashi ta wani yi tsalle a jikinsa,kaka ya juyo yaga Cele dinsa, ya fara cewa a'a a'a Cele ta ya rungumeta suna murna,lokacin Cele ta dawo hankalinta kanta ya Bude kwakwalwarta ta dawo dai dai,tsalle take tana murna Kaka ma haka ta saki kuka Kuma daga baya da ta tuna da Ahsan. Tace Kaka yace Cele kyale labarin nan mu koma ciki kawai ya rike hannunta suka shiga lifter zuwa bangaren kaka har dakinsa,Zama sukayi a gefen gadon kaka Cele tace Kaka ji yanda ka sake yin wani kyau da kiba kayi jajir, kafar Kaka ta kalla tace ina kaushinka kaka? Yace ya gudu Cele dole kiga nayi ja ga Zaki ga maiko kullum a cikinsa nake Cele ta,Kaka mu sake rungumewa suka sake rungumewa da kaka karo na biyu sannan Cele tace Kaka Ina yini tana washe baki murna ta isheta Kaka ya amsa yace lafiya kalau 'yata ta kaina,kaka Nawa Cele ta furta,kaka ya saki shewa kamar mace heeeeeeey wuuuuuu ya Mika mata hannu suka tafa,Cele tace Kaka na bayan hannu mu tafa dukkansu suka juyo da bayan hannu suka tafa,Kaka yace Cele ni sai naga kamar kin kunkunbura wallahi kamar baki da jini inda kisan haihuwa kika yi Cele kalau kuwa? Cele ta tuna dake kwakwalwa ta dawo tace Kaka labarin dogo ne Kaka bakin Abba ne ya bini da yace sai nayi ciki,Kaka kirji ya dafe yace Dan ubanki ba dai kafa kika budewa wani ba. Cele tace to ka tsaya mana kaji labarin, ta kwashe labarin komai da komai tun sacewarta har zuwa yanzu data gudo karshe tace Kaka makuwa nayi kaina sai naga ya juye na rasa a Ina