← Book details Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 93

Sashe 43

Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tafi ta kowa yo ta Isa ta fi miracle,nace never sai dai ta bi bayana,wani ya dora na biyu muka kunna muka ga yasa wasu suna chashewa an rubuta yanayi me Dadi,nace ba sabanba yau mun shiga uku,Nawwar magana yayi masa ta private yace Idan ana jin dadin a bar Online mana,Auta dariya yayi ya tura masa ya ranka mu babban Kai ne ba irinka ba an gama da Kai abu kadan sai ka rude mu kuwa sai an sha fama,Kai kuwa an wanke an baka ka shanye,Zanci ubanka wallahi cewar Nawwar sarkin masifa,Auta yayi voice yana cewa Yaya sai ya tsaya yace kashe light please sai Kuma yace sorry Yaya good night munyi can mu, waye yace kayi aure da wuri ka shanye dadinka kazo ka dameni ya kashe wayar gaba daya ya kwanta bacci abinsa.. Nawwar yana jin muryar Auta yace lallai yaron nan ya rainani yana magana da ni yana wani ce mata kashe light ya rainani na Daina wasa da shi,Nace chill man mene abin raini,dariya Nawwar yayi yace Allah Yan Makaranta abu kadan yanzu sai turanci nan gaba ma naga Alama Hausa Zaki daina,dariya nayi tare da makalewa a jikinsa,yace ga cikina yana ta girma Allah yasa a haifo min mace na fi son mace,Nace Ameen Allah ya bamu me albarka. Washe gari da asuba Auta ya tashi mutumin da kullum sai an tasheshi ya tafi masallaci Sallar asuba indai Mami bata je ba bazai tashi ba sai rana ta fito yawanci yake Sallar safiya amma yau harda tashi da asuba,Light ya kunna yace to ya zanyi na zama Mijin wata Idan ban tashi ba ace banyi hankali ba,brush yayi da Alwala ya fito sanye cikin jallabiya harda rike carbi fari ya tako dakin Salma ya Murda handle kofar ta Bude ya Dan tura kofar a saman Sallaya ya isketa zaune yace cab duk sammakon ka wani a tafe ya kwana munafuka itama Dan tayi aure ne wai ita ta gari bayan mata da yawa basa Sallah akan lokaci wasu ma sai suce sai su gama ayyukansu suke hadawa,juyawa yayi ya rufo mata kofar tana jinsa domin a fili ya furta maganarsa tace Dan kawai Addua nake ne da na rama amma zamu hadu ne. Yau Mami tana sa Ido ta Samanta ta leka part din Auta ta gani ko zai fito Sallah ko uban baccin nasa zaiyi sai kuwa ta Ganshi ya fito harda carbi da jallabiya,Baffa ta Kira tace zo kaga Auta me gida,window din ya karaso tare da rungume Mami ta baya suna kallon Auta suna dariya,Baffa sahu daya suka yi da Auta yau,sai da aka idar da Sallah ya tsaya harda azkhar sannan suna fitowa yace Baffa barka da asuba Ina kwana? Baffa yace sai kazo ma gaisa a hanya zaka gaishe ni,yace ni fa yau bazan zo ba bacci zan koma 12pm Kuma ina da lecture,au yau ma baza ka hakura da school ba kana Angon,yace me zan mata to shike nan sai na dinga zama,Baffa ya Kalli Auta yace Auta Anya kuwa kana son yarinyar nan duk mugun son aurenka,Ina sonta mana ya furta a ransa yana cewa karya nake bana sonta,sai da zasu rabu kowa zaiyi bangarensa yace ka gaida Mami,Baffa yayi dariya yace to zata ji ya tafi,Yana komawa bacci ya kwanta ya dinga bacci,Salma kuwa tuni ta koma bacci,sai 10am tashi tayi ta gyara gidan tace wallahi bazan gyara masa daki ba,wanka tayi taci kwalliya cikin leshinta na lefe brown and golden color tayi kyau,mayafi ta yafa ta fita taje part din Mami ta isketa a kitchen a kasa ta durkusa tace Ina kwana Mami,Mami taji Dadi taga hankalin Salma,ta amsa da fara'a,bayan nan ta fice tace zata je ta gaida Sauran tana mikewa Baffa ya fito cikin Shiri zai fita,ta sake zubewa a kasa guruf tace Ina Kwana ya amsa tace an tashi lafiya ya amsa da fara'a dama Baffa ya tsani gaisuwar zamanin nan da akeyi mussamman yaran yanzu ana ganin wayewa ce ko wacce Ina kwana wasu ma kafin ka amsa sunyi gaba Babu mutunci ba girmamawa Ina kwana kawai sai yarinya ta wuce ta barka nan,Baffa yace Honey zan fita,Salma kunya ta kamata a ranta tace bariki kan Uba tsofai tsofai a gabana cab wai honey,tana tsugune taga Mami ta rike hannayensa tana kwarara masa Addua,Salma tana satar kallon su ta mike sum sum ta fice kunya ta isheta ita Kam,part din wise ta shiga dauke da Sallama a bakinta Papa ya wani kwantar da Kansa a kirjin Wise suna Palo kuma,Baffa ganin surukarsa ce ashe ya tashi da sauri,Shima durkusawa tayi ta gaida shi ya amsa da fara'a ya tashi ya koma bedroom,tace Aunty Ina kwana? Wise tace ai ni kawarki ce yarinya tashi ta jawota saman kujera tace da Alama kalau kike wlh Auta ba abinda yayi gaskiya Ina Jira nazo gashi,Salma tana jin kunya tace sai kace wata kaza,bata Dade ba ta tafi wajen Iyamami Sabreen ta koma can da kwana ta gansu tare suka mata wani kallon banza suka watsar da kyar ma suka amsa gaisuwarta,Iyamami tace ashe da sauran hankalin da kika San kizo ki gaida manya Allah ya kyauta ko a Ina Auta ya kwaso Sabreen ta karasa da oho masa,Salma ta kalle su ta balla musu harara ta juya fiya fiya ta fice, Iyamami tace Iyye kaga yar iskar yarinya to dama tun kafin a aurota an zuga ta,lallai an sanar mata mune shegun gidan nan zata ci ubanta,Sabreen tace kyale banza can zata yanka. Salma part dinta ta koma tana shiga ta samu Mami har ta Aiko musu da abinci,Auta ta gani ya fito daga shi sai wando 3qutr ya fito da mopper da tsintsiya ya gyara bedroom dinsa tsaf da toilet,tazo zata wuce yace dadin abin Allah ya mana hannu Kuma ya bamu lafiya mu bamu Saba kazanta ba,binsa tayi da kallo gaba daya ta shagalta da kallon surar Auta Dan dagwas har ta manta ma a Ina take ta shagalta ta tsura masa Ido,yace Hello,hankalinta ta dawo tace ai kasan ba Kai kadai bane a gidan da mutane to baka birge ba ka Maida rigarka ka Saka ya fiye maka na gaji da ganin muninka,Auta yace sannu uwata Mami ya ja tsaki yaje ya ajiye mopper ya dawo ya wuce sama abinsa wanka ya fesa ya sha kana nan kaya ya dakko yar jakarsa ya ratayota ta wuyansa ya fito Dan gaye anci swagg, Salma ta zuba abinda take so tana ci,ya fito ko kulashi bata yi ba tana Shan tea tana danna wayarta karama Vivo,cup ya dakko ya zuba tea ya hada abinda ya sha yaci chips kadan ya dauki chegum me tsada ya jefa a bakinsa,ta kalle shi ta tabe baki tace Iyayi mu ayi mana Iyayi mene bamu sani ba Mami Son kawai, komai sai an baka ai Kai a garin nan baza ka taba samun aikin yi ba,ga mate Dinka nan suna Neman na kansu kaje gari ka gani Yara kanana sun zama attajirai Kai kuwa sai dai a baka ka dogara da kudin Iyaye,a haka Zaka iya daukan nauyina,Auta yace Allah ya baki lafiya naga Alama baki da hankali,Salma ta mike tare da rike kugu tace Kai waye da zaka fada min magana,tsaki ya ja ya fice ya barta tana kwafa,cikin fushi ya fito a fusace yana cewa yarinyar nan naga Alama bata da hankali,Nawwar ne ya juya kan kan motarsa yayi parking ya iske Auta yana Shirin shiga motarsa da Baffa ya siya masa gaf da aure,yace Ango Makaranta Kuma? Auta ya kalle shi kawai ransa a bace,yace Auta kalau Ango Kai da za a ga kana nishadi,Auta harara ya zubawa Nawwar ya shige motarsa ya wuce,dariya ta kama Nawwar yace duk yanda akayi Amarya ta hana Auta kanta haka ya kwana Babu komai, haka nema ya furta tare da shiga bangaren Mami. Mami tace Kai Kuma lafiya kake dariya Kai kadai yace ni da Auta ne kinga uwar hararar da ya min ya tafi fa school,Mami tace so soon haka har ya tafi? Yace ae Kuma yana fushi,tsokanarsa kayi maybe,Nawwar yayi dariya yace Anya kuwa Auta yana son yarinyar nan Mami,Mami tace Nima Ina ganin da wani abu kawai bazai fada bane sabo da Auta da aure amma ace gidan ma sai da na tasa keyarsa gaba yaje,Nawwar yace Allah? tace ae fa abin da mamaki wlh Kuma shi ya zabo abarsa bare ace mun takura masa,Nawwar yace lallaba shi zakiyi ya fada Miki ke Zaki iya jure iskancin Auta, kyale shi Idan haka yaci gaba da faruwa zan gane ai,Nawwar yace shi yasa na fada muku Auta ba wani hankali gare shi ba girman ne kawai kuka ki ji,da masifa Mami tace to munyi masa din kaji min yaro ka fa damu Autana,ai shi baya laifi dama,ae naji Dalla tashi ka tafi ni,Nawwar yace yau bazanje aiki ba fa Kuma Rabia na Kai Unguwa bata nan,Ina taje? Gidan Seraline wai zata yini a can,Salma tana gama karyawa ta wanke kwanikan ta yafa mayafinta ta taho part din Mami ko ta samu saukin tunanin Baso a ranta. A hankali tayi sallama ta shugo ciki Nawwar ta gani taga suna kama da Auta tasan shine yayansa harda jin kunyar Yaya,a gaban Nawwar ta durkusa tace Yaya Ina kwana,ya amsa tace Ina Auntyn fa? Yace taje unguwa kuna lafiya? tace lafiya Alhmdllh, gaban Mami ta koma ta sake durkusawa tace Mami ga kwanikan Ina za a ajiye? Mami tana sani tace ya tashi kuwa? tace ae ya tashi,Nawwar yace wai wa? Salma tace me can wajen take nufi fa,Nawwar da hannaye ya dafe bakinsa dariya zata kamashi wai Auta ne me Can wajen sai kace tsohuwa ita baza ta fadi sunan Miji ba Babu kyau wai,dariyarsa ya boye yace ai ya tafi school tace ae,yace a gaishe ki Mami cewar Salma,Mami tace wa fa? tace shi din,Nawwar jaridarsa ya dauka tare da rufe fuskarsa yana dariya a boye,Doguwar kujera ta samu ta kwanta a kai sai bacci, Ya kwashe ta ta dinga bacci sai gani suka yi tana ta uban bacci sai da azahar tayi sannan ta tashi lokacin Nawwar har yaje masallaci ya dawo tana yin Sallah ta Kuma kwanciya a saman Sallaya sai bacci,Nawwar suna ta jira da Mami suna kallonta ta dunkule waje daya
Chapter 43 · 0% Book details