← Book details Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 93

Sashe 5

Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

su kayan kwalliya dai body lotion da sauran duk takarkace na Mata har su Inners da kayan bacci komai an siya mata Kawai hand bag ce bata siya mata ba, wai ba inda Zan fita ai,har pakistain Ahsan ya siyawa Cele kala biyar masu kyau harda Riga da skert irin na larabawa kyawawa ganin Cele tana k kallonsu sun birgeta sai Kawai ya siya mata,duk abinda yaga Cele tana ta kallo sai ya siya mata,taga wani cup kato plactic Kuma na roba Amma design tace wannan da shi zan dinga Shan shayi,Ahsan yaji ta ambaci shayi tana daga cup din ya dinga dariya Yana mamaki ya kalli Cele yace Shay? ta daga Masa Kai ya dakko mata aka hada da cup din Suka je aka biya kudi Suka Shiga mota sai gidansu,Cele taga Aljannar duniya duk da su basuyin gida irin namu mutum ya shati fili Kawai yayi ginin da yaga dama su ba haka bane, Amma gidansu ya tsaru kana gani kasan me kudi ne tun daga layin da suke da kalolin gidajen dake yankin,gidaje ne Wanda basu fi hawa daya ba,Steps din benen ta wajen compound din yake sai ka bi ta nan sannan ka Shiga aihin gidan ma, compound Kuma harda parking space ko Ina yaji kayan alatu da flowers ado irin na larabawa, katon Palo ne na gaske yaji alatu an shirya Masa Aljannar duniya komai na ciki me tsada ne sababbi kuma kasancewar duk gaf da Ramadan ake canja kayan daki har cokali sai an canja latest duk shekara shima gidan sai an sake Masa sabon salon gyara,Sanyin ac Kawai ke tashi da wani kamshi,Yar aikinsu Yar bangaladesh me suna Ayusha tana ta aikinta ta Gama shirya dining abinda suke so ake dafa musu,Nan Cele taga asara Maheerah ce ta kalli abincin iri iri ta ja Dan ja tsuka tace taji yanzu bata son ci baza su ci ba,Ahsan ma yace abinda take so,dama su mazan su masu hankalin bautar Mata suke Yi kullum a wahala suke da matansu,Cele tana gani aka tattara abincin tas aka juye a Leda aka jefa a dustbin,Ayusha ta shiga kitchen itama Ayusha dake Yar waje ce har da wani kyamar Cele tana Mata wani kallon banza,Ahsan ne ya fito cikin Jallabiya fara yayi wanka ya shirya gata fitted inda ya bar Cele a tsaye haka ya sake fitowa bayan yayi wanka ya sameta a haka duk rashin kunyar Cele ta kasa cewa komai bakinta ya mutu,Ahsan kafadunta ya dafa da hannayensa biyu ya zaunar da ita a saman kujera Yana Mata murmushi, to dalilin Islamiyya dai ta gane da ya tambayeta sunanta tace Rufaida da Hausa Kuma ta fara Masa kwatance tana nuna gefen kofa tana cewa Nigeria Ismi Cele,Yace Cele da karyanyan harshensa yanda ya fada sai da ya bata dariya ta murmusa tare da daga masa kai da hausarta tace ae acan Nigeria Ismi Cele,Kai ya jinjina ya gane,Maheerah ce ta fito itama ta Sha wanka ta hade cikin wasu matsiyatan Kaya Ashe a gidansu kusan tsirara suke yawo Amma a waje sai ka gansu da Abaya da nikaf, wani mini skert ta saka na jean da Yar top me spaghetti hand Rabin nononuwanta duk a waje,tana da kiba Cele ta fita kyan diri nesa ba kusa har kyawun Fuska ma Sai ka zabi Cele baka zabe ta ba,hakoranta duk sunyi tsatsa sabo da mugun Shan Shan Zaki sunyi wani iri sun ciccinye dama basu fiye kyawun hakora ba,Ahsan kuwa kamar baya Shan zaki hakoransa farare tas kanana masu kyau shi Kam ta ko Ina Allah ya Masa baiwa,Tv ta kunna ta kamo wakokin larabawa masu rawa da gashi,Shi kuwa Laptop dinsa ya dauka kamfanin iPhone yana amfani da ita ya harde kafafu tana saman cinyarsa ga shayin Gahwa Yana korawa itama Maheerah shayin take Sha suna jiran abincin da suka ce Ayusha ta dafa yanzu,su dama masu kishi Basu barin Yar aiki ta zauna da wasu Kaya sai abaya Kuma Dole ta sa nikam a haka take musu aiki tana gamawa Kuma bata kwanar musu a gida sai dai ta tafi masaukinta da safe da wuri take zuwa kafin su fita ana yin Sallar asuba take zuwa haka Ayusha ma take Yi amma suna biyanta sosai ba mugunta,ba irin mu ba ki dauki yarki tayi ta wahala kina wulakantata yaran gida suna ci Mata mutunci gata kullum cikin wahala kina saka sutura me tsada dinki ma ki kasa Mata ko Yar Atamfa sai dai tayi ta Zama cikin tsumma,ta wanke kashin yaranki etc ki dauki dubu biyu ki bata a wata abin haushin har gidan manyan masu kudin Babu canjin albashi sai dai daiku. Cele tana Jin Kiran Sallah ta mike tace Salah,Maheerah ko kallonta bata yi ba Kawai tv take kallo,Ahsan ne ya nuna Mata dakinta har kayan da Suka siyo Mata shi ya tashi ya dauka ya Kai Mata dakin da Suka bata a matsayin nata,dakin yasha gyara,gado ne irin na larabawa na karfe amma designers ce har mudubin na daban ne kalar bed din sai wani slice Sip kana danna wani Abu zaka ga ya bude da kansa,harda katuwar plasma tv dinta,Cele tace ya ihali mutanen nan me suke nufi dani ne,tunaninta ma suman da tayi a mota ne yasa aka kaita asibiti Suka taimaketa. A cikin toilet dinta tayi wanka ta fito tare da daura Alwala ta shimfida sallayar data gani Fitowa tayi tace Qibla,Ahsan ya taso ya nuna Mata tayi Sallar magriba shi Kuma ya fice masallaci Maheerah tana nan a zaune tana kallon wakoki,Ayusha ma tayi Sallah Banda Maheerah,Ahsan ya dawo Yana ta Mata fada Amma sai ta Fara kukan shagwaba Wai ya takura Mata ita wahala take Sha a gidansa,ya shiga lallabata Yana bata hakuri,Cele Kuwa Fitowa tayi tace bari naje Palo na Sha kallon haukar Maheerah,ta fito ta isketa tana ta hawaye tana kuka kanta a bisa kafadar Ahsan Yana aikin lallashi,dariya ta kama Cele ta dinga kyalkyala dariya tace Yasin da a Nigeria kike da kinci ubanki hannun mazan mu da tuni kinci duka uwarki aka Miki yau naga Yar iskar Mata shegen Kai kamar turmi,ita a larabawan ma cutar Mijinta aka Yi hakora duk cin Zuma Kamar tsohuwar langa, Ahsan Jin tana ta maganganu tana kallonsu da yarena ya tambaye ta da hannu Wai lafiya? Dariya tayi tace da hausa nace wannan Yar iskar matar taka ce ta nuna Maheerah da baki ya kalli Cele yayi Murmushi harda sa min yatsa a lips dinsa Wai shiiiii nayi shuru Kar na takurawa Maheerah,Baki cele ta bude tace an gaisheka Alhaji salmanu Sallamamme ko Alhaji Sallau ne,kaga mijin tace,ya sake tambaya da hannu Wai me nace? Tace ubanka nace Sallamamme baza ka Zama Namiji ba ta gwada Masa yanda ake Marin mutum da zancen kurame tana zuga shi tace ya mareta, kafada ya makale,Cele tace yau Naga dolon mutum ni Rufaida. Ayi min sharhi yafi min godiya. MASU JUYA LITTAFI AUDIO BA IZINI BADA YAWUNA BA,NA RIGA NA SIYAR DA SHI. Masu bukatar sauraren Audio book dina ku duba YouTube channel S ZARIA TV https://chat.whatsapp.com/Dk4tpug5deM85rvWdb7KIR AsmaBaffa 08061929616 [8/9, 10:59 PM] +234 806 192 9616: 'YAR AIKIN KARUWAI 2 MATAFIYA 6-10 MASU AUDIO WANNAN BOOK NA SIYAR DA SHI,BAN AMINCE A JUYA MIN NOVEL BA IZINI BA. MASU BUKATAR SAURARAR AUDIO DINSA DA MA WASU ZAFAFAN NOVELS DIN KU NEMI YOUTUBE CHANNEL S ZARIA TV Official AsmaBaffa SADAUKARWA NE GA ZAINAB USMAN PAGE NAKI NE NAJIDA ALIYU BICCA Ina masu bukatar unique kitchen utensils . fabrics adult and children's wears shoe's and bag's. Da masu bukatar ahada musu lefe ko masu bukatar iya luggage's din kawai duk inkazo R&U EXCLUSIVE KITCHEN AND MORE. Zaku samu duk abinda kuke bukata ko a awanne state kake zaa kawo Masu bukata ga number. 0703 455 9202 https://chat.whatsapp.com/LAizQA6PofSLoFhQ7XeaQx Cele tana kallo Ayusha ta Gama girke girkenta Basu zauna a dining ba saman carpet ta jera musu abincin suka zauna a kasa tare da tankwashe Kafafunsu,ba tare da saka cokali ba da hannu Ahsan ya fara ci Yana kallon Maheerah wacce ta shagwabe fuska,yayi juyin duniya taci ta ki ci sai lallashinta yake da kyar ta yarda ya fara bata a baki tana ci da kyar,magana yayiwa Cele da hannu tazo Wai itama ta ci,harara Maheerah ta watsa mata ta hau masifa harda kuka akan Kawai yace tazo taci tare da su,Kalar abincin nasu ma Rufaida baza ta iya ci ba da larabci Maheerah tace Masa sai dai taje ta dafa da kanta amma baza ta ci musu abinci ba,Ayusha ya kira tazo tayi Shirin tafiya gida ta gama musu aiki yace ta tafi da Cele, ga Rufaida ta Fadi abinda take so a dafa mata,da zancen kurame ya dinga gwadawa Cele har ta gane wai ta bi Ayusha kitchen suna shiga Ayusha ta dinga masifa da jaraba zata Zama baiwar bakar fata tana zuwa ta hankade Cele,Irin baza ta koyawa Cele girki ba bare tazo ta rabata da aikinta,Cele Ido ta zarowa Ayusha itama da Hausa tace ke jaka nifa na iya girkina ba abinda ban iya ba ki tambaya kiji,Cele ce ni a kaso karewar iya soye soye,ke in kin Isa ki soya awara na gani ko ki soya fanke,yanda kike kyamata Nima Haka nake kyamarki ta karasa tare da dukan kirjin Ayusha,da hannu tasa kirjinta ta hade dana Ayusha ta hankada ta baya saura kadan Ayusha ta Fadi ta dafe jikin bango tana masifa da yarenta itama larabcin ma ta daina,Itama Cele da Hausa tace kina hauka ne ta daki kirji tace ke burar....kinci me cin....dan.....ashar ce kawai ke tashi,Ayusha taga Cele ta haukace Mata sai tsoro ta Fara ja da baya,Ahsan da Maheerah sunji yare na tashi ga na hausa ga na Yan bangaladesh kamar fada akeyi suka shigo ciki da sauri suka iske Cele taci kwalar Ayusha ta shaketa a bango tana ta fyalla Mata mari,tana kutuntuma ashar tace ai ba a ka'abah nake ba da Zan daga Miki kafa ko Kinga na saka harimi,Dan ubanki Niyyar Umrah ko aikin Hajji Kika ga na dauka ubanki zanci yo ko Umrah ban sauke ba bare na daga miki kafa,Ahsan yazo rabon fada Rufaida ta Masa Elbow a kirji ya ja baya tare da dafe kirjinsa Yana kiran sunan Allah,Ayusha Kuma taga anci uban oga ma Sai ta fara kuka, Maheerah
Chapter 5 · 0% Book details