← Book details Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 93

Sashe 26

Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

lale marhabin marhabin lale lale ta kwalawa Rahma Kira tace kawo musu ruwa mana,Ni Kuwa mamaki ya kamani ni sunki kulani Amma Nawwar da Auta shi Kamar sune Yan uwansu,Abba yace Allah ya muku Albarka babarku tayi farar haihuwa gaku maza Kuma gaku Kuna Kama da alama dai wa da kani ne,Auta yace ae nine kanin shi wannan yayana amma da kadan ya girmeni Wai Nawwar ne ya girme shi da kadan shi da matan ma su Sultana sun girme shi aure kawai za a musu sun girma,domin su sun shiga University tuni ma,Auta ya kalli Rahma a ransa yace wannan kwaila ce kirjinta ba komai sai tsayin kafa,Raheema ce ta fito itama ta gaida su Suka amsa Auta itam ya Kare Mata kallo sai kace munafuki a ransa yace wannan Daya tayi Mata kwari ta tsunbure baza ta girma da wuri ba kafin ta murmure za a dade itama dai kirjin ba komai kamar faifai ita kanta nonon take bukata a shayar da ita Ina zata Iya shayar da kamata Ina,Nawwar Yana kallon abinda Auta yake Yi na kallon matan hararar Auta yayi,da sauri yayi kasa da Kai da sauri. Ni Kuwa Ina Shiga Bilkisu Babba tace Masha Allah wannan twin din Cele ce gaskiya sun zuba min Ido suna kallon suturata da irin kyan da na tsula kudi basa buya idan akwai su,baki na zumburo nace sannunku,Suka amsa da yawwa,Umma na kalla cikin doguwar rigar atamfarta me kyau kamar Yar balarabiya,na durkusa a gabanta nace Ina kwana tana Murmushi ta amsa ta rike hannuna tace ga Yan uwanki ki gaida su, yayyenki ne na juya na gaishe su su Rahma Suka gaishe ni,Omaira ma ta gaishe ni,nace Ina wacce naga hotonta a kasko tana suya? dariya Suka Yi Suka ce Yar jarfa kenan Cele a kasko kenan sunanta Rufaida ana ce Mata Cele Amma fa Cele a kasko ita Yan biyunki ce tare aka haife ku itama ba anan gidan ta taso ba,nace mijina Yana tsakar gida,Aunty Bilki tace ai ya Zama dan gida ya shugo Kawai ayi labarin a gabansa,Nawwar na Kira nace ku shigo,Abba da Uwa Suka tabe baki yace maza da Shiga cikin Mata jeka kuje Kar ace Ina bakin ciki,Nawwar ya mike da Auta tuni kamshinsa ya cika ko Ina yayi sallama ya shigo palon Kato ne,Su Aunty ne Suka tashi suka bashi doguwar kujera shi da Auta Suka zauna. A kasa ya zube ya gaida Umma da su Aunty ma sauran ma suka gaida shi,bayan ya zauna aka kawo Mana ruwa da lemon da su Aunty Bilki Suka siyo Bilkisu ta fita ta shiga kitchen sune suka Yi girki aka kawo mana tuwon shinkafa danya miyar egusi sai meet pie me kyau, nace mun fa koshi,Aunty Bilkisu sai bala'i ai ba sai kin nuna mana mu talakawa bane dama ai mun San bamu Kai kici abincinmu ba kunfi karfinsa amma dai ke in baza kici ba ai su zasu ci,aikin banza duk Dan gidan nan inda yake sai ya nuna hali haba,Baki na bude nace ni daga nace na koshi sai ki kamani da fada haifata Kika yi,ciki ne dani ko baki gani ba abinci sai mai da yaji nake ci gashi Nan me cikin ki tambaye shi kiji,Nawwar yace kuyi hakuri bata cin abinci sai mai da yaji,Umma tace ko kunya babu Rabi kike ko,cikin shine abin kunya ni da ba shege nayi ba da ubansa kowa yasan dai me akeyi a samu ai aure nayi,Nawwar shi Kuma yace ae da auren mu Umma,su basu Saba Jin rashin kunya haka ba da tarbiyyarsu Kuma a Arewa suke da saukin fitsara sannan a gaban Mahaifiyarsu Suka taso,Bilkisu ta share zancen tace amma ai kwana zakuyi ko? Nace a'a Ina Zan iya kwana gashi nan ku tambaye shi idan zai yarda to bai Saba barina unguwar kwana ba na tafi na barshi da wa da dare fa a'a bazan kwana ba nikam, Umma tace ke a hannun wa Kika taso ne haka Rabi baki da kunya haka,Baki na turo nace ni nace ku jefar dani da Kun San da haka kuka jefar dani sai yanzu an ganni na girma na zama abar moriya za ace bani da kunya tuntuni ba sai a rikeni a bani kunyar ba,shi waccen mutumin me Jin haushina waye ne haka,Umma tace babanku ne mahaifi,nace Ni ku bani labari na sani nice yarku ko ba ni bace,Umma Ido ta tsura min ta fara bamu labarin asalinmu. Tace Mahaifinku dan Asalin Nasarawa Lafiya ne a wani kauyen Fulani rugar Jam,Mahaifinsu da Mahaifiyarsu Abu wacce ake Kira da Uwa su Tara Suka Haifa bakwai Mata biyu maza yanda ita kanta Abu Uwa kenan dukkan Iyayenta Mata Suka Haifa mutum Daya ne Namiji a ciki su hudu Mata namijj daya Kuma duk suna nan da rai ita Uwa itace Babba a cikin Yan uwanta sai Sa'ade,Baballe da Binta Uwa Kuma data yi aure danta daya tal ta Haifa a Duniya Muazu shine Mahaifinku Abba kenan tun yana matashi mahaifinsa ya rasu Bayan sun dawo Kaduna da Zama sakamakon fada da ya barke tsakanin Fulani da manoma gaba Daya kusan Dangin Mahaifinku suna nan Kaduna Wanda basuyi aure ba ma duk a nan suka Yi aure,Uwa ta Sha wahala da Danta sabo da bata da miji sai Yan Uwa ne suke taimakonta lokacin ma a gidan haya take,sabo da danta ta kasa yin aure Wai Kar ta auri wani mijin ya tsanar Mata da tunda mazan yanzu ba kowa ke son yayan wani ba,tana sana'oi kala kala da haka ta dauki nauyin Danta har ya gama Secondary sannan aka turashi makarantar Allo can Kano har ya Zama katon Saurayi Yana Almajirci ya samu wata Hajiya ta dauke shi Yana Mata aiken gida a can har ya Isa aure a wancan Zamanin kenan.
Chapter 26 · 0% Book details