← Book details Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 93

Sashe 79

Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Omaira ce ta shigo jiki a sanyaye tana jin kunyarsa ta zauna tayi shuru,yace ni me yasa ba Kya so na? Omaira tace sabo da baka iya soyayya da tarairaya ba ni ai ba aurenka zanyi ka min daba ba,farin ciki da nishadi nake so Kuma na samu me bani Wanda ya iya love,Baso muryarsa ta koma ta Yan kwayar asali yace Allah? tace ae yace to Bude kunnenki kiji dole sai kin so ni kuma ya zama dole ki aure ni ko kina so ko bakya do ko yardarki ko babu,Omaira tace sannu ubana ana soyayya dole ne? Zaki fara a kaina bana cewa Ina son Abu a juya min baya komai na sa a gaba to fa sai naga bayansa,Omaira tace sai muga Wanda zaka sa yayi min auren dole,murmushi yayi yace Zaki gani Omaira ki kwantar da hankalinki Omar Baso ba a ja da shi tun kafin matsala ta afku muke toshe ta mu, Omaira tace oho maka ni dai Mubaraq nake so Kuma shi zan aura inshallah. A fusace Baso ya mike ba Wanda yayiwa Sallama ya wuce abinsa,Omaira tace kaji mutum wlh bazan aure shi ba ta ja tsaki ta juya ta tafi. Tana shigowa nace kin kyauta kinji Dadi akan wani banza wanda ko zance bai zo ba,a pic da videos kawai kika Ganshi bazan iya wannan takaicinba ki shirya ki koma wajen Umma kici gaba da soyayyarki a can wacce bata San ciwon kanta ba. Washe gari Omaira ta tattara kayanta ta tafi gida. Omaira tana komawa Umma ta lullube ta da fada tace ita sam wlh Mubaraq take so aka buga tace Sam,Baso zuwansa wajenta biyu tana wulakanta shi a Kaduna din daga nan yace ya hakura shi baya daukan raini ta auri Wanda take so,Umma ce tace to lallai Mubaraq ya turo duk da bai taba zuwa zance ba daga waya sai video call,zai wahala a kwashe sati guda Omaira bata ga Mubaraq ya Aiko mata da gift ba,kyauta harda ta hauka Kuma komai me tsada,yau ma tana zaune wani ya shigo yaro yace ance Omaira tazo,fitowa tayi taga Yaron Mubaraq da ya Saba aikowa da ledojin shopping suna gaisawa ya Mika mata yace gashi inji Mubaraq yace kiyi hakuri zai yi tafiya ne Dubai, Omaira ta karba tana mamakin irin kyautukkan da take sha,kudi yake kashe mata kamar hauka,ta karba tayi godiya yaron ya juya ya tafi a wajen ta Kira shi tace Mubaraq kyautar nan tayi yawa ko yaushe a aike kake,yace Idan ban Miki ba wa zan yiwa sabo da ke nake Neman fa,tace to na gode Allah ya Saka da alkhairi,yace sai na kiraki ya kashe wayar. Mubaraq ne yace iyayensa zasu zo nan da kwana uku Omaira sai murna takeyi,Umma taje har gidan Abba shawara akan auren Omaira sabo da Abba an saduda gashi Idan Yara suka hada to ba a rabuwa dole sai anyi shawara akan yaran,Abba yace tunda tana so shike nan ayi mata Addua kawai Allah yasa na gari ne. Kwana uku kuwa suka kawo kudin aure dubu dari uku,Omaira tafi kowa murna tace Umma Yace fa ko cokali baza a siya ba ya zuba komai a gidan kar a sa bikin da nisa,Umma ta bude baki tace tashi daga nan marar kunya fitsarriya,sai kace bazawara sai Katsam muka ji an saka biki wai wata Daya tal,Mubaraq yace ya shirya. Baso ko da aka Saka bikin zuwansa biyu again amma Omaira tace ka makara ni fa na fada bana yi. Bayan kwanaki Cele da Ahsan suna Shirin tafiya Saudi bayan bikin Omaira,Auta kuwa soyayyar da suke da rashin kuwa tasa Mami ta Kore su suka tare a hadadden sabon gidansu harda me aikinsu,ba Wanda yake zuwa gidan sabo da rashin kunyar da su Auta suke zubawa shi da Salma. Gaba dayanmu bama murna da auren Omaira amma ita ko a jikinta gyaran jikinta take yi sosai,haka ko Anko muka ce baza muyi ba, Omaira ta dinga kuka Yan Uwa basa sonta ita,Cele tace ba shegen Angon da zanyi aje a sakeki a banza bada ni ba,Bilkisu tace ku kyale yar iska kawayenta suyi mata. Cele yau tare da ita muka fita Mami muka je gaisarwa muka iske Maman Sabreen tazo wai gaida Iyamami sabo da kawai ko papa zai ganta ya maidata dakinta,harda Saka Jambaki tayi wata gira an zana mata kamar budurwa,Cele tana ta dariya a ranta har Maman Sabreen ta tafi Basu hadu da Papa ba,Cele ce ta fito zamu tafi suka hadu da Sabreen,tace Sabreen Dan tsaya Ina da magana,Sabreen ta tsaya sabo da ita Cele tsoro take bata lamarinta ba mutunci,Cele tana karasowa tace ahhh iri na gani Kuma ya mana Idan ba damuwa Dan Allah ki sanar da Mama tayi goshi Kaka na yana ciki irin zubinta zai tafi da imanin kaka tsab zata gyara min Kaka ya dawo da kuruciyarsa,Dan Allah ki tayani Campaign, muna ciki, mu tayi mana ga jambaki yaji ta sha abinta ta zana girarta dodar inda kisan titin Lagos, Sabreen tace ai ba babanki bama kakanki? A'a ke bafa tsoho bane tukuf nice nake ce masa kaka sabo da wani passion kin gane,passion ne yasa nake ce masa kaka bama kaka nake cewa ba Kaks nake fada, kawai Dan Allah ki shigar da file dinmu ki tabbatar tayi signing,Sabreen tace lallai Cele akwaiki da raini wlh uwar tawa tace to uwata ce ai naga dai uwarki ce daga Neman aure taimakonta fa zamuyi ta sha Madara da kaji Idan bata so wlh a zamanin nan baza ta samu ko kamar kaks ba,wajen na karaso tare muka zo da Cele nace uhm please Sabreen Idan Antena kike tunani kaka ma yana da abarsa dai dai misali ba matsala,ga abinci me kyau ta sha Laban taci dajjaja,ga Alburtukal ta sha ta koshi,Sabreen tace baku da aikinyi Mama tafi karfin wani Kakan ku ,Cele tace zata Neme mu da kanta ne sai munyi yanga wlh,Sabreen tace mutanen banza marasa mutunci ta Kara gaba tana dariya wai da Antenarsa tace kut Rabi kwai kwartuwar yarinya. Bikin Omaira Yazo,Lefenta akwati takwas taji kaya masu kyau, ana gobe duk muna can har Mami,su Star duk suna can har Jamcy tana nan Santana sai ranar daurin Aure,mun sha lallai da gyaran gashi,Amarya ta zuba kyau taci gyara sosai,duk maganar da ake Ango wakilai yake turowa kawai bai zo ba har yau,Cele tace Ina jiyewa Omaira karfa taje ta auri wani banza hmmm tayi kuka da kanta,Umma tace mu dai sata a Addua kawai. Washe gari daurin Aure Auta Salma na kugunsa da ita Yazo da abarsa zai koma,Nawwar Yazo papa,Baffa,SantanAhsan dama shi yana Hotel ranar ma Cele a wajensa ta kwana da sassafe tazo gida,a can kofar gidan Abba za a daura ba a unguwar da Umma take ba,Mata suna gida 11am Baso ya iso kamar shine Angon wata arniyar shadda ya Saka da babbar Riga yar das da ita ya dasa Yar hula a gaban goshi,shaddar ita ba sky ba,ita ba silver ba ita Kuma baza ace fara ba kyalli kawai take,Nawwar yace kaga bakano anci hula suka tafa da Baso,Auta Yazo yace babban Yaya,Baso yace a'a shegen gari shegen kaya ya amaryar? Auta yace zam zam,Baso shi kam Auta kamar ba surukinsa ba,yace shegen kaya harda yin kasa da murya iceko kana more ta? Auta yayi dariya yace ba a magana,Baso yace ka kwashi harka Karka yi da wasa Karka daga kafa kullum aiki till down no Mercy no yawaa,suka sheke da dariya,Baso yace taci kayan Dadi a hannuna na riketa sosai ta koshi duk ka kwashe albarkatun nan,Auta yana ta dariya kamar zararre yace ka iya kiwo Baso,Baso yace Tasha Kankana nayi maka maintaining komai fa,Nawwar yana jinsu Yace anyi Yayan banza a Nan,suna nan suka ga an fito a masallaci wai har an daura Auren duk Wanda ma suka shafi Omaira Basu shiga ba,Auta ya mikawa Baso hannu yace tafiya zanyi ni,Nawwar yace mu wai haka ake ba sanarwa ba komai har an daura,Baso yace shirme kenan ai haka wasu suke yi irin na kauye suka yi ai na ciki sun sheda Nima tafiya zanyi,Baso ko wajen Umma bai je ba ya wuce ana ta zuwa Allah Sanya Alkhairi,Mubaraq ya Kira Omaira yace an daura su sun wuce gida,tana ta murna tace amma ka tsaya muyi pics ai,yace sauri yake shi Kam,Su Nawwar duk gida suka wuce,kawayen Amarya sunyi Dj sosai. Su Mami da Salma su da yamma suka wuce da su Star gaba daya sai mun Yan Kaduna da wajen magriba Amarya tayi wanka ta canja cikin wani material na daban ta sha kyau aka kawo motoci sunfi goma muka Kai Amarya gaskiya kowa sai da ya Yaba unguwar da gidan Kansa,gidane madaidaici me kyau sosai duk Wanda yaga gidan sai ya birge shi,furniture kuwa na kirki an zuba an kashe kudi a gidan sosai,dama mu dangi munje mun ga gidan tun kafin biki. Bedroom dinta hadadde ta zauna bayan kowa yaga gida muka mata Sallama tana ta uban kuka daga ita sai kawarta guda Daya Khaleesat,itama kawar dare na karayi ta tafi aka bar Omaira tana hawaye ita kadai, har 11pm sannan taji motsin shigowar Ango ta mike lokacin ta juya baya tana duba turare a jakarta zata sake shafawa ta tsinci muryar Omar Baso irin ta daba dabarsa yace ji mana,Juyowa tayi ta da sauri,Omaira tsoro ya kamata ta fara ja da baya jikinta yana rawa tace Dan Allah ka fita Karka kashe min aure kar mijina Yazo ya ganka please wayyo Allah Dan Allah Karka kashe ni Karka cutar dani sai kuka Baso yayi dariya a hankali yace duba wayarki,da sauri ta dauki wayarta ya kirata da wayarsa taga Mubaraq yace nine to na wayar nine mubaraq ki koma ki tambayi Abba da wa aka daura aure,ki tambayi Auta kiji da Omar Baso aka daura Kuma nine mubaraq nake chat da ke,Omaira tace karya ne tana ihun kuka,tace karya ne muryarku bata yi kama ba. Ku dinga sharhi fa tam AsmaBaffa [8/30, 10:20 PM] AsmaBaffa: 'YAR AIKIN KARUWAI 2 MATAFIYA BOOK 2 101-105 Official AsmaBaffa SADAUKARWA GA ZAINAB USMAN GARKUWAR MATA *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar
Chapter 79 · 0% Book details