Sashe 16
Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
government,kazo tumbir zigidir yanda kazo duniya sannan kace Wai bana girmamaka sabo da Allah ai Ina kokari ma su mutanen kaje musu a yanda kake zuwar min ka gani idan zasu sake saurarka,ai wlh bata kamata ma na gaisheka ba,Ni ya kamata ka gaisar kullum kace ya fargaban jiya,tunda a zauce zaka zo min kana ihu gaka ba Kaya ai abin fargaba ne amma sabo da kokarinmu na Mata washe gari harda gaisuwa wlh bazan gaisar dakai ba ai baizo a musulunci dole ba Kaine ma ya Dace ka gaisheni,bazan gaisar dakai ba fa Abhulkhair yawwa kuma body lotion Dina ya kusa karewa ka min transfer,kullum ka Tara min gajiya Kuma kana jira na tashi na gaisheka cab ashe zaka bushe,Malam Abhulkhair dariya yayi kawai yace ke komai naki yayi kinyi a rayuwa amma idan Kika tashi fadanki Kawai bi kike ta kaina,wa yace ka Dade a masallacin anyi karatu an Gama ka dawo muyi namu mana muma nifa baza a cuceni da malinta ba Dole ka bani lokaci na yawwa Kuma kayanka na gaji da ganinsu dinki kala uku ka Kara tun Aurenmu sabo da haka muje a siyi Kaya sababbi sannan kana Nan kaya ka dinga saka min a gidana Ina kallonka Ina Jin Dadi idan ba haka ba zanyi tawaye wlh,Malam Abhulkhair yace ya zanyi tunda na Zama mijin tace shike Nan naji yanda kike so Haka Zan koma amma kana nan kayan a iya gida Zan saka Miki? tace au da nufinka ka fita da su wata ta gani? Ni zaka sawa fa,an gama Aunty ya furta,tace yawwa Banda cin kudin marayu ko tallafin masallaci da ake sakawa a asusu kaci iya hakkinka albashinka na limanci da Kuma business dinka banda taba hakkin wasu,abinda zamuyi iya karfinka shi zamuyi,Yace na'am malama Tauraruwa wannan wa'azin ya shigeni,dariya Star tayi tace ai dai yau nace bazan yi girki ba a waje zamu je mu ci mu Dan shana,yace Inshaallah taso muje ki cudeni,Star tace wanka Mana please ni bana son gargajiyar nan mene cudewa Maganar dattijai,Malam dai sai yanda akayi da shi gaba daya star ta Gama mallake shi,gashi idan ya Mata laifi tayi ta jaraba,shi baida zafi ba ruwansa shi yayi Dace yasan dole baza ka samu Abu yanda kake so ba tunda kowa a duniya Yana da halin kwarai Dana banza Kuma baza kace zaka samu mutun dari bisa dari ba sai anyi hakuri. Kaka yau ana kwalla rana yayi Niyyar Umrah yaje ya dakko niyya da hiraminsa ya sake zuwa ya sauke Umrah ranar kwanansa uku a masallaci dakin Allah sai Ibada Kawai yake sai in yaji yunwa ya fito harabar masallaci ya siya yaci ya koshi ya koma,Addua yake kawai akan Allah ya bayyana masa Cele dinsa sannan Yana Addua Allah ya bashi kudin da zai dauki nauyin Kansa ba tare da yayi bara ba, yana zaune sai ga wata matar sarkin kasar Yemen,da masu take Mata baya mutum uku tazo Ibada,kana ganinta kasan akwai kudi,Kaka Yana zaune kawai yaga ta duka a gefensa ta zube Masa wasu makudan kudade Wanda dollars ne Kawai ta zube Masa Sadaka ta wuce ko kallonsa bata Yi ba,mutane suna kallo wasu suna cewa tsoho ya washe,Kaka ya daga hannu Yana Addua yaga kudin nan yace Allahu Akbar sai ya sauke Hannu yace Alhmdllh Alhmdllh Addua ta Kare ya kwashe kudi jiki na rawa ya mike maimako ya karasa Ina farin ciki yasa bazai iya ba tashi yayi yabar masallaci yace sai gida, a hanya ko gabansa baya kallo sauri yake yaje gida,sai ya hadu da askarawa suna kame yanzu sabo da ya samu kudi baya so su Kama shi duk askarawan Nan sun San Kaka yawanci sabo da duk inda ya gansu sai yaje ya Mika musu Hannu akan su kamashi sunki Kuma,wannan karon suna ganinsa daga ganinsu sai ya kwashe da uban gudu Kamar ana gudun fanfalaki tsoho dashi ya iya uban gudu haka,gulma sukayi Suka to ya Fara Jin dadi a kasarsu dole su Kama shi duk Sanda suka ganshi back to Nigeria, tun daga ranar Kaka da Askarawa Suka sa kafar wando daya, baya ma Fitowa daga masallacin layinsu sai gida,abinci ma a wajen takari yake siya masu kawowa gidansu Yana daki sai masallaci ko keyar Kaka Basu sake gani ba sabanin da Wanda kullum sai yaje wajensu, suyi ta labarin Kaka suna dariya,wani ogan askarawan kame a cikinsu yace Dan Allah ko sun ganshi Kar su kamashi su kyale shi ai tsoho ne dukkansu ya musu fada Kar su sake su Kama Kaka su kyaleshi ai rayuwarsa ta Kare ya tsufa kadan ya rage ya karasa sabo da ya tsufa,suka ce to Suka kyale Kaka idan ya fito ma har zuwa suke su Mika Masa hannu su tafa su dariya yake basu tsabar harkalla da hausawa wasu larabawan masu shaguna da masu kame suna Dan jin hausa,Yan kasuwar ma Kamar sun zauna a kasar hausa haka Suka iya sosai. Wani Askari ne da Hausa ya tare Kaka a hanyar masallaci yace kazo Ni Zan baka aiki zaka iya? da hausarsa lalatacciya yayiwa kaka magana,Kaka yace wanne iri? Yace Ina da mota Zan baka ka dinga tukawa taxi Zan maka takardu da komai ka iya mota? Kaka yace ai ni tsohon driver ne a Nigeria na Iya mota,yace idan baza ka iya yawo ba Ina da motar Yogourt Zan baka Ina da company na Madara zaka dinga kwaso Madara kana kaiwa wani kantuna da address Zan baka zan sa a koya maka aikin,Kaka yace na gode zanyi wannan ai ba na wahala bane suka tafa da ba askarar nan Bayan kwana biyu tsakani wani balarabe yazo daga wata state daban da gani kasan Yana da Naira ba askaren nan ya nemo Kaka,shi dai Kaka yana tsaye Yana jinsu suna ta larabci dake baya ji sai dai dai yake tsinta Kaka Bai sani ba ashe siyar da shi akayi akan kudade makudai Kamar wani Zamanin bayi anyi cinikinsa bai sani ba,Kaka ya yarda da wannan Dan sandan ya dakko kayansa yabi wannan mutumin balarabe a motarsa tunaninsa aikin za a koya Masa Suka tafi,Kaka yaga kamar hanyar Jeddah aka Yi da shi kawai dai Yana mota amma a jikinsa yaji kamar ba Alheri bane,suna uban gudu a mota Yana kwarara Addua. Mairo ciki ya tsufa Haihuwa ko yau ko gobe gashi takari asibitinsu ma Basu da gata a can ba kowanne asibiti suke zuwar musu ba Basu da yanci tunda basu da ingantattun shedar Zama a kasar su, Mairo kullum kudi Yana tafiya a biyan bashi Dan Wanda ta Tara shine taje siyayyar kayan jariri wani shagon larabawa,tunda taje larabawan Suka fara kus kus da sauran yaran shagon,Mairo tana zuwa Suka dinga washe Mata baki Suka ce ta shiga ta zaba ta shiga ciki ko Ina kayane iya kallonka Hanya ma a ciki kadan ce, ogan me shagon Yana bayan Mairo,yaran shagon Kuma wasu suna bayan ogan wasu mutun biyu sun tare gaban Mairo sun tsaya a gabanta wato sun sa Mairo a tsakiya kenan,Ogan ta baya Yana sosa Antenarsa gashi dattijo su Kuma yaran nasa Basu fi 20yrs ba shi kuwa zai Kai 60yrs ma amma sabo da zubar da girma da yaran suke hada baki,Mairo taji Antena tana guganta ta baya ga ciki tsoho ga yaran sunki matsawa sun tare Mata gabanta wani dan iska ma juyowa yayi shima Yana gogawa Mairo Antena ta gaba ogan ta baya,Mairo ta rasa yanda zata Yi ta tura ta tura sunki matsawa gashi sun matseta a tsakiya mararta sai ciwo ta fara,Yaron Dake gabanta ta samu ta galla Masa Mari ta nausheshi tana zaginsu da larabci Suma suna ramawa Wai me yasa Suka Zo musu kasa sun bar kasar su sunzo Iskanci kasarsu,Mairo sabo da su takari ne suna harka da mutane a garin har sun iya larabci ba laifi wani uban naushi ta Kai Suka rike hannunta Kuma basu fasa Mata gogen ba,yaron ta samu ta gartsawa cizo a goshinsa sai da ta fasa Masa goshi,ba shiri ya bata hanya ta fice da gudu gudu tana rike mararta ta fito bakin shagon ta tsuguna a wajen tana murkususu,Allah ne ya kawo su Sadiya Suka ga Mairo tana nakudar dole ta kamata Suka dauketa zuwa asibitin da za a iya dubata basu dade da kaita ba ta haifo yarta Mace me Kama da Saurayin da yayi kidnapping dinta ya Mata cikin, takari ba abinda ya dame su wannan ba sabon Abu ne ba ka haihu ba miji a wajensu,murna suke ta zuwa suna taya mairo, Mairo ta samu Sadiya ta bawa kudin Suka siyo Mata dukkan kayan bukata nata Dana jariri, zuwa dare aka sallamota ta dawo gidansu da yarta,Mairo sai Murna take yi tana kaunar yarta harda kissing dinta jinta take Kamar ranta,aka zaro nono Kamar ta taba shayarwa dake da lafiyarta ta haihu aka yo bismilla aka sawa jaririya nono a baki ana shafa Kan jaririya tace sunanki Madina kinji Yar lelena da larabci Zaki tashi kinji a lahira kin huta duk tambayar da za a Miki a lahira Zaki amsa abarki ba gargada bare Ina ina mu ki kyale mu ko ta yaya ma amsa tamu,Sadiya suna Jin Mairo,Sadiya tace in Banda jahilcinki Mairo larabci ko bakya ji a lahira ai Allah zai sa kiji dole da shi Zaki magana ba sai Wanda ya iya ba,Mairo tace ke rabu dani gwara ta iya tun a duniya. Bayan kwana uku Cele ce kullum ke kula da Ahsan,Maheerah tayi zuciya tunda tace ta kori Cele ya hanata tafiya to ta barwa Cele shi tayi abinda take so,Ahsan shima ko a jikinsa wanka ma Cele ce ke kaishi tana gwada Masa komai da ta gaji tace zata koya Masa ma yanda zai gane da Kansa ya dinga kai Kansa. Washe gari Maheerah sai data bari cele tana dakinta Ahsan Yana Palo yayi zuru sanye da makeken glass sai kuwa Maheerah tayi waya da Saurayinta yace gashi ma a gidan ta Bude Masa kofa,da sauri ta fice ta gaban Ahsan taje compound tsalle ta daka ta dane jikin Saurayinta tana murna tace da larabci my life ya makance zamu ci duniyan mu,dariya yayi Yana murna yace you are smart yana Jin turanci shi ya iya,yace I love you you are smart,yanzu wannan gidan gaba daya namu ne?