← Book details Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 93

Sashe 42

Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba tarbiyya please,yace chansa dai chansa dai na hakura ko Dan kudina su tsira,Wise ce ta budewa Salma mota ta fito da ita tana guda ga Amarya ga Amarya. Kawai Baso mahaukacin ba Wanda ya bawa Amarya ba danginsu ya sulale ya fece,sai Nawaf yayiwa waya shi tuni ma fa yana hanya yabi mota,Nawaf yace to ya sake tura masa dubu talatin ya Kara kudin mota,Baso yayi ta godiya ya koma gidansa yana murna daga shi sai mahaukaci Washe gari dare na yi Baso ya siyo manyan gasassun kaji da yogurt guda biyu ya bawa Mahaukacin guda da Madara shi ya dauki tasa yana ci yana cewa Alhmdllh na huta da jaraba haba ai na samu na Wala yarinya ta gallabeni da kyar na samu me siyanta sai shegen bakin jini. Salma kuwa bayan Baso ya fece bata sani ba tana tsaye tana Shan kallon fitsarru muna ta rawa Auta rawa yake kamar me,Salma ta kalle shi tare da tabe baki tace kalle shi kamar Dan Iska aikin banza. Zuwa dare aka Kai su Sultana Wise da Salma ta dinga tafiya sabo da taga bata da dangi,Mami ta dinga fada me yasa za mu dauki Amarya daga kawota mu tafi da ita Kai wasu Amaren,hakuri muka bayar. Ranar Salma bata ga Ango ba Shima bai ganta ba a bangarenta suka kwana tare da Hamra,Sabreen da Iyamami sama sama suka yi bikin su ba ruwansu irin suna jin haushin su Mami,Iyamami Kuma wai an bari Auta ma ya auro musu bare ba yar dangi ba,gashi tana jin tsoron Auta wajensa ma baza ta je ba basa Shiri ko kadan gashi bashi da kunya wanke ta yake sol. Yau duk Wanda Yazo biki na kusa da na nesa duk sun tafi sai iya Yan gidan,Hamra ita tasa masu aiki suka gyara part din Auta tsaf ko Ina yana kamshi ta hana Salma yin aiki ganin ta sawa kanta damuwa tunaninsu alhinin rabuwa da gida ne. Mami har can taje tayi mata nasiha sosai karshe tace ki dauke mu Iyayenki Dan Allah ba babanci kuyi hakuri da juna aure sai hakuri,Idan ya Miki laifi kizo ki fada min kinji,Salma taji sanyi ko ba komai iyayen Nawaf mutanen kirki ne har mamakinsu take gasu masu kudi amma ba wulakanci,tana mugun son Wise da ni Rabi da su Star sabo da ta ganmu Yan harka ne har wasa muke mata muna tsokanarta. Mami zata fice Salma tace ina matar Yayan me gidan nan? Mami tace waye megidan nan a kunyace ta kama Salma tana kasa da Kai tace Auta,Mami dariya tayi wai Auta ne ya zama me gida yanzu ta sake yin dariya tace tana gidanta,au ba a nan gidan take ba? Mami tace ae mana ku ma nan gaba zaku koma gidanku Idan an gama ginawa,Salma tace ina sonta wallahi ita da kawayenta da Wise take suna da kirki,Mami tace Wise Kanin Baffa take aure a takaice ta Dan bata labarin su,tace yanzu dama su Aunty Sultana sun girmi Me gidan nan,dariya ta sake kama Mami Idan tace wa Auta me gidan nan wani dariya ce take kama Mami,tace ai shine Auta,tace uhmm i see amma ya fisu girma ma kamar shine Babban, a ranta tace harda gemu da saje,Mami tace Dan Allah ku zauna lafiya,Salma tayi godiya sanye take cikin Atamfa super black and white tayi mugun kyau dama abinka da me kyau gata yar dagwas da ita matashiya. Mayafinta ta gyara tare da rufe kanta ciki ta zauna a tsakiyar bed,Wise ce ta shugo tana mata turaren daki iri iri, Salma ita Baso ta tuna sai kuka take,Wise tace kyayi ma Kya gama Yan banzan Yara sai balagar zuci da Miji ya shugo za ajiku lakwas kuna karbar Antena, Salma tana kuka bata gane mene Antena ba. Auta kuwa wanka yaci cikin wata Gezna ruwan Zuma ya tsula kyau yana kamshi ya gama Shiri ya zauna a bakin gado yana latsa waya a fili yace duk da cewar ba abinda zanyi wa Amarya amma da kunya yanzu kawai sai Mami taga na nufi part din Amarya ai da kunya sai da nace abokaina su rakani suka ce an Daina yayin raka Ango yanzu,Ina zan Saka kaina da kunyar Mami,yanzu Ina shiga shike nan ko banyi komai ba za ace nayi wani abu na zama Dan Iska,wayyo pillow ya jawo ya rungume yana cewa wayyo kunyar Mami waye zai rakani gashi ko kazar ban siyo mata ba ni ta Ina zan fara ne. Tashi yayi yana gwada yanda zaiyi Idan ya shiga ya sha kunu ya bata rai ya furta kawai cewa zanyi Salamulaykum sannunki,da sauri yace nooooo Sallama zanyi da yanga na ajiye mata ledar kajin nace good night,a'a ai Kuma ba tsari kawai muyi fada tunda ba Sona take ba Nima haka,nooooo Auta nutsuwa zakayi Kaine fa namijin, mijinta a kasanka take behave well,yace uhmm hakane tabbas,yace yanzu zan fita Allah yasa kar na hadu da Mami,a hankali ya Bude kofar yana sanda yana lallabawa kamar barawo wai zai tafi part dinsa kar a Ganshi da kunya,da sauri ya dawo dakinsa kamar Wanda za a kama,sake gwadawa yayi har ya fita ya sake dawowa yana dariya yace wlh bazan je ba bazan iya ba,can Kuma yace haba karya ne Auta Kaine fa Dan zamani haba ka waye kunya ma tuni muka cillar da ita,kwanciya yayi a gadonsa ya ja pillow ya rungume Mami ce ta banko kofar ta shugo dauke da katuwar ledar nama da kayan sha,uhm Auta Dan gata auren gata,Mami tace wai uban me kake Jira ne jiya fa baka je ba sai da Hamra suka kwana ko da matsala ne? kamar kana boye min abu,Auta duk zumudinka ka zauna jiya baka je ba yanzu uban me kake a nan ka bar yar mutane gashi har 10pm sai Wise na tura ta tayata zama,tashi ka tafi muje oya,Auta yace ni dai Mami wayyo yana yarfe hannu,dariya ya bawa Mami yace Mami zanyi kuka nima,muje Mami ta jawo shi ta rufe kofar tace kayanka an Kai can komai yana can muje,suka fito yana wani tirjewa yana sangarta,Mami tace zan mareka muje,suka tafi har bakin kofa ta kaishi tace kayi Addua ungo ta Mika masa ledar ya karba,ya juyo yana kallon Mami tace kaje,Rungume Mami yayi yace I love you Mami Babu kamarki,I will miss you gobe baza kizo ki tashe ni a bacci ba? Dariya Mami tayi tace ga matarka nan,mu kwana lafiya,tsokanar Mami yayi yace Mami ta juyo tace na'am yace hanyar ta Ina zan bi? zagi ta auna masa, ya shige ciki yana dariya har ya rufe kofa ya sake budewa yace Mami da karfi,ta juyo yace Good night kice Ina gaida Baffa,tafiyarta tayi,yana juyawa yaga Wise ta gama turaren tace Ango a bi yar mutane a sannu,Auta yace Mama karama karki bani kuka,Wise ta fice tana dariya ta musu sai da safe. A dinga sharhi please shine godiyata ni AsmaBaffa 08061929616 [8/15, 9:51 PM] AMINA KABIR CAPS: 'YAR AIKIN KARUWAI 2 MATAFIYA BOOK 2 51-55 Official AsmaBaffa SADAUKARWA GA ZAINAB USMAN *MISKI 3in1 Alfirdaus* Albishirinku original miski daga *Egypt* miskin da koda yaushe Kuna yabawa dashi yana dauke 1.*Musk oil* ana shafawa agaba bayan gama al'ada inda hali za'a iya ringa sawa Koda yaushe yana maganin infection yana gyara gaban mace sosai ko yaushe gurin yakasance cikin kamshi bayaga haka sunnah ne amfani da miski 2.*Musk cream* Ana shafawa ajiki gaba daya musamman wajan cinyoyi yana sa jikin mace koyaushe yakasance cikin kamshi kuma yana gyara fata, yasa tayi laushi 3.*Turaren tsarki* wannan turaren karshe ne ba lallai se bayan gama period ba koda yaushe zaki iya rinka tsarki dashi yana gyara gurinnan sosai, kuma ana shafawa a hammata yana kawar da da wari karku bari abaku labari Masu bukata ku ne wannan number 09065959708 Page naku ne Sadiya Muhammad Zakiyya Bello Badimahd238 Gwaggonsu Amina Maman Ibrahim Dr Suhailat Hussein Armai. Auta ciki ya shiga tare da haurawa sama direct dakinsa ya bude bata ciki ya dawo daya bedroom din ya tura kofar a hankali ya iske Salma tana uban kuka ita Baso take tunawa,Baki Auta ya tabe ya karasa ciki yace sannu da aiki ya bude ledar ya dauki abinda zai iya ci ya ajiye mata sauran yace ayi kuka lafiya,Salma wani takaici yasa tace sai anyi din Ina ruwanka dani, babu abinda ya shafeka da ni,juyowa yayi yace who even care about you kalleki Dan Allah ya ja tsaki, Salma kuma ta furta Karka sake ka shiga harkata,Ido ya tsura mata yace ni na Miki kama da ajinki? Salma ta juyo ta kalle shi tana yatsina tace Karka zo har dakina kace zaka fada min magana,dariyar yake Auta yayi yace Ina ya zama dakinki? Wa zai bawa irinki daki? Babu ni ba kai na fada maka Karka jawo Aljanuna su tashi na hada ma jini da majina, wani beran masallaci da Kai,Auta ya kalleta kawai wato tsabar lalacewa bera ne Kuma na masallaci ma. Auta yace cikin fushi look at this dirty smelling local village girl, idiot ke Idan ban koma Santana naci ubanki ba shege nake useless girl yaja tsaki zai fice Salma tace Kai me nan wajen akuyarka ta kiyayi ramata wlh Nima tsagera ce Baso kawai nake wa biyayya,baki da aikin yi cewar Auta ya fice a fusace ya banko mata kofar kamar zai balla kofar, wani kallon banza ta bi kofar da shi ta ja tsaki ta mike tare da sawa kofar key tazo ta zauna ta baje kayan ciye ciyenta taci ta koshi,Alwala tayi da Sallah tana kallon dakinta a fili tace haduwa kuda a gefen gyambo Inama tare da Baso muke a nan wayyo Allah ta fada saman gadonta tana tunanin Basonta,Auta kuwa ya ja tsaki yafi goma yace Auta ka sa kudinka ka siyo problems da hannunka yace gobe Monday yana da lecture,Alwala yayi bayan yaci ya sha yayi Sallar Nafeela sannan yayi Shirin baccinsa cikin kayan bacci masu santsi Riga me dogon hannu sharara da ita da dogon wasu silver color,saman katon bed dinsa na alfarma ya haura ya jawo wayarsa ya hau Online,Nawwar yana kwance a jikin matarsa ni Rabiah muna danna waya dukkanmu muka ga Auta a Online yayi status ya rubuta Matata tafi ta kowa,Nawwar yayi dariya yace kaji Dan Iskan yaro a wajenka
Chapter 42 · 0% Book details