← Book details Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 93

Sashe 35

Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai ka karba karya kake Oga dole sai ka karba ko na maka dukan tsiya a nan,Nawaf yaga Baso tsakani da Allah dukansa zaiyi yana wani tangal tangal a hanya,hannu yasa ya karba,yace yawwa abokina kaga gidanmu can muje,Nawaf yace kayi hakuri gida zanje,hannu yasa ya fisgo Auta gidansu a gefen kusa da hanya yake,wani gida kamar shagon Samari dakuna guda biyu sai wani daki kamar kango sai yar Katanga da kitchen na langa langa bandakin ma rabinsa na langa langa ne,kofar gidan Kuma ko kofa Babu sai buhun Leda, Nawaf ya bishi suka shiga ko ina tsaf neat,Salma tana wanke wanke a tsakar gidan ga wani mahaukaci a gefe yana zaune yana wasanni yana soshe soshe gashinsa duguzaza da kasumba babban mutum ne zai kai 47yrs, Auta yana ta kallon mutumin,Baso ya dakkowa Auta benchi dogo ya goge masa yana tangadi yace zauna master,Auta ya zauna shi dai,Salma tana aikinta Baso ya daka mata uwar tsawa ta mike jiki na bari yace kawo masa ruwa,Auta da sauri yace na gode Dan Allah, kai ba a mana musu a nan yawwa ke kawo masa ruwa sai ka sha,Nawaf yayi shuru Salma ta kamfato masa ruwa a randa,Auta ya Dan dodana bakinsa a bakin kofin kamar yana sha yace yawwa Alhmdllh na koshi kai har naji Dadi kishirwa ta tafi,Salma tana kallon wayon da Auta yayi tayi shuru dai. Auta yace wannan Mahaukacin fa? Salma tace ae a gari ya tsinto shi,Baso ya daka mata tsawa yace zan ballaki munafuka jibarki kina fama da koshoko me zan ci dake Baba ya mutu ya barmin masifa wlh bazan aureki ba bana sonki,Salma taji kuka ya taho mata tana son Baso matuka a duniya bata taba son wani ba face Baso,Auta shi dai Halin da ya gansu yaji Kuma Salma ba muharramarsa bace gata kyakyawa ta karshen karshe gata katuwa me shape komai ya fita a jikinta son kowa kin Wanda ya rasa fara da ita amma ba fara can ba normal normal dai sai kyawun tsiya kamar me,shi Kuma Auta bata dame shi ba Sam Sahar ce a ransa. Tambayar Salma yayi yace baku da Iyaye ne?Salma idonta ya kawo ruwa tana kallon Baso tana jin tsoro tace ae bamu da su,Yaya na bashi labari? Baso yace cikin dabanci ku kuka sani ko ki bashi ko kar ki bashi duk daya. Salma ta Kalli Nawaf tace mu yan asalin Ringim ne da babana da baban Baso uwarsu daya ubansu daya,su biyu iyayensu suka Haifa,tun suna Yara iyayensu suka rasu sai yan uwa Kuma suna can kauye,cikin maraici suka taso ba irin wahalar da basu sha ba a rayuwa har suka dawo Kano suna Sana'a suka samu gidan haya suka yi aure a cikin gida daya kowanne da matarsa suna zamansu lafiya kuma matan nasu duk Yan Ringim ne dangi ne,lokacin baban Baso shine Babban Haladu matarsa ta haife shi yaci suna Umar ana ce masa Baso,ni kuwa ko cikina Babu lokacin suna zaune har sai da ya shekara goma sha biyar sannan aka samu cikina,lokacin Kuma Maman Umar Baso ta rasu sai Babansa,ranar da Mamata ta haife ni anyi murna naci suna Salma,muna zaune lafiya har Baso ya cika shekara 32ni Kuma ina shekara 18, watarana Mamana Aisha tayi girki shinkafa da wake lokacin ina Makaranta, Baso kuma ya gama iya secondary an turashi almajiranta har ma yana Shirin dawowa ya zama saurayi sai aure,ni Kuma ina Ss3,Mama ta zubawa Haladu Baban Baso abinci itama ta zuba nata taci ta koshi,Sallar azahar tayi da kyar lokacin cikinta ya fara ciwo tana idarwa ta kwanta daga nan ko tashi batayi ba ta rasu,Ranar Kuma Baso ya dawo ganin gida ya zama saurayi ashe ba karatun yake ba kawaii Shaye Shaye ya koya a almajirantar shi,tun yana yaro a boye yake sha Idan baya gida yana can duk an zaci mutumin kirki ne ashe ya lalace illar tura yaro wata uwa duniya da sunan Almajiranta wasu dai ba karatun suke ba,sabo da Babu me daukan nauyinsu yunwa masifa ce ace yaro bara zaiyi yaci ya koshi,Babu tarbiyya Babu me lura da shi bare lafiyarsa duk sai abinda yaga dama. Baso yana zuwa ya samu Haladu Babansa yana Shure Shuren mutuwa ina shigowa Nima da Uniform Dina na iske Mamata ta rasu bata motsi na fito da gudu na samu Baso gaban Haladu yana Shirin tafiya lahira. Haladu Hannuna ya kama ya kama Hannun Baso ya hada waje daya yace Baso gata nan ban muku dole ba amma zanso ace ka auri Salma,ka daure ka auri Salma Kaine kadai zaka rike min marainiya yar Dan uwana da Amana,Karka bari tayi kuka ka aureta ku zauna lafiya ka kula da ita,Karka sake komawa Makaranta ka zauna ka nemi Sana'a kuje danginmu su daura muku aure Karka Kaci Aman....kafin ya karasa rai yayi halinsa, ranar munyi kuka na fitar hankali ni da Yaya Umar Baso, bayan anyi bincike aka gano ashe waken da Umma tayi amfanin da shi ta dafa shinkafa da wake maganin kwarin da aka Saka masa guba ce wacce su dai tafi karfin jininsu tunda wasu sun dafa Kuma basu mutu ba amma su ta musu illa. Salma taci gaba da cewa abinda iyayenmu suka mutu suka bari shi muka tattara muka siyi wannan Dan gidan muna zaune,tace Yaya Baso kayi hakuri zan fadi halinka,yace to yar iska sai kinci ubanki karasa ina ji,Salma tace ni da ka ganni bana jin magana ina da tsokana,shi Kuma Baso kullum Shaye shayensa yawa yake gashi ya iya gyaran machine sana'arsa kenan gyaran machine yana Shaye shayensa amma Kuma ba laifi kullum muna ci mu koshi ko ba Dadi,yana masifa yaki cikawa Mahaifinsa burinsa yace baya so na,ba wacce ya tsana Irina,kullum sai ya dake ni ya zageni ya tsine min ba muguntar da baya min...kafin ta rufe baki a labarinta Baso yace to bana sonki ko dole ne nace bana so, Salma taci gaba tace duk duniya ni ba Wanda nake so Irin Baso ina sonsa a duniya amma yaki aurena,ni ke masa wanki da guga,girki,ebo ruwa,komai da ka sani macen aure tana yi ina masa burina ya aureni,rannan daga tambayarsa yaushe zai kai Sadakina wallahi har targade ya ji min,gashi a haka yana da addini ga taimako,Kaga wancen mahaukacin tun muna Yara kowa ya sanshi a bola yana tsince tsince sai dai baya duka sannan haka zaka Ganshi a unguwa yana bin gidaje da kwanon barar abinci ana bashi sadaka yana ci,Kuma baka Isa ka wanke masa kwanon ba,sannan ko an masa wanka ya dinga ihu yana zubawa jikinsa kasa da bola,sannan baya magana,bashi da inda yake kwana haka zaka ga ruwan sama ya masa dukan tsiya a bola,sauro,sanyi rana duk a Kansa,amma Baso Baba yana rasuwa kaga wancen dakin zaka Ganshi kamar kango to dakine Baso ne ya dakko mahaukacin ya kawo shi,wallahi duk sati sai ya masa wanka,Idan bashi da lafiya shine yake Kiran mutane suna tayashi ya kaishi asibiti ayi masa Allurai,abinci Kuma kullum da kwanonsa ina dafawa zai fito har ya Saba ma. Dakinsa ne leka ka gani har net ya Saka masa amma dake mahaukaci ne sai ya fincike net din ya kwanta haka sauro yayi ta cizonsa, Dan Allah ai ya cancanci a so shi ko? Nawaf yana gama ji yace ya cancanta gaskiya ta wani bangaren ma sai wannan ya zama silar shigarsa Aljanna wannan ba karamun jahadi yayi ba,Baso yana ciccijewa yace ke zan tattaka ki wallahi Allah bana sonta ni bana son kyakyawa,Auta dariya yayi ana Neman me kyau shi baya so,yace kai to sai mummuna? Yace ae ni mummuna zan samu na taimakawa,Nawwar yace lallai Shaye Shaye ya maka illa baka ganewa ka haukace ai wannan tayi gata da hankali kalleta fa chaschas chas da ita,Baso matashi son kowa kin wacce ta rasa da shi Shima yana nunawa da hannu yana magana bana so wallahi,Salma ta fashe da kuka tana cewa Idan baka aureni ba mutuwa zanyi Dan Allah ka cikawa Baba burinsa ka biya Sadaki na,a fusace Baso ya mike ya zare belt dinsa ya fara tafkar Salma,Auta ne ya kwaceta da kyar akan kawai tace ya biya Sadaki ta har da fasa mata gefen Ido tana kuka wiwi,Nawaf a ransa yace ya kamata a taimaki yarinyar nan gaskiya zai iya kasheta watarana gasu su biyu a gida Kuma ba muharramai ba wani abu zai iya faruwa gashi shi Umar din Dan kwaya ya fara haukacewa,Nawaf tashi yayi yace zai tafi Salma ta biyo shi tana kuka tana cewa Dan Allah duk da cewa baka da wasu shekaru kamar Yaya ka sa baki ya aureni,Auta yace karki damu zan taimakeki,ta fara murna ta goge hawayenta kamar ba ita aka gama zanewa ba, tace yau kawata Sumayya sai ta ji labarin nan Umar zai aureni tana tsallen murna,Nawaf yayi dariya suka fito har Baso. Suna fitowa kofar gida Salma taga me siyar da madarar turare da yawa zai wuce da abinsa a Kansa,Salma tace tsaya me turare,ya kawo ya sauke kwandonsa na turare,Salma sai da ta samu Wanda zai wahala a samu a wajensa dama haka takeyi Idan taga me turare wai Dan ta samu na banza,sai ta Kira Wanda babu ma sunan turare haka wai malam kana Umarsal? Sunanta ta hada Dana Baso Umar ita Kuma Salma shine Umarsal,Bai taba jin sunan turare haka ba bashi da shi yace Hajiya Babu,tace a'a dole kana da shi Muji na wajenka,Me turare ya dinga Bude turarukansa tana dangwalawa a hannunta kala yafi talatin tace gaskiya Babu kayi hakuri jeka,shi me turare sana'arsu ce haka dole sai an dangwala kaji irinsa,yace to ya tattara tarkacensa ya tafi,yana tafiya ta murje a hannunta ta shafe hijab dinta da kayan jikinta har wuyanta ta shafe tace Alhmdllh naci banza ina fita za a ce na Faso gari,Auta yana tsaye yana kallon ikon Allah dariya ta bashi da son banza yace ke turare 500 baza ki iya siya ba? Salma tace rufa min asiri ban iya almubazzaranci ba shinkafa bata ishe ni ba ina naga ta kamshi ta wuce tayi tafiyarta ta bar Baso da Auta. Baso yace yawwa ta tafi yanzu kai Dan inane? da Alama ku masu kudi ne Kalli shaddarka Kalli ma fatarka wallahi kayi hankali yan Hisba suna ganinka a Kano sai sun aske maka wannan
Chapter 35 · 0% Book details