← Book details Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 93

Sashe 74

Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a hankali ya Saka key yana wani sanda yanda ba me ji,ya dawo saman gadon yace kina jin abinda nake ji kuwa Babar Mairo ?Gwaggo tace yanzu nake Shirin tambayarka dama, su gwaggo sun Saba fetsararsu a gida,Dagaci yace nan a gidan mutane muke kar naji kince uhum ranki zai baci,tace to dagaci suka dinga Abu daya an zaci bacci suke yi har wurin magriba Basu fito ba Babu Wanda ya Kuma neme su sai magriba ya fito cikin shirinsa na yadi me kyau zai tafi masallaci Shima ala dole ne Dan a gidan wasu yake shi yasa,Gwaggo ce ta fito itama ansha Atamfa ta zauna,Cele tana kallon su tana dariya a ranta tace wlh da ace Abba ma tare da Umma suke sai na saka musu,Ni dai ban yarda da Cele ba Sam idonta na faka na bude Jakarta na dauke maganin gaba daya na boye. Auta ne ya Kira Cele ta fita suna compound yace Cele tamu,tace kaga ka fadi abinda yasa ka kirani Kai ya Sosa yace Salma taki yarda Dani ko first night har yanzu ta Hana,Cele ta sha mamaki tace wai da gaske take dama? Yace ae da gaske take mana cewar Auta,Cele tace Ina zuwa ta koma ta duba Jakarta ba magani tace wai Ina maganina ne? Nace wanne? Karki Raina min hankali Rabi ki bani abina babu me bude min jaka sai ke,Nace ni ban yarda dake ba Cele baki da tsoro muguwa kowa Zaki iya sa masa,Dariya tayi tace Dan Allah ki bani Auta yace wlh baiyi first night ba Salma taki yarda,Nace gaskiya tana zaluntarsa yarinyar nan a basu su sha su biyun,aka Dan zuba a cikin cock,Na dauke ragowar na boye fafur na hana Cele maganinta sai hakura tayi ta kyaleni ta kaiwa Auta,Auta yace na gode,tace Kai jeka ka jefa kwallo a raga,Auta yace daga yau sunana Maradona, nine maradona ma yau kwallo sai ta shiga raga,Auta ya tafi Yana zuwa Salma tana Shirin bacci yana shan abinsa a hankali yasan dole ne ta karba halin Salma ya sani,ai kuwa tace bani na sha Nima,ba musu yace gashi ta zauna a gefensa tana danna laptop dinsa tana Shan abinta har ta shanye,15mnt Auta ya birkice itama tana ji amma tsoro ya hanata,Auta ya daure bai kulata ba,Salma kanta ta Sosa ta dan doki kafadar Auta tare da girgizawa tace Auta babban yaro,Auta me abin mamaki,ta sake gigirza Auta tace Auta babbar harka,uhmm su Auta masu Antena Aunty zokala inyeeee,dariya ta kwacewa Auta sosai ya shiga kyakyatawa,Salma itama dariyar tayi tare da furta your are always on my mind,Auta ya shiga sarrafata sabo da tsoro har gardama tayi taki yarda,sai da taji Sako iya Sako bata San sanda ta bada Kai ba,yau ma an sha kuka ba a cewa komai amma ba irin na farko ba. Dagaci yau ya ebi harka,Iyamami da Sabreen kuwa kwana suka yi rawar Banjo a daki ba Miji. Kwanan su Dagaci uku suka je gidan Rabi suka gani sannan suka tafi da sha tara ta arziki. Bayan tafiyarsu da kwana biyu Cele da Ahsan suka tafi Kaduna,ita Kuma Salma mahaukacin gidansu da ya warke Yazo tare da Baso da Yan uwansa. Suna zuwa aka sauke su na fito gaida su ni da Nawwar sai naga Alhaji Kutama tsohon Wanda aka taba daura mana aure tun da ya tafi kasar waje bai dawo ba sai takadar saki ya Aiko min da shi,suna kama da mahaukacin da ya warke da Alama Kaninsa ne,Nawwar ya kalleni yace kin sansu ne nace ae nazo na zauna,Shima Alhaji Kutama mamaki ya kamashi yace Rabi ko ba Rabi bace? Nace ita ce mana Ina yininku muka gaisa yace me kike a nan? Nace aure na haihu ne nazo gidan iyayen mijina wanka,yace wow masha Allah,Nawwar na kalla nace shine Wanda aka taba daura mana aure baya kasar ya Aiko min da takarda,Nawwar sai kishi ya tashi ya wani canja fuska yayi kicin kicin,Alhaji Mukhtar mahaukacin da ya warke yace dama itace baiwar Allah kiyi hakuri,nace ba komai ni da mijina yanzu ai ya wuce,Salma tazo suka gaisa Alhaji Mukhtar yace ga Yar Albarka itace ance me bani abinci Salma tayi murmushi tace gaskiya naji Dadi daka warke bari na Kira mijina ta mike ta Kira Auta Yazo,suka dinga kallon Auta Dan matashi an masa aure su Kam abin ya birge su,Alhaji Mukhtar yace shike nan kunga sai ku girma tare da yaranku,irinku ne za a ga danku kamar kaninku,muka yi dariya mukullum mota ya mikawa Salma yace yata ga kyautarki,Salma ta karba jiki na rawa tace mukullin mene? Kar dai kace mota? Yace itace na siya Miki,Salma murna da godiya dai ba a magana,tace Aunty ku tayani godiya,dukkan mu muka masa godiya,Auta harda rungume Salma yana mata murna,muka fito ganin mota galleliyar gaske fara sol cikin motar komai pink kalar ta mata,zata Kai ta million uku,Salma ta dinga Murna ta mikawa Auta key din tace boye min,muka kwashe da dariya Sabun shiga motar ma baza ta iya ajiye key din ba da kanta. Baso ne ya ja Nawwar gefe yace ya maganar tamu? Nawwar yace tana nan tasan da zuwanka Karka damu. Bayan mun dawo Palo mun zauna dukkanmu Alhji Mukhtar yace Salma Ina matukar godiya ke da Baso Allah shine zai biya ku bani da bakin gode muku domin a zamanin Kaci nama Kuma ka bawa mahaukaci Shima yaci naman,duk abinda Kaci Mahaukaci sai yaci ba ma Almajiri ko wani ba mahaukaci fa ai sai dai Allah ya Saka muku bani da abin biyanku,yau Nima zan baku labarina kuji a takaice Wanda ko Baso ban fadawa ba,Baffa da Mami muna zaune da su, ya fara kamar haka Mun kasance mu takwas Babar mu ta Haifa mata shida mazan biyu amma dukkan mata tun suna Yara suke mutuwa sai iya mu biyun maza Allah ya bar mata ni da Kaninsa gashi nan Alhaji Kutama,bayan Babanmu ya rasu Mama itace gatan mu muna Yara lokacin baza mu iya yiwa kanmu komai ba,gashi bata da karfi Ganin zamu sha wahala baza mu samu ilimi ba ta fara sana'ar wanki da guga,tana yin Kuma kosai a bakin Tasha da wannan sana'ar ta dauki nauyinmu muka yi i limin boko tun daga primary har degree ni da Dan uwana,Muna dawowa daga bautar kasa ta tattara gadonmu da muka gada ta siyar ta bawa kowa kudinsa ya fara sana'a cikin ikon Allah dukkan mu sana'ar kasuwancin ya karbe mu kudi kawai muke samu Alhaji Mukhtar ya fashe da kuka da kyar ya saurara yaci gaba da labarin yace Mama tana kallo muna samun kudin bata taba cewa mu bata sisinmu ba Kuma bata fasa sana'arta da ta Saba yi ba,maimakon mu hutar da ita amma bamu yi Hakan ba,muna kallo tana wahala dai amma sai Gini ma muka yi muka yi aure tana can gidan gado Wanda aka mutu aka barmu a ciki gidane rubabbe kamar zai rufto. Har muka Kara bunkasa tana sana'arta kyautar duniya Idan mun mata mu bata dubu biyu,Amma bata taba complain ba sai dai tayi ta sa mana Albarka tana mana nasiha akan mu dinga yin sadaka muna taimakon talakawa tana nuna mana halaye na kwarai amma kwandalar mu ba Wanda yake ci to ita kanta bata ci bare Yan uwa bare Kuma a Kai ga talaka daga mu sai matan mu sai yayanmu Sai Kuma dangin matan mu,har arziki na yasa na Gina gida a Abuja katafaren gida haka uwata tana lalataccen gidan nan ga karfinta ya kare amma tana sana'arta bamu dauke mata komai ba, Kuma Babar Matata a gidana dake Abuja take zaune har Yan uwanta uwata Kuma tana nan tana fama. Shi Kuma Alhaji Kutama Kano yayi gida sabo da sana'arsa gwara shi ma yana Dan Kai mata shinkafa da galon din Mai watarana Kuma ya fini yawan zuwa ganinta sannan yace Idan zata sha shayi taje wajen me shayi ta karba a ajiye masa list Idan Yazo zai biya kudin,amma Idan Yazo gari me shayin ya fada masa ya dinga bala'i kenan yana cewa shi ana Tara masa bashi da yawa,sai da ya zama Mama ta Daina karba ma gaba daya,duk layin nan zaginmu ake ana tsine mana Albarka mun bar uwarmu wacce ta sha wahala da mu. Tun Ina zuwa ganinta bayan watanni sai na dawo ma sai na shekara bata ganni ba,shi Kuma Alhaji Kutama yakan kwashe wata shida kafin taga wani,Idan muka je tace ko baza ku bani komai ba ku dinga zuwa Ina ganinku Dan Allah ai naji dadi amma bamu canja ba. Yace haka muka kwashe shekaru masu yawa ba kasar da bama zuwa amma ita ko aikin hajji bamu kaita ba Wanda nayi imanin da mata ta Haifa da taga gata duk da cewa mazan ma da yawa akwai masu Albarka amma imanin mata na daban ne,kwallarsa ya goge yace ana haka watarana gidan da take ciki ya rushe Allah yasa ta dan fito amma duk da haka Gini ya zubo mata a kafa har bata iya tafiya sai Jan gindi,a haka Yan unguwa suka nemi number ta,kasan mu Hausawa ko ya mutum yake da kudi to baya daga waya sai yaga dama,Kiran duniya ban daga ba,haka ma Kutama bai daga ba,har wani makwafciya tana da Hali maaikaciya ce itace ta bata daki a gidanta take zaune ita take dawainiya da ita kafar taki warkewa,gashi mu bamu je ko ganinta ba bamu San ma a wanne hali take ba,daga mu sai matanmu,tana can tana Jinya tana Shan wahala amma wlh matar nan itace take mata komai inda kasan itace ta haifeta,Mijin matar Ashiru Kuma yana bakin kokarinsa Shima,a haka kafarta har ta rube aka ce sai dai a Yanke,Mijin matar har Abuja Yazo da Kansa ya sameni ya sanar min Halin da ake ciki amma ban je ba sai dubu ashirin na bashi nace ka Kai mata aiki ya min yawa zanzo ne,Mutumin ya tsaya yana kallona yace Alhaji Mukht baza ku gama da duniya lafiya ba,tun kuna Yara ba abinda uwarku bata muku ba amma wallahi baku da Imani Kuma tun a duniya sai kunga abinda zai same ku baza ku gama da duniya lafiya,wallahi duk me wulakanta iyayensa baya kyautata musu to ya shiga uku bazai ga dai dai a rayuwarsa ba,Uwa guda wasu ma nema suke Allah
Chapter 74 · 0% Book details