Sashe 52
Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kayanka zan Saka na zama yar daudu ta juya kanta jikin window ta kwanta a jikin kujera bata Dade ba sai bacci har me gyara Yazo yace ai security ta shiga,ya mata abinda zai mata sannan Salma ta Farka suka tafi. Yau tun safe suke cikin school kuma sai 5pm zasu tashi,suna fita break Auta yaje ya mata take away har aji ya kawo mata,Yan ajinsu suna ta Kallonsu,Salma ta turo baki tace ka bude min ta koma ta kwanta,Auta ya bude Mata yace gashi nan ya tashi ya fita,tashi tayi da sauri ta leka shi ta window,taga mata sai tare shi suke yi suna gaisawa gashi Auta popular ne a school din,abincinta ta dauka ta dawo bangaren su Auta ta zauna a nan taci abincin duk inda Auta yayi idonta na Kai,shi bai kula da ita bama,sai da suka fito shi da wasu maza biyu suna submiting assignment mata suka zo wajen wata ana ce mata Chima ta dafa kafadar Auta,Auta ya Kalli gabas yamma kudu da arewa yaga Salma a wajen data fiye zama,kanta ta dauke da sauri,da sauri Auta ya janye jikinsa daga bangaren su Chima ya koma gefen Emeka,Inda Salma take zaune ya nufo Yazo ya zauna a gefenta tare da tambayarta me yasa kike son zama a nan? Ae kace haka mana tunda ta'asa kake aikatawa ba alkhairi ba dole kace na fiye zamar muku a waje,wlh duk abinda kakeyi Ina gani sai na fadawa Baffa tunda Kai Dan gatan Mami ne Baffa zan fadawa abinda kake yi a school,Auta yace Allah ya baki sa'a wai mene damuwarki Dani tunda Baso kike so Ina ruwanki dani,tashi tayi ta tafi. Suna komawa gida sai bangaren Baffa yana nan kuwa Mami tana wajen ta shiga ta durkusa ta sake gaishe su suka amsa,Salma tace Baffa Karar Auta na kawo,Baffa yace Ina jinki Salma me yayi Miki Kuma,tace Auta fa ba karatun yake ba,abinda aka kaishi baya yi Kuma ance indai kana zaune da mutum kaga abinda zai cuce shi ka fada,gaskiya Auta asarar kudi akeyi kamata yayi ma a cire shi daga school ya dauki hanyar lalacewa,ko wacce mace tazo ta dinga rike shi wlh kala kala ko Ina yake mata suna nan,dama an San Auta da shegen son mata a baya,Baffa yace zai aikata zan masa fada Kuma kin kyauta da kika fada min,Mami tace Ina Autan? Salma tace ai yasan bashi da gaskiya ya buya a daki,murmushi Mami tayi tace to za a masa fada, tace to ta tafi tana murna tace Allah yasa a cireshi daga makarantar, Su Mami su dariya ma ta basu ko zancen nasu yiwa Auta ba,ita Kuma Salma ta zaci an masa fada. Bayan taci abinci ta huta sai da ta yiwa Auta girkin dare. Washe gari da sassafe tayi sharar compound tazo tayi Shirin school suka tafi tana murna an yiwa Auta fada suna zuwa taga mata dai Basu fasa abinda suke ba,Salma sai ta koma gadin Auta sai ta bar lecture ta fito tana leken Auta,ana tsaka da lecture ta dauki Escuse ta fito taje ta lallaba a boye ta gano Auta yana nan lafiya a zaune shi kadai ba mace ta koma aji,ba a Dade ba ta sake ficewa ta zo saitin window inda Auta yake zama ta leka shi ya juyo da sauri,ya ganta tana lekawa ciki,yace mene ne ko Kun tashi ku? yana Mika zazzabi yake ji Mura yake,tace a'a ta juya tayi tafiyarta,baki Auta ya tabe yaci gaba da duba littafinsa,sai da suka gama lecture suna jiran 1hr su shiga wata,Salma ma ta fito su sun gama gaba daya,inda Auta yake zaune taje ta tsaya tare da Mika masa littafinta tana kumbura tace Assignment ne ni ban iya ba Allah,nayi nayi na kasa ni ban ma gane ba,gefensa ya nuna mata yace sit,zama tayi yace Allah yasa Nima na iya,tace yo ai da kyar zaka iya din tunda ba karatun kake ba burinka mata su tabaka,Auta yace ae Allah ai mata akwai dadi,ta kule sosai tace dama ai dama dadi kake ji Kuma Allah yana rubuta maka zunubi,littafinta ya duba ya kwala mata biro a kanta yace wannan ne kika kasa ganewa sabo da bakya ja duk katon kan nan a banza,baki ta turo masa hannunta me kyau fari ya sha lalle maroon ta Mika masa tace bani abina,Hannun nata yabi da kallo yayi kyau,yace kalli yanda zanyi zan koya Miki,yana mata explanation ta zuba masa Ido har ya gama yace kin gane? Salma Shuru,kafadarta ya girgiza tayi firgigit yace Zaki kashe kanki da tunani fa akan Baso,kin Hana kanki sukuni,gaki kyakyawa sai cutar kanki kikeyi,Salma taji kanta yayi wani girma an yabeta,Ido ta lumshe tayi murmushi,murmushi yayi yace yar Baso an fara hankali kwayar ta fara sakinki ne? Kanta ta dauke ta mike zata tafi ya jawota ta zauna jagwab yace Ina zuwa? ta zaro masa ido lokaci Daya ta lumshe,kallonta ya sake ta sake zaro Ido ta Maida abinta normal,murmushi yayi ya mike yace time dinmu yayi bye,ya barta a zaune tana jiransa, Headphone ta makala a kunnenta tana jin Waka tana kallon Auta ta window,Shima jefi jefi yana kallonta. Washe gari Babu school Auta bazai je Office ba yana gida a kwance yana zazzabin Mura,Salma kamar kullum tayi aikinta Share ko Ina na gidan ta dawo ta dauki break fast dinsa ta nufi dakinsa tana zuwa ta ganshi a kudundune cikin bargo,tace dama daga ganinka kalar cuta ne sai da nace ai Karka shiga ruwa ka shiga ai gashi nan,ta Bude bargon ta ganshi daga shi sai boxers,tsoro taji ta rufe shi da wuri ganin Antenar Auta,tace Kai wannan ta mussamman ce kaga yaro,Zarangade sunan wata ciyawa, a'a wannan yayi aurensa ya samu Industry me kyau wannan sai dai manyan mata masu Industry a baje Ina mu Ina wannen , kitchen ta Koma ta masa shayin ginger kaninfari da masoro yayi yaji tare da saka sugar ta matsa lemon tsami kadan ta hada da Zuma ta kawo masa,Mami ta iske a wajen Auta,Mami ta Kalli Salma tace wannan fa tace tea din ginger na masa ko zai samu lafiya yana magani,Mami tace an gaisheki an fara hankali ashe,dariya tayi tace Mami ai sabo da ku nake yi badan shi ba,Mami tace kuna waya da Baso kuwa? tace a'a Baso ai ya zama Mugu Ina kiransa zai bani wani aikin Allah Mami Kalli hannu na tsabar rike tsintsiya har ya canja,gidan yayi girma a tausayawa Marainiya,tayi magana tana marairaicewa,Mami tace so muke kiyi hankali ai,tace nayi Allah,Mami tayi murmushin jin Dadi tace ban yarda ba,Salma ta marairaice tace a canja min wani Dan Allah Mami Allah naci ubana yanzu,Mami tace to bari a Kira Baso a ji,Salma ta zaro Ido tace shike nan na shiga uku,Mami ta sake Kiran Baso bayan sun gaisa Mami tace Salma ta gaji fa ta nutsu yanzu,Baso yace da saura ku Daina tausayinta mage ce me kwanciyar daukan rai,Mami tace a'a na canja mata ta Daina komai yanzu zata dinga yin aikin Auta kawai,Baso yace a Kara mata da goge windows na gidan duka,Mami tayi dariyar muguntar Baso,ta mikawa Salma waya,yace kina jina? tace ae yace goge windows duka na gidan,Salma ta hango Uban windunan tace Dan Allah a Maida min sharata,dawo sharar Yaya,Baso sai da yayi dariya yace to yanzu dai zan Miki sassauci yac e kinga Mami Idan kika sake tayi girki da kanta ta bada wanki wani waje da shi Kansa Auta to wlh sai na kusa halaka ki,Kuma yanzu a dakinsa Zaki dinga kwana Idan naji baki je ba sai na zo garin,tace to,yace saura ki masa rashin kunya Dan ubanki,Salma tace indai wannan ne ai da sauki zanyi,yace yawwa sannan ke Zaki dinga shirya shi kullum kaya Idan zai Saka sai kin Taya shi Idan ya fada min baki yi wayyoooo Salma kin gama yawo Idan nazo,Salma Kam ita an rage mata wahala murna take tace to,yace Banda fadar sunansa gatsal,tace ai bana fada ka tambaya kaji ban taba fada ba,yace yawwa Idan kinyi abinda nace to Baso yana kaunarki,Salma farin ciki ya kamata Baso yana sonta sai washe baki take yi. Mami tana kallonta tace Allah ya kyauta ni Kam me Baso yake baki ne Salma Wanda babu a gidan nan? Salma tayi shuru tace Babu Mami komai kunfi Baso kawai shakuwa ce da yanda yake kula Dani duk da yana dukana amma ni nake cewa ina sonsa shine yake dukana akan haka,Baso yana da kyawun halaye Wanda sai Wanda ya zauna da shi zai gane,Ummm Mami tace,kin san dai kina da aure Kuma babu kyau a Musulunci son wani kana da aure,tace ba kyau na sani Ina so na Daina na kasa ne,Mami tace Allah ya kyauta, Auta yana jinsu a cikin bargo,Mami ce ta bude bargon tace tashi kasha magani,Salati Mami ta saki ganin Auta yana kuka,bata kawo komai ba tace duk cutar ce,ae kawai yace, Salma ta dawo gefensa da sauri ta zauna tana taba wuyansa tace a lallai jikinka da zafi lallai kayi kuka kayi hakuri baza ka mutu yanzu ba,ai cuta ba mutuwa bace,Mami tashi tayi ta fice jikinta a sanyaye tasan Auta karya yake ba kukan cuta yake ba,Salma ce ta haura saman bed din tace sanyi? Kai ya daga mata kawai,ta goge masa hawayen da hannunta tace haba sabo da Kai Auta ne sai shagwabar tsiya,dariya yayi yace ke yar fari ce ai shi yasa kike baki da saiti,gaki kwaila gaki yar fari,gaji rainon Baso dole baza a ga daidai ba,Salma tace kwaila tana gidansu, maganin ta bashi yana sha tare da sarkafo hannunta ta kafadunsa tana bashi a baki sun jere a tsakiyar bed,sai kallon Auta take kamar ba gobe,a hankali tace Auta me gemu,juyowa yayi suka hada Ido suna kallon juna sun tsurawa juna Ido,A hankali yace a aske bai Miki ba? tace a'a ka barshi mana ya maka kyau. Yace ai Baso ya fini kyau ko? tace haba Karka cuci kanka ai ba hadi, tace kwanta bari naje na maka girki,yace ki barshi ni bana jin yunwa,no kazo ka fara yiwa mutane kuka gwara a baka ni ai Kuma naga ta kaina wajen Mugun Bawa ta mike ta fita,bata Dade ba ta dawo da abinci ta ajiye a gefe,yaji sauki har waya ma yake dannawa tace ga abincin,yace haka aka ce