← Book details Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 93

Sashe 49

Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

komawa cikin ukuba,Khaleel yayi dariya yace to Umma fito ki ga motarki, ta fito suka zaga ta baya taga mota lafiyayya ta kirki me kyau arsh,ta shafa motar tace Allah yayi masa Albarka tana goge hawayen murna tace mutumin kirki Zaki dauka driver ya dinga tuka ki,Umma zakwkura ce tace na koya dai ai Koya zanyi Dan nan da lafiyata da komai,yace me aikin gida fa? Tace sai na aurar da su Omaira kaf sai a daukar min me aiki,yace to shike nan yana gamawa ya tafi,Umma kin komawa tayi shuru Uwa suka ga bata dawo ba ga Yara su Bilkisu sun dakko kurkura suna ta kwashe kayan sawa Dana abinci sauran tarkacen kayan dakin Umma kuwa Omaira ta fito tasa kafa tayi ball da tukunyarsu ta girki ta daki wani bahon wankan su tace Dan ubanku ku lalace tace Uwa ga kwance ne Kya dinga yiwa danki girki tunda bakwa son mata mu Allah ya mana tashi,Ku tashi ku tafi gidan uban wa ai nan ne gidan ubanku dole ku zauna ita uwarku duk inda zata taje to taje cewar Abba yana bakin ciki yaji Umma ta samu gida hadadden ga Alheri daban daban,Omaira taje gaban Uwa ta buga skert dinta da hannaye biyu tace a kada Miki buje a haka Zaki kare ta juya tayi fatali da wani tire dinsu ta bar gidan,Abba yana kallo wato shi baza su iya masa rashin mutunci ba sai uwarsa, Su Rahma suka tafi su tuni sunbi motar kaya,Omaira kuwa ba rawar da bata yi ba a gaban su Abba harda galala da kafafu ta fice,sai kallon gidansu suke suna Murna,Aunty Rabi taci sunanta Miracle wallahi cewar Omaira, su Bilkisu a sabon gida suka yini suna ta kallon motar Umma. Mairo zuwa yanzu a Hannun Mahmud ta jigata duk kuwa da abinci ta rame tayi duhu Dan man da take shafawa baya bari taje ko kofar gida ya kare tayi uwar Rama,yarinyarta kuwa tayi bulbul da ita,kullum Mairo a kuka take gashi ba dare ba rana sex yake da ita yana jin dadinsa kamar me,Mairo Addua ta koma Allah ya kubutar da ita ta huta,yau yana dawowa ko hutawa baiyi ba ya fara tube kayansa,Mairo hawaye ya zubo mata ko a jikinsa ya fara shafata Babu nutsuwa gagagaga ya shigeta,Mairo azaba tasa ta jawo kwalabarta data fasa ta boye a kasan gado tace sa masa a wuya tace sake ni Dan babarka suka fara kokawa zai kwace kwalabar Mairo ta Yanke shi da ita a Kansa,balarabe yaga jini ya saki Kara,Mairo ta fara Aljanun karya kamar gaske ta hau Aljanu ta barbaza gashinta tana ihu da hauka tana fari da Ido tana kafkafkaf kamar me fyarfyadiya tana gurnani,tsorata Mahmud yayi gashi da tsoron mutuwa Nan take ya saki Mairo duk da haka Sai da ta kafta masa yanka a hannu da kwalaba ya rike hannunsa yana Kara, ta dauki yarta ta fice da gudu Allah yasa yana sauri zaiyi sex bai ko rufe kofar ba,Mairo ta fito tana falfala gudu kamar za a kamata tana gudu tana kwarara ihu a gari ko wanne takari yaga Mairo sai ya kwashe da gudu Shima ya Kara gaba,tana gudu Cele tana siyayya taga mutane radada ga Mairo tana ihu fasa siyayyar tayi ta fito ta kwashe da gudu,Kaka Allah sarki ya dawo daga masallaci da sallayarsa yaga takari yuuuu suna uban gudu Shima yabi sahu sai ga Kaka cankal cankal da kafafu sirara, Yazo ya wuce su Cele,Cele ta tsaya cak tace Yasin bani da amfani tunda kaka ya fini gudu,Kaka kamar guguwa haka, taci gaba da gudu har cikin gida tace wlh sai mun bar garin nan wannan masifa da me tayi kama kullum mutum a gudu,Mairo kuwa sai da ta zo gaban askarawa ta zube a kasa tace da larabci Dan Allah ku kamani ku kaini Nigeria,dariya suka hau yi mata suka ce yau ba ranar kame bace ba a Basu umarni ba,tace Dan Allah ku taimaka wani ya boyeni ana baku damar kame ku fito Dani,suka ki yarda sai gidan Sadiya ta tafi tace wlh ko a kafa sai na tafi Nigeria,da kyar Sadiya ta lallaba ta tace ta bari tukun ayi aikin hajji sai ta tafi Mairo duk ta zauce, a zabure take ta cakumi Sadiya tace Allah ya Isa ke da uwarki tsinannu Kun jefa ni a masifa,kin san haka larabawan suke kika zugani nayi aure,Sadiya tace ahayye muka dai taimake ki,ke da kika gudu kika bar Iyayenki marar tarbiyya kinzo da cikin shege an taimakeki kina mana iskancin banza, Kuma larabawan an fada Miki kowa haka yake da sex da yawa ko a bakar fata ana samun irinsu Wanda basa gajiya sai kiga laifina wallahi sai na koreki Nima nan aure nayi gidan mijina ne kafin ya sakeni Ina caskar kudi zan Kara gaba,Mairo tace Allah ya hadaki da irin Mahmud suka yi kaca kaca daga baya suka shirya dai. Gwaggo ta warke fes sai dai yanzu tana dingisawa baza ta taba komawa dai dai ba,Dagaci an murmure Rabi tana masa aike akai Akai gashi yana ta kasuwarsa yanzu Jira suke ta haihu suje kafin bikin Gaji,Gaji ta samu Miji a cikin Kano yana da mata da yaransa uku lecturer dinsu ne a da,bikinta saura wata uku kafin lokacin suna sa rai Rabi ta haihu suna ta Shiri, yaran Dagaci mazan suna ta karatunsa suma,Gwaggo kuwa an nutsu lokaci kadan sai ta sa an Kira mata Rabi a waya sunyi hira tace Idan ta haihu zasu je. Rabi ta basu kabarin anga iyayenta ta fada musu komai tace zasu zo tare da su har gida,Dagaci sai yadawa yake a gari Rabi anga iyayenta,ance wacce Rabin? Rabi 'yata dana rike yar tsuntuwa iyayenta sun bayyana Alhmdllh zasu zo ma. Seraline kuwa ta dauke uwarta Inna ta Maida ta gidanta bangarenta daban sabo da ita kadai ta rage mata, Inna ana can itama. Gidan su Cele wasu dakunan da suke Empty sai gani tayi an kawo Yan daudu su wajen takwas gasu da Jallabiya ta maza, can babu zani baza a barsu a garin ba sai dai sunyi bleaching kwalliya suke irin ta mata duk gasu nan a Makkah Yan daudu shekara da shekaru sai su tafi can da sunan neman kudi suna daudu a can suna luwadi sun cika gari suna ta batawa mutane suna,wasu ma sunfi shekara ashirin a can. Cele tace ya zama dole na bar gidan nan wallahi wannan zama a wannan gidan bala'in zunubi sai ya shafeka,wannan wacce masifa ce haka,dole a raina mu wlh dole a daina ganin Takari da mutunci,wasu ne suke bata wasu akewa takari kudin goro amma akwai na gari, Driver ne yayi Sallama da Cele ta fito ta ganshi da kantamemiyar mota ya juyata yanda baza ta Kalli gaban glass ba,Ahsan yana ciki yana kallonta,suka gaisa tace Kaine ka siyo min botikin Awara? Sannan kana ta min Aiken kudi? Hammad yayi murmushi yace ae nine,a gaskiya na ganki Ina sonki,Cele ta kalle shi tsaf tace kayi hakuri ni zuciyata ta Saba da ganin me haske balarabe nake so ga Wanda yake jajir kullum idona Idan Ina kallonsa zasu Kara haske,Hammad yayi murmushi yace kiyi hakuri ki bani dama,Cele tace bafa zan soka ba ni Karka takura min wani nake so ni,Hammad yace larabawan nan basu da kirki,Cele tace Allah ya kona me karya Karka harzuka ni,ko Ina akwai na gari akwai na banza,Wanda nake so na gari ne,Hammad yace kiyi hakuri naga har kin harzuka,please Idan ba damuwa zan canja miki gidan zama,Cele ta kalle shi tace bada ni ba ka hada Kai da wasu larabawan a siyar dani yanda suka yiwa kaka,Yace haba dai Ina muamula da larabawa amma na kirki tace Kai ka kiyayeni munga Abila habee ma karewar tuggu,mu fa a tafin hannu mu kuke muna da tarihin garin nan abinda suka aikatawa masu Imani nasan akwai burbushin su Abu jahal har yanzu ba ruwana a Africa ma akwai nasu,ka kyaleni na bar garin nan lafiya ana aikin hajji zan tafi Idan na sauke farali,driver Hammad yace ni dai Ina rokonki Idan kina so ma zan hadaki da Yan sanda su ai baza su cuceki ba,Cele tace amma ba mutun daya ba a taho da bataliya guda ayi min kwambo da su sannan na je,yace to na gode ya juya ya mata Sallama,Cele tace jibe shi wani guntu da shi Dan banza suffa kamar gajeren wandon Kaka ta juya ciki,yana komawa mota ya fadawa Ahsan yanda sukayi yayi dariya yace ai Yan Makkah suna Shan gori a wajen baki sabo da Annabin Rahma yayi Hijira sun Kori Dan uwansu. Washe gari motocin Yan Sanda sun Kai hudu ga mota Ahsan ya bada suka zo kofar gidan su Cele ba Ahsan a wannan karon,Yan gidan suna ta murna anzo kama Cele wai ta tsokani wani balaraben za ayi maganinta,sai suka ga ta hado kayanta ta fito tsakar gida tace na gaji da kwasar zunubi kullum Ina gidan fasikai,Boobs dinta tallafe tace abuna ya huta da kawo hari yanzu zai Kara bulbul,shegu inshallah sai an kamaku Daya bayan daya sai kunyi bursuna a kasar nan,suna jinta tana masifa tace Allah yasa na hadu da wata a hanya ta min magana ko ta nuna ta sannu wallahi sai na mata daga daga,in ance a fita filin badar Kun kasa sai madugo matsiyatan banza baza Kuga Annabi ba ta fice ta barsu,tana fita suka ce Alhmdllh haba jaraba ta tafi yau zamu huta. Kaka aka biya ya fito da kayansa Shima zai shiga gefen Cele yayi Bismillah yace Ubangiji ka rabu da sharrin Yan uwan kafiran zamanin baya ya shiga mota suka tafi,Cele tace kaka muyi alkunutu tun a mota suka fara karanta alkunut ita da kaka har aka kaisu dai wani gida a unguwar takari ne amma gidane dogo a hawa na biyu Cele take ita da Kaka,gidane hadadde na glass da Glass gidan glass takari suke Kiran gidan,2bedroom and Palo sai kitchen kowanne daki da toilet komai sabo ne a ciki me kyau Palo yasha kujeru da center carpet,Hammad yace Alhmdllh kuyi zamanku a nan Kuma ku daina wata sana'a zan dauki nauyinku,Cele tace Masha Allah,Allah yasa na soka a haka,nidai ba ruwana Idan ban so ka ba Karka kace na yaudareka ko na cuceka naci kudinka,bani na Saka ba
Chapter 49 · 0% Book details