← Book details Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 93

Sashe 21

Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Office part dinta ya wuce direct tun daga Shiga yake karewa ko Ina kallo dan gyaran na daban ne,Mami ya samu a bedroom ta tsaya jikin mudubi tana ta kallon kanta tana zancen zuci ita kadai,shiga yayi da Sallama ta juyo da sauri,ya bita da kallo yace amma party Zaki je ko? Party Kuma bana son Iskanci yau ka taba gani Ina saka Riga da skert,Uhmm Nawwar yace ko dai bako zakiyi,ban sani ba karka dameni da tambayar masifa bana son irin wannan Auta ma Nema yake ma ya fiku hankali, Nawwar yayi dariya yace Baffa yace Auta ya fini kema kince Auta ya fimu ai shike nan,Duk yarana babu me sanin yakamata irin Auta Kai ai girman banza ne dakai,Nawwar yace yau Kuma Mami,Allah ya baki hakuri ga Auta nan Indai shine,Kudin da Kika ce na tura Miki tace na gani na gode Allah ya Kara budi yace Ameen ya juya ya fice, Yana shugowa bangarena na buya a bayan kofa na tsorata shi Dariya yayi yace Dan cikinki Zaki tsorata ba ni ba Muka haura sama,nace yau akwai show a gidan nan yau Baffa zaizo inji Auta,Nawwar yace no wonder ai naji a jikina bako Mami zata yi irin wannan kyau haka yau,ba a dade ba Driver ya kawo Baffa sai kace wani Ango ya Sha fararen Kaya harda babbar Riga sababbi gal,tare da Auta aka zo shine dan Kira shine me iso,Palo Suka shiga da sallama Auta yaga gyaran Mami sai dariya yake boyewa ya haura sama yace Mami yazo fa ki fito,Mami harda bata rai Wai aji tace gani nan,Auta ya dawo yace Baffa gata nan,Baffa yace to jeka abinka,Auta ya fice ya dawo part din Nawwar ya barsu. Bayan sati Daya Maheerah ta shirya da dare zata fita Ahsan Yana Main palo Cele ma haka da littafinta tana bitar larabcinta a gabansa idan ta fada da yarensu sai ya gyara Mata yanda ake fada dai dai tana fassarawa da Hausa shima sai ya rike hausar yasan me ake nufi a haka suke karatun,Cele ta kalli Maheerah tace da tsohon Daren nan Zaki fita gidan uban wa zaki je wato kwartanci Zaki tafi kenan to baza ki fita ba,Maheerah ba Jin hausa take ba ta juya zata fita Cele ta riko rigarta tace wlh sai dai ki Kira kwarton gidan nan yazo na ganshi idan da rambon Zan masa bille kaciyarsa to yazo,Maheerah bata sani ba ai kuwa ta koma daki tace da Saurayinta yazo gidan tunda dai mijin Nan nata baya gani ita a bukace take yaga wancen karon yazo ya fita lafiya,wannan karon ma sai yazo a gaban Ahsan Suka wuce ciki,Cele dama labewa tayi a dakinta suna shiga ta fito ta dakko sabuwar reza data gani a dakin, Maheerah ta nemi key din dakin ta rasa haka ta kulle ba key sunyi tsirara a dakin suna Masha'arsu Cele ta Shige ciki,Balaraben nan yayi mugun tsorata,da larabci yace wannan wacece? Maheerah tace wacce aka yiwa dashen ciki ce ta dameni ta hanani sakewa Ina ganin Nan gaba gidan nan Zan bar mata shi Kuma Ahsan baya so a taba ta ko kadan na gaji,Saurayin yace Yana makahon ya Zama miskini Amma ya dinga takuraki,Cele taji ance miskini tace na miskinawa Uwarka zagi,tace yau sai na maka bille a kaciyarka shege me Kan fir'auna ta nufe su Suka tsorata sunga ta zaro reza tace wlh sai na Miki bille a Fuska irin na Nigeria Zaki ci ubanki yau,na taba ganin Yar iska irinki da mijinki sabo da baya gani ki koma kawo kwarto,rayuwa Kamar ta dabbobin dama haka kike yi ku ba kunya ba tsoron Allah,na taba ganin tashin hankali irin wannan wannan wanne irin masifa ce wallahi yau baza ku tafi free ba. BAN YARDA A MAIDA MIN DA NOVEL AUDIO BA BABU IZINI NA,MASU AUDIO KAR KUCI HAKKINA GA MASU SIYAR MIN DA LITTAFINA BAN SANI BA KU SANI KUN CI HARAMUN WLH KO NI KYAUTA NA BAYAR KUNA SIYAR MIN DA NOVEL AsmaBaffa 08061929616 [8/9, 10:59 PM] +234 806 192 9616: 'YAR AIKIN KARUWAI 2 MATAFIYA BOOK 2
Chapter 21 · 0% Book details