← Book details Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 93

Sashe 45

Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kuka wai an mata fada sabo da samun waje,Auta a ransa yace dama talaka bai iya samun waje ba,yarinyar da kullum sai an jibgeta na tausaya mata na aureta yau na zama kamar sa'anta ba komai kaima Allah ya Kara maka da Omaira ka aura da duk ba haka ba gadon soyayya tsaki ya ja yace a fili Wanda baiji bari ba ai yaji hoho rubbish ya tashi ya fice. Nawwar ne ya shigo ni da shi cikina ya tsufa sosai,Mami tace daga Ina haka? Nace asibiti muka je muka biyo,Salma tana ta kuka,Nawwar yace lafiya take kuka? Mami tace gata nan tambayeta ta fada muku da bakinta,Salma tana kuka da shesheka tace sh...sh..shine...Nawwar yace shine wa? Shi....nace waye shi? tana goge hawaye tace Me can wajen, na kwashe da dariya nace Auta? ta daga Kai tace shine yake tsokanata har gori yake min,Mami tayi salati tace Salma kiji tsoron Allah Auta ba abinda ya Miki yana zaune kika ce sai ya m atsa Miki ke Zaki zauna kina masa rashin kunya,kiyi ta kukanki tunda ke baza a fada Miki gaskiya ba,Nawwar yace to kiyi shuru za a masa fada kinji,ta goge hawayenta tace to,Mami tace bari na dawo ta nufi kitchen sai ga Auta yayi wanka ya dawo cikin 3qtr da Riga me gajeren hannu, hannunsa daya a aljihunsa daya Kuma wayarsa a rike yana latsata. Salma tana ganin shine ta mike tsaye taga ya nufi kujera ya zauna komawa tayi wajensa tana kallon kitchen kar Mami ta ganta tace tasar min ni nan wajen nake so a nan zan zauna,Auta iya kulewa ya kule amma ya shareta ya tashi ya koma dayar ya zauna Salma ta zauna tayi irin zaman Auta ta harde kafafu ta fito da vivo dinta tana dannawa itama,yana cin chewgum kawai ita ba chegum a bakinta ta fara tauna itama,ni da Nawwar muka zuba Ido muna kallo kamar Film,dariya kawai suke bamu,Auta yana da abin hannu a tsintsiyar hannunsa na Samari Salma ta gyara nata na mata, juyowa tayi Shima ya juyo suka hada Ido gwalo ta masa,Hannu ya Kai zai dauki Remote ta Riga shi daukewa tana sani ta Kai tashar cartoon,Auta ya zuba tagumi da hannu Daya ya ajiye wayar a gefe ji yake kamar ya lakada mata dukan tsiya. Nawwar ne ya Kalli Auta suka hada Ido Nawwar yace Matata tafi ta kowa ya rike hannuna,yasan da shi yake sabo da status dinsa ranar da ya shiga dakin Amarya,tashi yayi a fusace ya shiga kitchen yace Mami ki wa Yaya Nawwar magana tun dazu ya zuga matarsa sai Kallona suke suna min dariya,Mami ce ta fito tace waye yake taba min Baby,Nawwar yace ba ruwanmu daga nace Matata tafi ta kowa,Auta yace wlh da ni yake ai na sani, Mami tace ku tashi ku bar mana gida ta Kori su Nawwar. Mami tana shiga kitchen ya zo ya zubawa Salma rankwashi tare da furta marar tarbiyya yar Namiji,dama tunda Baso ne ya rike ki Ina Zaki hankali,oho maka dai . Bayan kwanaki kadan Salma ganin Auta yana ta zuwa school sabo da kwaikwayo sai da taje gaida Baffa bayan sun gaisa tace Baffa dama alfarma nake nema,yace Ina jinki,Salma tace tunda na gama secondary Kuma result Dina yayi kyau Dan Allah ko yar college ce ka sani,Baffa murmushi yayi yace ki kawo min takardun naki ta dinga murna,dama ta taho da abinta,Mami ta samu itama ta fada mata,tace kinyi hankali Salma Kuma kin birgeni,taje ta dakko takardunta ta kaiwa Baffa Wanda ya kamata a nema aka Nemo mata aka mata registration a Makarantar da Auta yake zuwa bai ko sani ba sai da zata fara zuwa Baffa ya sanar masa,ransa ya baci akace Kuma tare zasu dinga tafiya su dawo,amma department din Salma daban ita microbiology tace tana so shi Kuma Business time table dinsu kusan lokaci Daya ne,har waya Mami ta siya mata me tsada Samsung. Yau Monday da wuri ta shirya cikin Arabian gown peach tayi rolling ta sa jaka arsh da takalmi me Dan tufu Arsh, 9am suna da lecture har Auta,ta fito da wuri ta tsaya a jikin motarsa tana waya da Baso yana masifa karki dameni da Kira fa haba jiya kin kirani yau ma haka wanne naci ne wannan ya kashe wayarsa,Nan take idonta ya cika da hawaye sosai ta kasa cire Baso a ranta sabo da Baso take ta yiwa Auta rashin mutunci ko zai gaji ya sake ta ko ya koreta amma yaki,Auta ne ya fito cikin wankansa na farin jean rigarsa silver yayi kyau ya sa glass me kyau a fuskarsa,ganinsa da Glass Salma hankalinta ya tashi da Mami ta bata kudin Makaranta taki karba amma ganin glass din Auta ta koma ciki da gudu,Sai da Mami taji tsoro tana haki tace Mami bani kudin school din na tuna zanga abin ci, Mami murmushi tayi ta bata dubu Daya,ta fito da gudu,Auta har yayiwa motarsa key ta Bude gaban motar ta shiga tana haki, tsaki ya ja yace da kin sani karki fito ki gani Idan zan jiraki,Salma tace ai dai motar ma siya maka aka yi baka da kudin siya,zaka iya siya ne? Ina kaga sana'a baza ka iya ba,Auta yace Mannerless kawai,ya fisgi mota suka tafi,suna zuwa school din taga Yan mata masu aji sai rububin Auta suke,suna cewa Nawaf kanwarka ce? Salma tana fitowa tace matarsa ce,sai lokacin suka tuna Auta fa yayi Aure suka dinga yabawa da kyawunta wasu Kuma suna kishi,Auta yace muje na rakaki bangarenku suka jera suka wuce suna tafiya yace ba tarbiyya kwaila dake sai jaraba duk kin gado jinin Baso mayya ya hankada keyarta ta kusa kifawa,tace kana wani girman Kai da fadi Kai ga me masoya wani Nawa....kasa karasawa tayi sabo da Baso yace sai taci ubanta Idan yaji ta Kira sunan Miji gatsal sai ta fasa cewa Nawaf tace sabo da Kai Kaine,yar kauye kina birni amma kamar a kauye kika girma foolish girl,har aji ya Rakata ya juya ya koma nasu,duk ajin yawanci kusan ba musulmi Allah yasa Makaranta me kyau tayi ta samu foundation me kyau,wasu suna ta Yaba kyanta suna tambaya amma ke Fulani ce? Itama da turanci ta basu amsa tace Kuma tana da aure,suka dinga dariya suna mamaki dama wai sun San Hausawa da auren wuri yar yarinya sai a ganta da Yara su sai sun tsofe a gida yawanci. Suna gama lectures dinsu na yau ta fito ta sha yawo kafin taga Auta ta hango shi zagaye da mata suna ta duba littafi duk christian ne,Salma ko magana tana zuwa ta kutso ciki ta fisgo Hannun Auta tace tarbiyyar taka kenan harda rike kunnenta kunnenta wato baka jin magana ko muje to,fuska ya bata yace zan karyaki wlh nan ba a gida muke ba ya fisge hannunsa,juyawa tayi ta dinga zaga school tana kallo har ta hango masu Saida glass suna wucewa ta samu Dan fake fake ba me tsada ba Dan dari takwas ta siya ta kafta abinta itama a fuska harda yanga,ta fito waje taga masu siyar da agwalima da kwakwar manja ta siyi kwakwar manja ta wanke da ruwa ta Maida cikin Leda fara,Auta ne ya mata mahaukacin horn da mota ta juyo a fusace taga shine zagawa tayi ta shiga gaba yaja suka tafi tana cin kwakwar manjanta,ta dakko guda biyu ta mikawa Auta ungo ni badan halinka ba,ko kulata baiyi ba haka suka koma gida,ta Riga Auta shiga ciki Mami tace an dawo? tace ae Mami,ke kadai kika dawo? ta girgiza Kai tace a'a da shi muka dawo,Mami sai da tayi dariya again ita baza ta fadi ko Auta ba ma,Auta ne ya shigo ya zauna a gefen Mami Salma ta dawo daya gefen ta zauna suka sa Mami a tsakiya,Auta yana ganin kwaikwayo shi Kam yace wai ke babarki ce? baki ta turo zai kwanta a kafadar Mami Salma ta ture Kansa yace wai mene haka wanne irin iskanci ne wannan ni sa'anki ne wai,Salma tace to da nawa ka girmeni,kwafa ya ja, Mami tace haka kika je Makarantar kuna yi kenan,Salma tace Mami wallahi yayi watsi da tarbiyyarki kullum a cikin Yan mata yake zama bashi da abokai maza sai mata kowacce ta dinga yagula sunansa anyhow kowacce da tazo shi, shi,Mami tace me yasa bakya fadar sunansa ne? Salma tace fada aka min akace ba kyau, Mami tace to ga Auta,ga sunaye nan ki sa masa mana wani a ciki,Salma tace wannan zanwa suna ai sai dai na kirashi da mugun bawa kawai,Auta yace marar tarbiyya,Mami tayi dariya ta mike tace sai kuyi ai kunga tafiyata,Auta ya mike tace Mugun bawa, yace marar tarbiyya. Cele ce ta duba riyal biyu dinta bata ganta ba Kuma a saman bed dinta ta ajiye fitowa tayi tsakar gida akan riyal biyu kacal tana cewa Allah ya tsiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiinewa Yan gidan nan shegu Yayan madugo,baza Kuga Annabi ba duk wacce tasan ta dauka ta fito da ita wallahi ko ta hadu da fushin Cele yar mutanen Kaduna,wacce tasan ta dauki riyal biyu ta fito da su ko ta hadu da Halin yar mutanen Kaduna,akan haka sai na tafi Ka'abah nayi dawafi,wallahi duk wacce bata fito da ita ba sai naje nayi dawafi cikin mace ya kulle ta mutu duk shegiyar data San ta daukar min riyal biyu ta fito da ita ba mutunci gumina ce ba haramci na aikata ba na samu,banyi madugo an lagudeni na samo ba,banyi kawalci ba,ba wajen boka naje ba sana'a nayi na samu gumina nace,Babu mutunci ba tsohuwa ba yarinya wallahi a fito min da kudi baza ku amfane ni ba, 'ya'yan wata shegiya, 'ya'yan wani Dan banza,wacce ta kawo Cele tana zaune duk suna nan kowa yayi shuru sai wacce ta kawo Cele tace Dan Allah dakko kayanki wallahi ni na yafe Miki kudin haya zan biya Miki zaman da kikayi hada kayanki ki tafi,Cele tana wani jingina da bango tana dagowa tana komawa tana fari da Ido da bala'i tace ba Dan Iskan,Babu yar madugon da ta Isa na bar gidan nan zama daram sai sanda Allah yayi tashina Ina nan,Kuma bance ki biya min kudi ba yawwa ficikarki ta haramci bazan ci ba, Yayan masu baki da kunu ma basu Isa ba,Raliya tace ke wallahi ki kiyaye mu ni tunda naga harkarki ba mutunci
Chapter 45 · 0% Book details