Sashe 63
Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bata kwaikwayon Halin banza sai na shirme ko gayu ko abinci ko wani abu dai na shiririta shi take kwaikwayo wlh ko raba Daya biyu karki yi naki ta gani ta shanye,Cele tace wash ta baje ta kwanta a kasa ku kunna min ac,idon Cele yayi kwal kwal kamar zata yi kuka,murya a sanyaye tace ni ki koya min soyayya ki Daina damuna da Surutu wlh yau abin kunya zanyi a nan gidan zanyi first night,Naci dariya nace wayyo Allah Cele zata mutu Ahsan maza ka karaso,Cele ta Miko min wayarta tace ungo Idan ya Kira ki daga Shima da shegen iyayinsa yaki ya karaso tun dazu a Ina ya tsaya ne oho,nace Cele tashi na koya Miki love,Cele ta mike zaune tana fifita local government da hannu tace inda kisan nayi Zigidir Rabi,Allah wadaran Halin su Star Yan bariki banza Yan barikin wofi ai sai su fada min Illarsa mugayen banza shegiyar Mandula tana tafiya kamar tsohon kunkuru duk sai naci ubansu daya bayan daya,Allah ya tsine musu mutanen banza mutanen wofi,dariya nake Cele tace harda ke Yan iska kwartaye ba abinda kuka iya sai iskanci,waccen kinibabbiyar Star harda da wani cewa suna sha ita da Abhulkhairi,Ita Kuma Wise tana make murya yana da kyau ai hakane kyan maganin ya Isa wlh in aka Saba akwai dadi sai ayi ta soyewa shegiyar murya kamar ta tsakuwa,ita Kuma Sera ko ba maganin nan ba ai Sabeer yana matukar sonsa,Yar Zabil nawa mijin dake yare ne ai bama free da shi, shegiya da murya kamar ta Devido,Kwartayayen banza wannan Mandula ta Daina ciniki daga yau Babu me sake siya zata gani,dauke biro da takarda ki zana local government din nan da Antena ki bani hadda bazan iya ba yau wlh abin kunya zanyi,mikewa Cele tayi tana Jan skert tana karkada skert dinta da hannu,sai da naji tausayinta yanda ta rasa sukuni nace da haka kike so Salma tayi? Cele tace wlh ko ba yau ba sai na bawa yarinyar tunda jifa ya fada kaina ya fada kan uban kowa wallah kika sake kema sai kinyi wani cikin kafin arba'in gwara ki kyaleni Idan Zaki koya min ki koya min,Mami tsaf zan iya bata ta sha Baffa ya kwashi gara,muka yi dariya tace to tsofaffin sai soyayyar tsiya wai harda ce mata honey a gaban mutane ku da suruka duk Yan bariki. Nace to ni yanzu Cele me zan koya Miki? Uwarki Zaki koya min Idan iskanci ne ai Kun iya ,Nayi dariya nace Ahsan ne zai koya Miki Nima mijina ne ya koya min,ko me kika ga yanayi kawai ki masa,inda kika taba kika ga yaji Dadi shi Zaki yi har ku Saba,Cele tace to da biyayya, ta shiga wanka tace bari na shirya kafin Yazo naci dariya kamar me,na Kira Star na bata labarin ta tab reshe Ya juye da mujiya ta dinga dariya Nace yau kuna ta Shan zagi tace ai gobe zamu zo gashi rai fess wlh ko a jikina,Cele tayi wanka ta fito na bata Yan magungunan mata na niima da sauransu na hada mata da Madara ta shanye kuwa ta shirya ta zaro sabuwar rigar baccinta gantalalliyar rigar bacci me kyau dark green ta Saka na bata turaruka na daban ta shafa ko Ina lungu da Sako nace bafa daga zuwa Zaki afka masa ba nasan halinki ki daure ki ja aji,Cele tace Ina ajin yake wlh Babu,yo aji ai sai Makarantar boko yana can har da winduna da kofofi ni nawa a bude yake na bude kofofin ajin da winduna duka ke ceiling dinma na bare shi da rufin kwanon kango ne kawai, ke ni karki dameni fa kiji da danki shi Zaki wa fada ba ni ba baki haife ni ba. Umma ce ta Kira waya ta mana gajiyar suna tace Cele fa,a hankali tace kice nayi bacci yau ko kaka Bai Isa na daga wayarsa ba sai masu abin bayarwa su Ahsan ,wayarta ce tayi ringing nace wa Umma tayi bacci tace to kice da safe ta kirani nace to ta kashe wayar . Cele daga Kiran Ahsan tayi yace suna cikin gidan ma sunyi parking ta fito,Cele ta dakeni a baya da mugun zafi na dafe wajen tace Yazo banza ki tayani murna yana gidan nan,nace ki Daina murna Cele kuka zakiyi yau,Cele tace ni na tafi Yar bakin ciki sabo da ke ba dama Nawwar yayi shine kike kishi Dani,nace Allah sarki mu Antena Allah na tuba wanne kalar Vitamin ne nata bamu ji ba mu,kici gaba da shayar da danki ni na tafi ta Saka hijab har kasa a saman rigar baccinta ta fita Tana fita ya hangota ya fito yana dafe Kansa,ciwon Kai yakeyi Bai Saba tafiya haka ba shi Kam sai yau,Cele taje a hankali tana cewa a ranta aji aji taho taho aji taho har ta karasa a hankali a ranta tace slow slow ta tafi a hankali ta rungume shi ba ayi gaggawa ba,ta masa sannu da zuwa yana ta murna har ya manta da ciwon kan ma,hancinsa me tsini ta ja masa tace sai yau? taki sakinsa ta makale a jikinsa Ahsan ana ta murna tunaninsa missing nasa tayi haka,ta kalle shi sama da kasa mamaki ya isheta ya dauki wankan shadda Dunkin Dan Dede shi cif cif me Hannun links farar shadda Kal yana kamshi harda coka hula a gaban goshi hular ma me kyau komai fari dama su akwai son farin Abu,Cele tayi dariya sosai tace duk dama wannan Shirin yake,yace wai ya taho da lefen a dakko tace ba yanzu ba sai anje gidan Iyaye ake kaiwa yace to,duk zancen nan da suke Cele tana jikinsa ta makale,ta leka suka gaisa da Hammad,tace Yazo su shiga yace shifa yayi booking hotel room Kuma securities zai Sallama su tafi sai gobe Hammad ma yana bukatar hutu, Cele tace gwara hotel din ma,tace ya sallame su Auta ya kaisu Hotel har Hammad duk ya Sallama yace suje da motaocin su bar masa Daya gobe zai Kira su,Shima Hammad hotel din da ya kama daban, mutane sunyi bacci ba Wanda yasan Yazo,ko ni nace da Safe ma gaisa. Cele ta rike hannunsa suka tafi part din Auta shi Auta ma bai dawo ba,Salma ce a Palo tana kallo jiransa take yi su kwanta,Cele ta bude kofa suka shiga,Salma taga Ahsan tace lallai kice Ango yazo,Cele taja kwafa a ranta tace kunga yarinya fes da ita na gano ki Zaki ci ubanki,Ahsan ya dagawa Salma hannu da jagwalalliyar hausarsa yace Ina kwana,tace ai dare ne barka da dare zaka ce ah su Cele an dace oh yau kice mu toshe kunnenmu? Cele tace ke wallahi haushinki nake ji karki dameni karuwar yarinya sai kissar tsiya kamar ba rainon Namiji ba taja Ahsan suka yi gaba cikin bedroom Ahsan yace sai mun fito,Salma tace a fito lafiya chansa Cele chansa dai,Cele tace zamu hadu ne bari in sauke damuwata Zaki ci kwal ubanki,suna shiga ciki Cele ta nuna masa abincin tace ko zaka iya ci? Yace a'a shi baya cin wannan,Cele ta hau masifa tace ai kuwa sai Kaci fita nayi da nisa na Nemo maka a restaurant din larabawa kace baza ka ci,yace shi a lallai bazai ci ba ga larabawa da kafiyar masifa su basu san babu da tattali ba sam yace bazai ci ba,Cele ta Kira Auta tace kana Ina yace ya kusa da gida tace ka koma please ka nemowa Ahsan abincin larabawa ni na siyo masa irin rice dinsu da wata stew da naga suna ci yace shi a kasarsu ba irinta bace,Auta yace yo ba sai ki bar Dan banza da yunwa ba Idan yaji wuya tuwo ma cinyewa zaiyi wlh da kin sani tuwo kika masa ba a birge su fa kin sani basu san talauci ba,Cele tace please Auta wani aiki zaiyi ne sai yaci ya koshi,Auta yace da Daren nan a gidan mutane wanki zai Miki ko guga haba Cele ki dinga tausayin balaraben nan kullum ana nuna Miki hanya bakya ji,Cele tayi dariyar takaici tace Auta ka kiyayeni tam,Yace ko aikin magidanta zaiyi ne? Wayar Cele ta kashe ta rabu da Auta,Auta yana zuwa ya siyo sakwara da miyar Egusi da farfesun naman kaza me yaji,ya siyo gasashen kifi aka bade shi da wata miyar yaji ya kawo yace an samo,Cele tana murna tace shugo ku gaisa Auta ya shugo yace a'a sadaka yalla,tace wannan yafi karfin sadaka yalla,Annabin Allah a kasarsu yake,Auta yace dole na bashi girma,ya Mika masa hannu suka gaisa Ahsan yace ya Nigeria? Auta yace da sauki gamu a ciki muna ta hakuri,Cele tace jeka to ka tafi dakinku ka kama matarka kar na ganku a nan haka,Auta yace kallo zamuyi mu,Cele tace wai baka sha zobo bane Auta ya tuna Salma ta fada masa Cele ta bata zobo ta kawo masa amma ya subuce kofin ya fashe Idan sun hadu yace ya sha ya gode,Auta yace Ina ta so ma in Miki godiya zobo haka me dadin gaske na gode,Cele tace Kuma ba abinda kaji? Auta yace ni dai naji dadinsa gaskiya a bakina ya min kin iya Kuma thanks ya juya ya fice,yana zuwa ya ruko Hannun Salma yace muje Autar Auta,ta mike tana murza Ido na shagwaba wai bacci take ji, hannayen ya cjre yace muje I'm sorry aikena ake tayi na zama boy boy a gidan nan, Allah tun dazu nake jiranka ai kasan bacci nake ji,Auta yayi dariya yace sarki Yar Auta ni na bar Miki sunan nawa ma,mije yau tare zamuyi wanka,Salma ta zaro Ido tace ni nayi wanka na gaskiya suka shige bedroom. Ni kuwa Ina kwance da jaririna kawai naji nono na Daya ya soke ni a ciki kamar an tsira min Allurai,a Daren nonon nawa ya fara ciwo guda Daya,na kwana Ina kuka na dinga Kiran Nawwar yana ta bacci,kafin safiya nono Daya ya kumbura sosai. Auta wanka ya shiga Salma tayi Shirin baccinta yayi wanka da brush ya fito bacci yake ji Shima ya gaji,ya fito Salma me Miji ta zabo masa kayan bacci ta Taya shi shiryawa Yazo Saka wando ya jefar da towel Salma tayi tsalle ta fada saman gado ta rufe ido da pillow tace Dan Allah mene haka ai sai kasa ta dinga min gizo cikin dare tana tsoratani