Sashe 13
Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
glass dinsa ta zaunar da shi,Cele ce ta fito daga kitchen sai data tsorata ganin kwalliyar Ahsan,Maheerah tana gefe kuma,Cele ce tazo tace na gaji dole na tofa albarkacin bakina,Maheerah ta kalleta ganin tana magana da masifa,ta nuna Maheerah da yatsa tace sabo da bashi da lafiya baya gani shine kike Masa wulakanci haka dama nasan ba sonsa kike ba munafuka annamimiya,Maheerah ta gane Annamimiya sun sani kalmarsu ce,Cele tace kiji Ni da kyau majnoon....Maheerah ta nuna kanta Cele tace ae ke fa ta Mata ambola tace Umminki, Maheerah ta Kama Cele da kokawa Cele ta shaketa to Maheerah ba karfi Cele ta wanketa da Mari ta jefar da ita tare da take ruwan cikinta,Maheerah ihu take,Ahsan Yana tambaya meke faruwa da larabci,Ayusha ce ta fito tana ganin haka ta koma kitchen ta buya tasan cele da karfi,Cele ta dage ta zauna a Kan Maheerah ta dinga naushin bakinta Kamar ta samu gardi,bakin Maheerah ya fashe sosai jini na fita,Ahsan Yana ta masifa daga Zaune su bari yasan da Cele akeyi,cikin harshensa karyayye yake furta Celei Celei,ya koma Rufaida,sai lokacin Rufaida ta kyale Maheera dake kwance tana kuka,gashi ita ba abin ta kiri cele ba cikinsu dake jikinta shine hope din Maheerah tunda bata haihuwa wannan ce damarta ta samun da jininta,da kyar Maheerah ta tashi ta koma daki tana kuka tana wanke bakinta. Cele Kuma hannun Ahsan ta riko tunda baya ganinta taji tausayinsa sosai har hawaye ya zubo mata,hannunsa ta Dora ta fuskarta Wai yaji kukan tausayinsa da takeyi tace Sannu kaji kuka nake Ina tausaya maka Allah ya baka lafiya wayyo me kamshi na ta fashe da kuka yau ko turaren ma da nake shaka ba a saka maka ba Amma gashi a makale a kayanka kamar ka saka,Me kamshina ta sake fada tare da durkusawa a gabansa,hannunsa ya Dora a kanta Yana lallashinta da hannu, Dan karamin towel ta dakko da ruwa ta zauna a gabansa gwiwoyinta a kasa ta goge Masa bakin da Maheera ta shafa Masa a gira ta goge Masa jambakin tas ta zauna ta gyara Masa cola din rigarsa,ta mike ta koma dakinta ta dakko cumb tare da gyara Masa gashinsa Yana jinta Yana ta Murmushi Yana ta mata godiya Shukran Maheerah ce ta fito Fuska a kumbure ta iske Cele tana kula da Ahsan zuwa tayi ta ture Cele,Cele ma tace Kai Kai Kika tureni ta sa kugunta ta bangaje Maheerah, Maheera ta fusata Suka hade kugu kowanne gefe daya suna tura juna Kamar zasu fada Kan Ahsan suna kokawa kowacce tana Nishi,Maheera tasa Hannu zata gyarawa Ahsan gashi Cele ta bige hannunta tace karki ta min shi na kwace shi ta fada jikin Ahsan ta kakkare shi da hannayensa biyu Maheerah baza ta taba Mata ba,Maheerah tana mamakin karfin hali da shishigi irin na Cele,Celeta kankane Ahsan,shi Kuma yasan itace a jikinsa yace Celei Haram...Haram yana kiran matarsa Wai itace muharammarsa,Cele tace Sannu Alhaji Saluhu kaikam Kayi asara Sam baka da basira ka gama Zama Sallamamme duk abinda ta maka baka ji har wani kiranta kake Zauji zauji Kai dalla rufe min baki dan ma ana Jin kamshinka Naga shegiyar da zata sake tabaka yau taki tashi ta kankane a jikinsa,Maheerah ta dage iya karfinta sai ta banbare Cele a jikin Mijinta Amma ta kasa ta Kira Ayusha tace taimaka Mata,Ayusha tana tsoron Cele tace ba ruwanta,Maheerah hakan ya Kona Mata rai Nan take tace ta kori Ayusha daga aiki ta San inda dare ya mata,Ayusha tana bata hakuri ta dauki takalmi ta bita ba shiri Ayusha ta bar gida an koreta daga aiki,Ahsan Yana jinsu bai ce komai ba ga Cele ta makale shi,Maheerah kwafa tayi ta koma bedroom. Ko Sallah Zaiyi Cele ce take kaishi ta zuba Masa ruwa yayi Alwala ta sashi a Sallaya yayi Sallah,da dare ma zai kwanta ita ta kaishi dakinsa,Maheerah tana ganinsa ta jashi har da kwace hannunsa a hannun Cele ta kaishi toilet ta Masa wanka Suka fito ta shirya shi Suka kwanta,Cele tace Maheerah sai kinci ubanki wanka tayi ta shirya cikin kayan bacci ta nufi dakin su Maheera ta Bude kofa tana zuwa ba ko magana sum sum ta wuce tare da haurawa saman bed din Kamar yarsu ta Shige tsakiya ta kwanta,Maheerah zaune ta mike tasa hannaye ta jawo kafafun Cele kiiii zuwa kasa ita ta koma ta kwanta,Cele ta mike itama tace karya kike Dan ubanki Zikri sunan Baban Maheerah Zikri dama Cele taji ana ce Mata Maheerah bint zikri ta sake jawo Maheerah itama kasa ta koma ta hau saman bed din,Maheerah ta gaji ta fashe da kuka ta zauna a kasa tana rusa kuka,Oga Ahsan shi baccinsa ma yake yi Yana jinsu suna ta fama ya musu magana sunki ji,Cele tace daga yau wlh sai dai mu kwana tare Zaki ga tsiya,Maheerah tana masifa da larabci tace bata son dan dake jikin Cele ta bar musu gidansu Kawai yafi,Cele bata San me take cewa ba ta Mata Gwalo tare da Jan bargo ta kwanta nesa da Ahsan,Maheerah haushi yasa ta mike ta hau Kan Cele tana dukanta,Ahsan ko kulasu baiyi ba suna ta kokawa,karshe da ya gaji yayi magana wai Maheerah ta maida shi Palo ya kwana a kujera,ta Masa jagora ta maida shi Palo ya kwanta a saman kujera ta kawo Masa bargo,Cele tace wlh sai dai muyi asara ni da ke Babu me kwana da shi ta baje akan gadon tayi kwanciyarta,Maheera harda zuwa tace da Ahsan su koma daya dakin su kwana yace ta kyale shi a kujera zai kwana a palo. Kaka zaune yake a daki dawowarsa daga bara kenan Yana irga kudinsa,kudin ya rike a hannunsa Yana kallonsu Yana tunanin Cele kuka ya saki ba tare da shiri ba ya tashi a fusace ya fice sai inda yasan Askawaran kame sunfi tsayawa ya tafi can Yana uban sauri ya samesu Kuwa da yawa suna ta kame cikinsu ya fada ya Mika musu hannaye Wai a sa Masa ankwa yana cewa Nigeria wa Shan Koko da kosai wa dankalin Hausa ya fiye min dadi a rayuwata,suna kallonsa sun gane me yake nufi Suka kece da dariya Wai a maida shi Nigeria Suka ce la lah Suka ki Kama Kaka suna ta dariya sun San wuya yaji yayi rokon duniya Suka ce ya tafi gida ya huta ga Makkah akwai dadi haka Kaka ya dawo falau falau da jallabiyyarsa Kamar buhu Yana yawo a ciki. Mami ce tayi bakuwa kawarta Hajiya Karimatu tazo suna ta hira Mami tana bata labarin Makkah,Hajiya Karimatu tace Wai ya akayi kika kashe aurenki Allah ya Miki zabi na gari balarabe ance me kudi kyakyawa? Murmushi Mami tayi tace Ina kyau ai kudin banza me zanyi da su da kyar Allah ya kwace ni bawan Allah zai kashe ni Dana dawo da sai da nayi jinya,yaron nan Nawwar ya fada min gaskiya naki ji naje mutumin nan Kamar Allah ya Aiko shi Kamar ya samu akuya Ina lallaba tsufana zai karasa ni ni ba yarinya ba,Abarsa takai tsayin hannuna kamu Uku ke Naga bala'i Dan nonon da Yaran da na haifa Suka rage kala sai da ya kusa karasa su, Hajiya Karimatu ta dinga dariya,Sai ga Nawaf Auta ya shigo cikin Jean crazy ko Ina a farfashe Wai shi gayu,Mami Shuru sukayi duf Kamar ruwa ya cinye su Kar yaro yaji,Mami tace Auta, yace Na'am ya gaida su sannan yace Mami baki kusa iddar bane? Hajiya Karimatu tace Kai ka ji min yaro Ina ruwanka,Baffa ne ya damu wlh duk ya rame bana son ganinsa haka har fa mu zancen yake Mana ya koma yaro,Mami Fuska ta bata tace Ina ruwanku da idda ta kowa ya isheni cikinku idan Kuna tunanin Zan koma wajen tsohon ku to ku daina ba inda zanje,Nawaf yace Allah ya baki hakuri ya mike ya fice ya dawo part Dina harda tagumi shi a Dole Yana cikin damuwa,Ni da Nawwar muka kalli Nawaf Muka yi dariya,Nace Auta ga abinci na gama, yace bana cin abincin me ciki daga yawu sai Amai bazan iya ba,ki fadawa kawarki ta daina kallona a gida tunda ta auri tsoho na Mene zata dinga kallona sabo da Ina birgeta,Nawwar yace Wise din ce take kallonka ta San da zamanka ma a duniya,yace wlh ta sani ai Ina kallonta tana kallona kullum a fada mata Ni bana son matar aure sannan ka fadawa Mami in ta Gama Idda ta koma wajen Baffa,Baffa har kuka yake fa,Nawwar yace Allah Auta? yace ae baka gani ba abin tausayi jiya kasa kallon ball nayi wlh Zan tafi kallon ball ya kirani yace Autan Mami ya Mamin taku nace tana lafiya,yace har yanzu tana can da mijinta? nace ae, baka gani ba yaya Baffa zai min kuka wlh, nace Masa ya dawo da tsohuwar matarsa yace har abada ya Gama aure Wai aikin ma kwana nan zai daina zuwa, Kai Yaya ka tsira kana da kudinka idan Baffa ya talauce ni ya zanyi ko University ban Gama ba bare a samu a aurar dani,Kuma ni babban aiki nake so da me Baffa zai bani jari tunda Kai ka Zama na Mata na mata sai abinda Aunty Rabi tace in tace ka daina kulani ma dainawa zaka yi gaskiya a San yanda za ayi mune a ruwa idan baya Neman kudi kadarorinsa zai Fara siyarwa mu yanzu idan ta Allah ta kasance fa ya cinye kadararsa gashi bamu da aikin yi ya mutu ya barmu ba harka a'a da sake mu Baffa ne gatanmu wallahi Indai Ina nan a duniya dole mami ta koma ba a tausayinmu Kawai an watsar damu wannan ai ba yi bane, Baffa ya koma abin tausayi yayi kuskure ai ya gane ba sai a yafe Masa ba,ni gaskiya tana Idda Zan fada Masa gaskiya ta fito tayi idda da Zan iya walicci ma nine waliyyin Mami a sake daurawa na aurar da ita, dariya Auta ya bamu yana ta masifa sai ya aurar da Mami ga Baffa,Nawwar Tsaki yaja yace mahaukaci ai sai ka Zama waliyyin mu gani ni tashi ka bar min gida,kina ji Aunty a Haka zai iya rike mu idan ba Baffa? to Baffa dai ya dauki hanyar talaucewa ba ruwana kullum Yana daki Yana tunani ya fice ya bar gidan, Nawwar yace wannan Autan namu