← Book details Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 93

Sashe 20

Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

key,tana kallonsu,Hajiya Hauwa tayiwa Maheerah magana da larabci tana gaisheta, Maheerah ta samu me Jin larabci sai zagi Kawai Wai ta shugo musu gida ba Izini,Cele tace kyale banza muyi abinda ya kawo ki ta shiga daki ta dakko littafin data gani Diary din Maheerah da take rubuta tarihin rayuwarta kaf ta dakko ta bude page din da ba rubutu ta mikawa Hajiya Hauwa tace rubuta nima tarihin koyon larabcina nane, Hajiya Hauwa tayi dariya ta Fara rubutu da Hausa larabcin ma da Hausa take rubutawa yanda Cele zata gane kalmomi masu ma'ana Wanda ya Dace mutum ya iya su ta koya Mata sabo da Zama da masu yare,Cele tace ya sunan ciki da larabci ciki na haihuwa ta rubuta mata,tace cuta fa Nan ma aka rubuta mata tana ta tambayoyi ana rubutawa sai da Suka Yi da yawa sannan Maheerah ta lura Diary dinta aka lalata Mata,tazo tana masifa da bala'i,Hajiya Hauwa tace wannan gidan naku bana zuwa bane Rufaida idan nazo Zan shigo na kiraki mu dinga haduwa a iya tsakar gida,Cele tace to ba damuwa ta rakata ta tafi ta dawo ta dauki Remote ta kunna channel din da ake nuna dakin Ka'abah ana ibada,Maheerah wani Tsaki ta ja ta fisge remote tare da canja channel ta Kai tashar larabawa masu rawa da damammun kaya, data gaji ma tashar turawa ta Kama me saka wakokin disco ta tsani a kamo Mata tashar Dake nuna wani addini. Cele shareta tayi har Ahsan ya dawo driver ya shigo da shi har ciki,Yana shigowa Cele ta mike ana cewa marhabah marhababika ya Ahsan dariya yayi ba shiri Cele tana kashe Larabci, hannunsa ta jawo harda cewa ta'al ta'Ali na'am shuwayya tana rikeshi suna tafiya tana cewa shuwayya Shuwayya a kujera ta zaunar da shi tace Ijilis,Yace Jalasna Wai ya zauna,Cele tace ya gane ya Gane na Fara iyawa a tafa min tana tafawa kanta Yana ta dariya Idonsa sanye da glass baya gani Wai, Maheerah Tsaki taja da larabci tace bata iya komai ba Babu abinda ta iya sai lalata Mana yare,tasowa tayi zata ta dawo kusa da mijinta Ahsan,Cele da sauri ta kankane shi tace karki zo Mana mu,Maheerah Takaici yasa ta tafkawa Cele mari Ahsan da larabci yace plate ne ya fashe haka? Maheerah tace Marinta nayi na gaji da abinda take min idan ciki ne nace bana so na hakura a sallameta Ni wallahi Zan iya zubar da cikin ma kowa ya huta,Ahsan yace mari haka wanne irin zalunci ne wannan ki mareta,ciki baza a zubar ba Ina son abina,Cele tace bashi Kika ci wallahi Kuma bazan tashi ba mijina ne ta kwanta a jikin Ahsan Yana kokarin janyeta yace Haram ya Subhannallah ya Subhannallah, Cele tace kaji da shi ta sake narkewa a kirjinsa tace Ina nan ta Sosa kumatunta tace fata gata Fara ashe karfi ne da ita kamar bayan kada,Ido suka hada da Maheerah ta Mata gwalo tace ke dai ta ko Ina baki hadu ba fata kamar bayan kada, Ahsan Yana so ya janye jikinsa Cele tace Kai dai baka San Dadi ba kafi son waccen me duwawu Kamar shape din Albasa, tashi tayi taje kitchen zata kawo Masa shayinsu da Suka Saba Sha,Maheerah ta koma jikinsa ta kanmake mijinta Cele ta fito ta ajiye shayin tasa hannaye ta fisgo Maheerah,ita Kuma ta manne a jikinsa,Ahsan yace shayi zai Sha Cele tayi sauri ta ebo shayin a spoon ta Kai bakinsa Maheerah tace wlh bazan yarda ta kwace min miji ba sai dai muyi ta yi ta Shige kitchen itama ta hado shayinta da snacks ta kawo Suka tsaya su biyu akan Ahsan Cele tana bashi Shayi Maheerah ma ta ebo nata ta Mika Masa shi kadai yake dariya a ransa dukkansu ya dinga karba ko wacce ta bashi ya karbe Yana Sha,Maheera ta dauki Snacks Ana shafa Masa gashi noorul Qalbi ta Mika Masa ya gutsira Yana ci,Cele ma ta shafa gashinsa tace ni harda gemun Zan taba duk da ni Haram ce to nace Haram nima ta shafe gemu da gashin Kansa shi kuma Alhaji Salmau Yana zaune kurum abinsa,Maheerah ta duka zata Masa kiss a lips,Cele ta durma mata duka a gadon baya ta bangajeta ta kwace Snacks din itama Wai ita zata bashi Ahsan Yana ji Yana ta ci shi kam Mata biyu akansa suna ta masifa,Maheerah tana zuwa ta fisge shayin ta Kai kitchen ta zubar duka ta dawo ta kwace Snacks din ta maida kitchen tace ya koshi da larabci,Ahsan yace shi bai koshi ba Yana masifa,Cele ta fahimci me yake nufi ta Shige kitchen ta Dora indomie tana Mata hadin Nigeria Amma bata sa yaji ba,Maheerah ma kitchen da shigo ta dasa tukunya tana girkinta na larabawa itama Cele tana nata duk a cikin Ahsan za a bashi, Cele ta riga Maheerah gamawa. Tana zuwa ta kawo Masa ta dawo dashi kasan carpet ya zauna tasa fork tana bashi a baki yana ci sai ga Maheerah ma da nata a plate ta zauna suke jere ita da Cele,Cele ta matsa jikinsa Kamar zata shige cikinsa Maheerah Kuma ta biyo da abincinta ta saman Kan Cele ta shallake zuwa bakin Ahsan,Ahsan ya gaji ya shiga surfa bala'i da masifa yace baya cin na kowa a cikin su sun dame shi ya mike Yana lalube da kyar ya koma bedroom shi Dadi ya isheshi Mata sai fada suke a kansa. Maheerah ce ta bi bayansa harda sawa kofa key Kar Cele ta biyo ta,Cele tace zaki fito ma. Kannen Wise su Uku Mata ne Suka zo wajen Wise sun kawo Mata Ziyara,Tunda Auta yayiwa Iyamami fata fata bata sake Shiga Harkar Wise ba sannan Iklima ma tsorata tayi ta gudu garinsu Amma har Yanzu Iyamami da sauranta,Kannen Wise Suka ce Aunty yau kwanan mu hudu ko kofar gida bamu je kisa a kaimu yawo,tace Zan kaiku da kaina amma Bari nasa Nawaf ya kaiku gidan su Rabi ku gaishe su,Wise a waya ta Kira Auta tace Autan mu,yace Ina jinki dan Allah su walida zaka Kai gidajen kawayena su Star,yace karfe nawa? tace 11am dai tunda yawon nasu da yawa,yace to su shirya Amma Kar a barni da jira, sun ma shirya su Kai suke jira kaga yanzu 10am yace to gani Nan. Auta wanka ya dauka cikin kana nan Kaya kamar zai bar kasar 11:30am yazo yace ku fito Suka fito suna ta kallon Iyayin Auta,Walida tace gashi kyakyawa haka shi dai Auta bai San suna Yi ba har Suka je jikin mota yace Babbar ta shigo gaba,Suna kunshe dariya Walida ta shiga gaba,Yana shiga ya kunna uban kida,Walida tace wow haka nake son mota da kida amma sululu motar wasu ba dadi,Auta yace wannan motar manyan Yara ce ai,Suka ce munga alama,Iyamami ce ta wuce tana musu kallon banza a cikin mota tace ai fa mun shiga Uku an auri jinin kudi kullum dangi suna Nan Kai Kuma bawan Mata da kaga Mata shike nan sai ka kasa zaune ka kasa tsaye,Auta yace ya ranki ya rufe mota yaja yayi gaba,Walida ta zake da yawa ita a Dole sai ta nuna ita wayayyiya ce a wajen Auta,Bata San maza Indai mutum na kirki bane me zakewa da nuna ta waye bata birge su,Yan matan yanzu da yawa haka suke burinsu su nuna su fa sun waye suna wani fitsara Wanda wannan baya birge mazan. Gidan Star ya Fara kaisu tana kitchen tana girki Malam Abhulkhair Yana ta yanka Mata salat ya zauna dirshan a kujera,ana Sallama Suka amsa Auta yace baki ne mu shigo,Malam yace Muna zuwa yace da namiji Nawaf ya balaga saka Hijab,Star tace to ta saka hijab har kasa ya bude kofa yace ku shigo Nawaf Kaine ka kawo kannen namu kenan? Yace ae suka zauna,Star yace Dan duniya shine baza a dinga zuwa gaishe bi ko ya Jin Dadi? Auta yace Jin dadi ai sai me aure Abhulkhair ya dinga dariya,Star ta kawo musu kayan ci da sha, Abhulkhair ya koma kitchen Yana kula da girki su kuma suna ta hirarsu,Auta yace Malam guda a kitchen ko ni da ba Malam ba ai baza a min wannan rainin ba,Star tace wlh karka cika baki yaro,sun dade a gidan Star sannan Suka tafi gidan Yar Zabil,Nan ma sun dade,sai gidan Mandula da Sera daga Nan Suka yada zango a gidan Nawwar daga nan sai dare ya maida su gida harda siya musu kayan makulashe. Sabreen yau tana gidan Santana tana kallon soyayya Kawai burgeta sukeyi sai taji wani haushin kanta da Dana sani da yanda ta samu Miji na kirki ta tsaya shirme gashi yanzu Kamar Santana ma ta rasa, Bayan Santana ya fita Jamcy ta rakashi ta dawo tace sai rayuwarku take birgeni Jamcy idan na tuna abinda nayi Ina nadama gashi na rasa kowa ko me matar ma ban samu ba Kuma auren nake so,a shirye nake idan na samu Miji Zan daina Shan komai cuta dai na Riga na cuci kaina,Jamcy tace Ni kaina da ban zaci Zan so Santana ba sai gashi zabin Alkhairi kullum cikin nishadi nake sai Naga shaye shayen da Muka dinga Yi rayuwa ce Kamar ta dabbobin da Basu San me suke ba,a da har mijinki na so Sabreen na so na Miki kwace sabo da kin kasa fahimtar gaskiya shaye shayenki yayi yawa Amma hakan Bai faru ba Nima ban cimma burina ba Allah yasa aka hadani da Santana wannan rayuwar ta fimin daraja da mutunci akan shaye shayen da ya Zama ruwan dare ga Mata da maza Ni Kam na daina Ina Miki Addua kema Allah yasa ki daina, Sabreen tayi mamaki tace yanzu da Nawwar yace Yana sonki sai ki yarda? Da gudu wallahi ke dai Allah ya kiyaye Kawai,Sabreen ta Sha mamaki tace rayuwa kenan gashi na rasa kin rasa shike nan,gobe Zan tafi garin su Mama zanje nayi sati daya,Jamcy tace Allah ya kaimu Dan Allah ki gaishe min ita,zata ji Inshaallah. Mami yau taji Baffa zaizo Auta ya fada Mata tun sassafe take gyara part dinta tana kalkale kalkale sai kamshi da sheki ko ina,ta shirya girki lafiyayye taci kwalliya cikin hadadden leshi sai kace wata budurwa harda sa Riga da skert sai kace wata matashiya haka Mami ta koma ta kafe dauri,Nawwar bai sani ba ya dawo daga
Chapter 20 · 0% Book details