← Book details Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 93

Sashe 55

Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da private komai Kal Kal yana kamshi,Mami tace ruwan zafi fa,na fara wani yarfe hannu Mami ta fita ta Kira Wise da Star suka shigo tace kuje ciki ni kunyata take ji ku tabbar ruwan zafi ta sa,Ai kuwa suka shiga sai kace Yan iska a tsaye ma Nayi wanka na danyi gashi sama sama nace sai anje gida na fito,bani da karfi sosai,Abaya Wata Maroon me kyau Mami ta bani na Sanya na shirya kaina sosai na kwanta a saman gadon ina huce gajiya,Mami ce ta fito tace Zaku iya shigowa. Sun Riga me abin shiga ma Nawwar ya tsaya yana kallon ikon Allah yace sai kace Dan su to ku gama ni na shiga kowa yana daukan jiririn Kato da shi yana masa Addua,Inna da Seraline suka iso suma har da abinci lafiyayye a manyan flasks,Star tace kice girki kika tsaya yi,tace wlh shi na tsaya yiwa Me jego harda tea yaji hadi aka zuba min na shanye nan take sabo da yunwa, Mami ganin Nawwar shuru bai shigo ba ta fito masa da jaririn ya karba yana murna kamar zai tashi sama kafin ma ya masa Addua yace Mami ya take? tace abinci ma fa take ci kalau take fes da ita kawai karfi ne bata da shi sosai kuma wannan dama Idan mutum ya haihu yana jin hakan sai a hankali a dawo dai dai,sunyi mata Allurai da magunguna gasu ka siyo mata,ta Mika masa takardar, Mami iceko sun mata wannan abun Wanda ake kwashewa mace jinin dake mararta ni bana so a dade ana wani jini abu yaki ci yaki cinyewa,Mami tace to fitsararre marar ta Ido abinda Kai kasa nurse suka mata ai sun fada mana,dariya Nawwar yayi yace Mami sauki na nema mata fa,kaga yiwa yaro Addua ni,Nawwar ya masa Addua sosai yanda addini ya koyar sannan ya mikawa Mami yace kice su fito dan Allah ni zanga Matata wannan masifa haka duk Auta ne ya jawo da ya Kira su,Sai ga Auta ya dawo da ledojinsa na kayan marmari da nama da su Madara tarkace dai,dama yana kawo Nawwar ya bar asibitin,Nawwar ya kalle shi yace Auta ikon Allah ,Murmushi yayi kadan yace sai Aunty ta haihu zanyi dariya,yace ai kayi Da Autan Mami ta haihu tun yaushe kana can gantali,Auta yace haba ana ganinta? Yace ae mana an canja mata daki ma har taci abinci,Auta yace nayi Da shike nan na zama Daddy ya shiga ciki da Sallama suka Amsa,yace Masha Allah Aunty ya jiki? tana cin abinci tace Alhmdllh Nawaf,ya karbi yaron a Hannun Mami ya masa Addua yace kamar Yaya Nawwar kamar Aunty miracle suka yi dariya,Santana ma ya shigo yaga jariri ya tafi, sai da suka gama rubibinsu Mami tace duk su tafi gida suka fito suka tafi Banda Salma yar anace kamar danta ta karbe shi harda jijjiga shi,tsokanar Rabi tayi tace bari a masa rawa,da sauri na nunata da yatsa ina karkadawa uhm..uhm..uhm wai kar ta sake tayi masa,Auta yace to anyi da Kuma ba Saban ba,Nawwar ne ya shigo suka mike suka fito duka har Mami,ni kuwa na durfafi abinci sai yi nake,ya kalleni kawai yace sannu ya jikin? Nace da sauki na ajiye plate tass na cinye abinci,na bude ledar Auta na dauki yogurt sai da na kusa shanye roba guda,na dakko fruits nan ma naci wannan naci wancan sai da naji na koshi sannan na sha ruwa Faro nace Alhmdllh,sai lokacin na Kalli Nawwar dake tsaye yana kallona,nace zauna mana,ya sake cewa ya jiki nace da sauki lafiya nake,nace Baby local government ta fafe Yasin ta afka ai wani ruftawa tayi Kai naga bala'i,dariya Nawwar yayi, na dafa kafadarsa nace kaiiiiiii haihuwa da wahala yanzu su Wise nake tausayawa zasu dandana kudarsu, Nawwar ya zuba min Ido kawai, ina uban bashi labari na nuna kugu na nace aka rike ni ta nan,aka damki nan,aka tattaro marata aka yamutsa aka yamutsa sai naji kamar kasusuwana sun watse, Subhannallahi sai yanzu nake jin kunyar Mami tsirara nayi a gabanta,dariya Nawwar yayi yace shike nan ai kayan danta ne dan ta gani ba komai ai Larura ce,duk da haka da kunya Allah,itama ai mamanki ce ko? Nace ae mana,Allah yasa an mana hutun school Nawwar yace ai naji dadi nima,ki Kara hutawa zuwa yamma a sallamemu bari na Kira Umma,na Kira Umma ta daga nace Umma na haihu,Umma tace Masha Allah me aka samu? Namiji Umma,tace to Allah ya raya bari gobe su Omaira su taho ko kafin manyan su zo,nace to zan turo musu kudin mota,Umma tace akwai kudi fa,nace ai baza a kwashe naki ba Umma zan tura musu,to Allah yayi Albarka Ina me gidan, nace gashi bari na bashi ta mikawa Nawwar waya,ya karba suka gaisa ta masa Allah ya raya yace Ameen Ameen Umma. Bacci na kwanta na fara shakar uban bacci tun safe bayan na haihu har 5pm sannan na tashi,Mami tace dama ke muke Jira ki tashi an sallame mu,nace to na mike a hankali ina yatsina fuska,Salma tana wajen ta kalle ni tace rauni kika ji a wajen? Mami tace shegen baki kamar kinci aku,dariya Salma tayi tace Mami yanzu ai kuna so na ko? Mami tace dama muna sonki ai horaki aka yi dauki kayan mu tafi,Nawwar ya dakko flasks da sauran tarkacen Itama Salma ta dauka suka dawo gida abinsu,bangaren Mami a sama aka bawa Rabi daki,Suka shiga na zauna a gefen bed da kyar ina yatsine fuska,Mami tace ai ruwan zafi Zaki shiga gashi Zaki na sosai shine Zaki samu afwa,Wise ta hada min ruwan zafin harda zuba shegun magungunansu na tsumi a ciki,na tafi toilet naga magani a ruwan nace Wise ni yaushe zan koma wajen Nawwar a sake abin nan,Wise tace hehehe sanda Zaki koma ma ku zuba sex wa ya sani,wlh Idan baza ki shiga ba zan Kira Mami sai ya Huce abin haushi ke ba Salma ba bare nace zan Kira Baso,nace zan rama wlh ai kema Zaki haihu so soon,da kyar na shiga ruwan ina zama na Kwalla ihu tare da mikewa,Nawwar yace kinji Mami ta Kone,rabu dasu wanka take fa,na sake zama zan mike Wise ta danne min kafadu kamar zan mutu haka nake kuka sabo da zafi,sai da ya huce sannan na mike,Wise ta wanke min gashina tas da shampoo me kamshi ta barni ciki nayi na sabulu da kaina na shirya kaina na fito daure da towel da karami a kaina ina tsanewa,Nawwar yana gefen gadon a zaune shi kadai,nace Ina Mamin? ta tafi yiwa jariri wanka,ya taso a hankali yace shike nan na zama Gwauro ya rungume ni ta baya,hannu ya dora a kaina yana tsane min gashin, Mami ce ta shugo ta zuba masa harara tace a gaskiya ka dame mu ka tafi mana haka tunda kaga jaririn kaga lafiyarta,yace irin wannan shi yasa ba a son a bar mace ta tafi gidan Iyaye,ya mike ya fice yana cewa mutum da matarsa kawai sabo da ta haihu sai a Hana mutum sukuni,Miracle nace ka kwaso kayan jaririn nan daka siyo a kawo nan,yayi tafiyarsa gida ma gaba daya,wanka yayi ya shirya cikin kananan kayansa hadaddu purple ya kwaso kayan jaririn ya kasa zama a gida shi kadai ya dawo gidan,lokacin anyiwa yaro wanka an shirya shi cikin fararen kaya,nima na saka doguwar rigar material readymade me siririn hannu na shafa turaruka masu tsada ni da yaron sai kamshi muke me dadin shaka,dakin Salma tazo ta gyara ta dame bed din ta kwashe tarkacen fitarwa ta fitar dasu komai neat daki yana kamshi,Auta ne ya shigo ya sha gayu zai fita yace Hajiya Aunty me jariri inyeee ba Saban ba anyi da mun shiga uku Kuma, Yaya Nawwar ya kenan naga karyar maita yanzu gwara ya karo aure kawai,na harare shi ina dariya nace ya karo mana Idan ya Isa,ai sai ka auro masa wata mu gani dan iya Kai da ka kasa komai wlh ka bani kunya Auta Kai da muke ta Jira yarinyar nan sarkin giringidishi kayi mana maganinta ka kasa duk son aurenka,Auta yace sannu sannu dai Aunty a sannu sannu sai Kun kaita asibiti an mata dinki,Allah ya shiryeka Auta Dan Iska a baki,dariya yayi yana kallon Kansa a mudubi, Salma ce ta dawo cikin yar fitted gown dinta me dogon hannu itama an sheka kyau harda kwalliya,tazo ta ture Auta daga jikin mudubin matsa Nima na Kalli kaina,Auta ya kalleta yace to baki kyau ba,a boye Kuma yana kare mata kallo yana yiwa Rabi signa da Ido yana nuna duwawun Cele da hannu yace harka iya harka,Rabi ta sheke da dariyar iskancin Auta,Salma ana ta faman gyara kwalliya bata San me suke ba,Wise ce ta shigo taga Abinda Auta yake tayi dariya tace yau na shiga uku,Salma ce ta juyo tace me ya faru Aunty tace ba komai,Auta fita zaiyi yace nikam sai dare,Salma da sauri tace Ina zaka je Kuma,yawo ya furta,ka tafi dani,yace a'a ni Ina ni Ina ke ai ke sai Baso ki zauna ki karbi Yan barkar jariri ya bude kofa ya fice,Salma ta biyo shi da gudu tabi steps da uban gudu,da Mami suka ci Karo,tace ke Kam Salma bakya rabo da gudu Ina Zaki haka,tana haki tace Abu na manta ta fice,Auta har yayi nisa ta cin masa tana hakki tace wallahi Idan ..Idan ..ka kula wata bazan yafe ba,ta juya ta dawo kafin Auta ya juyo har tayi nisa,baki ya tabe ya wuce ya shiga mota abinsa. Nawwar ne ya shigo ya iske Salma da Wise a dakin suna hira,Salma tace sannu da zuwa Yaya ya farincikin an Baby,dariya ta basu ta mike ta fice,itama Wise ta fito,Salma wajen Mami ta dawo tace ki kawo jaririn a Kai shi ga Babansa can Yazo,Mami tayi dariya tace sai yace a Kai masa abinsa? tace ae yace son ganinsa yake bai karewa dansa kallo ba,Mami tace sannu zubaida wai yau kinwa Auta girki ma kuwa? tace banyi ba muna ta cuku cikun haihuwa,Mami tace to tafi kitchen ki Dora girki ba iya na Auta ba kowa da kowa,Hamra gobe zata dawo daga gidan su Aunty Rukayya a Katsina ta dinga tayaki aikin,tace to Mami ta wuce,Mami ta shiga da jariri ta iske Nawwar a zaune nace ai har naji sauki da nayi gashin nan,wani karfi naji,Mami tazo
Chapter 55 · 0% Book details