← Book details Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 93

Sashe 46

Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba arziki a cikinta na fita shirginki bana kulaki karki sa Dani wallahi zuriarki kaf har na kabari sai na zage su tas. Bazawarar dariya Cele tayi tace ai ni bari kiji bana cecekuce budawa nake da mutum in daka mutum in lugude shi, Allah na tuba bare ke da kike kamar karmami duwawu kamar kaskon soya manja,Idan kin Isa mu hadu a filin badar sai muyi yaki a can,sai da su Samira suka yi dariya,Samira tace fadan ma sai anje filin badar? Ai ta tabbatar ni bada wasa na fito ba,ke a yanda na fito nazo takari daidai nake da ko uban waye,ni ba a tabani ba ma ni kadai bala'i nake wa kaina bare an kulani an shiga gonata ,akan Riyal biyu ta billahillazi ji nake kamar zanyi aman wuta gwara ko wace ta kiyayeni,ji nake kamar na zama dragon na muku feshin wuta karku sake kaini bango wallahi yau baza ku runtsa ba tunda baku da mutunci abu ya hade muku biyu ga madugo ga sata wannan wacce masifa ce riyal biyu ta a dauke min a dake ni Kuma ace za a hanani kuka,mace daya ce ta min abinda bana so na kyaleta a garin nan Kuma itama na Riga na Mika karata wajen Allah,Meenal ce ta zaro riyal biyu tace indai akan wannan ne gata ni na baki kyauta,Cele ta tsani Meenal ta karba ta hada kudin da kan Meenal ta maketa sosai tace na tsaneki wallahi mayya bana so ai ni dake ba sauran mutunci mun kulla kenan tunda kika taba min dukiyar maza na wallahi bana sonki,Dattijan sukayi shewa suka ce au nono ne dukiyar maza, wannan jarabar nono sai kace an taba wata tsiya,ana kera shi ne a gidanku?Cele ta tambaya, Suka yi shuru. Cele bala'i take ba ji ba gani sai ga matar da Ahsan ya turo da botikin Awarar ta kwala Sallama Suka amsa tace wacece Rufaida Cele? Cele ta daga hannu tace I'm ya akayi ko kece kika dauki riyal biyun yanzu ki karbi rabonki? Matar tace a'a ni wani ne ya aiko ni yace a kawo Miki wai naki ya fashe gashi,Cele ta karba sak irin na awararta,tana mamaki tace waye wannan haka ni ba mashinshini ba tunda nazo garin nan banyi masoyi ba sai Yan madugo,Matar ta bude baki tace Subhannallahi Allah ya shirya su ashe ba Neman kudi suka zo ba lalata suka zo yi kusa da dakin Allah wallahi irinsu ke bata wasu gaba daya ake mana kudin goro,duk sun bata gari ana kallon takari marasa daraja,Cele tace ai mutanen banza ne wallahi da dare haka suke lalubeni wata tsinanniya ma ta taba min albarkatun kirjina Ina bacci ai kuwa na tsine mata albarka zata gani Kuma,Matar tace Allah ya shirya wannan ba gidan zama bane in kin samu dama ki tashi,Cele tace so nake dukkansu na koya musu darasi gasu nan har tsofaffin banza. Matar tace to ni zan tafi,Cele tace wai bakar fatar ne ya baki? tace ae baki ne yace a kawo Miki zaizo yace,Cele tace to maybe a masu siyen Awara ne na gode tsaya na baki tukwici mana ta zaro riyal biyar tace ungo tukwici,haba sai kace yarinya tace Kya ci ko Altuffa,ko Laban wa buskota wai biscuits,matar ta karba tana dariya da godiya ta tafi. Washe gari Ahsan wanka ya sha cikin kana nan kaya yasa Driver ya kaishi inda Cele ke zama tana siyar da Awara,yayi parking yana mota yana kallon Cele tana zuba ciniki,kudi ya bawa driver yace yaje ya siye awarar duka ya rabawa masu siya kyauta,Driver ya fita yaje ya samu Cele da Hausa yace Hajiya nawa ne dukanta? Cele tace duka Kuma botiki biyu fa,yace ae sadaka zanyi naga ana siya zan rabawa alumma Cele ta fada masa ya bata kudin gaba daya ta tashi tana gyara mayafinta bata San da mutun a motar ba taje jikin mudubin motar da Ahsan ke ciki a zaune tana gyara mayafinta ta zaro lipgloss a jaka ta shafa ta gyara mayafinta da tayi rolling ta jingina da jikin motar tare da harde hannayen ta a kirjinta,Ahsan yana kallonta shi fes ta ciki bakinsa ya dora a jikin glass ta saitin bayan Cele yana ta zuba kiss bata sani ba ji yake kamar ita yake wa kiss din,sai kissing din glass yake. Ayi hakuri chaji ne ya kare A dinga sharhi yafi Godiyar nan AsmaBaffa 08061929616 'YAR AIKIN KARUWAI 2 MATAFIYA BOOK 2 56-60 Official AsmaBaffa SADAUKARWA GA ZAINAB USMAN *MISKI 3in1 Alfirdaus* Albishirinku original miski daga *Egypt* miskin da koda yaushe Kuna yabawa dashi yana dauke 1.*Musk oil* ana shafawa agaba bayan gama al'ada inda hali za'a iya ringa sawa Koda yaushe yana maganin infection yana gyara gaban mace sosai ko yaushe gurin yakasance cikin kamshi bayaga haka sunnah ne amfani da miski 2.*Musk cream* Ana shafawa ajiki gaba daya musamman wajan cinyoyi yana sa jikin mace koyaushe yakasance cikin kamshi kuma yana gyara fata, yasa tayi laushi 3.*Turaren tsarki* wannan turaren karshe ne ba lallai se bayan gama period ba koda yaushe zaki iya rinka tsarki dashi yana gyara gurinnan sosai, kuma ana shafawa a hammata yana kawar da da wari karku bari abaku labari Masu bukata ku ne wannan number 09065959708 Page naku ne Jannat collection Mhiz Auwal Faeezah Jalloty Zuwairayahaya8 Ameesha couture Hammad shine driver Ahsan,duk Wanda Yazo siyen Awara kyauta ake bashi ta dai dai kudinsa da zai siya,sai data kare tas ya bawa Cele botikanta ta karba tace na gode ta juya ta wuce gidan Kaka,tana tafiya tana irga kudinta tana Wakar larabawa ta Nancy ba uwar data iya kawai haukarta take fada , Ahsan yana binta da mota bata gane ba har gidan Kaka a kofar gida ta tsaya gidan dogon gida wajen Hawa goma sha nawa amma Cele haka ta dinga kwalawa kaka Kira,Kakaaaaaaaaaa kamar me Kiran Sallah,Kaka ne ya dawo daga masallaci da gudu tunda Cele ta ganshi da gudu tace to shegun Suna bayansa muke nan kullum a gudu sabo da kana kasar mutane itama kafin Kaka ya karaso tayi cikin gidan da gudu,Kaka ne ya shigo a hankali,tace Kaka sun tafi? Yace wa? Masu kame wanne kame Kuma wasa jini fa nakeyi ni sabo da na Kara kwarewa a gudu,Cele tace wallahi kaban tsoro na zaci askarawa ne wannan gudu haka haba Kaka,Kaka yace yau naji yar jakar Uba Idan ban fara koyon tsere ba sai yaushe,kina ganin garin nan irinmu gaba daya mun zama Yan tsere ba yaro ba babba ni yanzu motsa jikina zan dinga yi kullum da safe,Cele tace Kaka,yace Naam tace Ahsan din yaki zuwa yaki dawowa bakin Dan Iska wlh Idan bai zo ba sai na masa rashin mutunci muna yin aikin hajji zamuyi tafiyar mu,ni yanzu Number din Umma ce bani da ita bani data kowa,Kaka yace Allah ya kawo shi yar nan Cele ko aure kike so ne yanzu? Cele tace ae yanzu hankalina yayi wajen aure Kaka,Nima inyi Auren nan na shiga gwagwarmayar rayuwa,in hau gadona ni kadai na kwanta,Kaka in dafa abinda nake so kana gidana dakinka daban duk zani muna tare ko? Kaka yace ke kadai ma zaki kwanta a gadon haka ake auren,dariya Cele ta saki tayi dage da kafafun ta tare da dafa kafadar Kaka kamar sa'anta tace na sani Kaka ai na sani wai irin yar kunyar nan. Allah ya kawo na gari tace Ameen. Cele da Kaka suka fito tace muje mu fara siyayyar tsaraba kafin muyi aikin hajji mu tafi Nigeria ko,Kaka ya bita hannunta rike cikin na kaka suna tafiya tace Kaka Allah kayi kumatu duk ramarka ji yanda ka Dan ciko,Kaka yace Madara wasa ce? Zaki da maiko ba wasa ba Yar nan baki ga nayi kiba ba,ke kuwa har yanzu kumburin nan bai barki ba Cele ko sai an Kara Miki jini ne? Cele tace Alla ya kiyaye inshallah zan murmure ai akwai abinci me kyau, Shagon da suka shiga suna siyayya Cele tana ta jidarwa Ummanta kaya da Yan uwanta sai gani suka yi masu kantin sun shigo sunce komai ya musu su zaba an biya kudin,Cele tace waye haka ne? Kaka yace oho ke bari na gwangwaje kaina nima cewar Kaka ya dinga jidar kaya Cele ma haka masu tsada tunda sunji ance komai su zaba an biya sai da suka gama sannan aka shirya musu a Leda suka tafi,Ahsan yana ta jin Dadi ya riga ya biya mu su,suna tafiya a hanya sunyi nisa wani balaraben ya tare su a hanya ya Mika musu kudi da dan yawa yace sadaka bayan Ahsan ne ya aiko shi ya kawo,Cele ta Kalli Kaka tace adduar mu fa ta karbu a dakin Allah,lokacin kudinmu Yazo cewar Kaka,yace muje mu sha abin nan me sanyi iskrim yake ko me,Cele tayi dariya tace Ice cream Kaka,yace kune Yara mu Kam bakin mu ya gaji da miyar kuka tun muna Yara,suna zuwa wajen Ice cream din sai da suka gama siya zasu biya kudi wani balaraben ya shigo yace ya biya musu su je,Cele daga ji an biya tace Kaka ai kadan muka siya mu Kara,yace mu Kara zasu biya Allah ne yake ciyar damu,suka Kara da yawa aka ce nan ma an biya,Cele tace anya kuwa babu aljani a harkar nan,Ahsan yana bayan su basu sani ba suna juyowa ya juya baya ya tafi,sun zaci kawai wani balaraben ne,amma Cele tace wlh kamar Ahsan wancan Dan banga fuskarsa bane,Kaka yace ke wannan da gani ko a kasar nan me kudi ne Kalli ma kalar jallabiyarsa Kalli takalminsa,Kai Kaka Ahsan dinma haka yake,Kaka ya sheke da dariya yace Cele kina takari Zaki samu kalar wancen ko ta baya ka kalle shi kasan ba karya, ke dai muje a bar zancen,Cele tace shike nan tunda baka yarda ba amma shi Allah ba abinda ya gagare shi zai iya hadani ma da sarkin garin nan. Salma ganin Auta kullum yana motsa jiki Exercise itama sai ta sa hijab tazo tayi ta gudu a can karshen gidan inda Auta yake,Bai kulata bata kulashi kullum haka suke yi da sassafe. Bayan sati biyu yau Salma ta sha wanka cikin kana nan kaya ta tsula uban kyau,jean dogo sai Riga me kyau yau ba school, tana zaune ta harde kafa tana kallo, Mami ta fito tace kin
Chapter 46 · 0% Book details