← Book details Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 93

Sashe 56

Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta Miko min jaririn na karba tace bashi nono ya sha yunwa yake ji,Miracle na wani jawo bargo na lulluba wai a ciki zata bashi kar a kalle mata Nono,Mami tace a haka ake bawa jaririn nono a kwance cikin bargo baza ki fito ba,na mike zaune na jawo mayafi me kauri na lubbe nononta da jaririn,Mami tace hmm ta juya ta fita,tana fita nace sa key a kofar Baby, Nawwar ya Saka key kuwa ta bude nononta da jaririn. Nawwar ya kalleni nace zafi zafi wlh in yana ja,yace ai baki Saba ba ne shi yasa,Nawwar yana ta kallon dansa yace wannan yaron Allah me Iko yanzu da nine nake sha da yanzu kin zauce ko? nayi dariya nace ae ma Idan Dan uban ne ba ajin komai amma da uban ya sa baki wayyo sai sweet,Nawwar yace hukuncin Allah kenan to na bashi aro ya zanyi,aka juya jariri daya barin nan ma ya sha nace ya koshi kai gashi har yayi bacci. Sai da na gama gyarawa ya bude kofar su Sultana Amare anzo,Jamcy ma a ranar Santana ya kawota,Mandula da Yar zabil duk laulayi suke sunzo suma da mazajensu sunga jariri,Star kuwa Malam ya kawota da dare again ta Kai masa jariri ya masa Addua yace saura namu,Star tace kwana nawa ne wai star da ya wohoho ta karbi jaririn tana masa Addua Karka sake kayo Halin mamanka na fada maka Ameen,nace amma baki da mutunci ni halin tsiya ne da ni? Masifar wai take nufi ayi mata afwa cewar Malam Abhulkair harda fada da kalar tausayi. Wise da Salma sune Yan zaman barka suna makale, washe gari su Omaira suka dira a gidan,Omaira, Raheema da Rahma,Salma ba zaman lafiya ganin Yan mata sunzo suma Kuma kyawawa, gashi Auta nasu ne dama,Auta suke ta nema kawai,ni kuwa Ina satar kallon Salma yanda hankalinta ya tashi,nace Omaira kuje kuyi aiki fa ana baki wa zai dinga abinci duk da akwai masu aiki dole kuyi min,Omaira tace to suka fita,suna fita nace Salma tace Na'am nace ya kamata ki fara gyaran jiki,murmushi tayi tace wa zan wa? Nace in Zaki fara ma ki fara kinga dai ke baki da Uwa a gaban Namiji kika girma, ni Ina da su ba siya zakiyi ba zan baki ana Shan na Infection sabo da tsaro da na niima da sauransu,Salma tace Idan da Zaki zan sha ni bana son magani,tsaki nayi nace Wise ce fa zata hada Miki komai ki dinga zuwa wajenta zata baki munyi zancen,Salma tace to na gode. Kamar muryar Auta taji a kasa da sauri ta fita,nayi dariya nace wannan yarinya ta fada son Auta bata sani ba,fitowa tayi taga shine suke ta labari da su Omaira suna dariya,kishi me tsanani ya kama Salma ta sakko kasa,Auta yana kallonta sai da gabansa ya fadi shi Kam har tsoron Salma yake ta ganshi da mata, Salma cikinsu ta shiga aka ci gaba da hirar da ita tana hararar Auta a boye, tashi tayi ta rike Hannun Auta tace muje,Omaira tace Auta ango gaskiya Amarya kina ji da Autan Mami,Salma tace ba dole ba aje ayi min awon gaba da shi,suka yi dariya su Basu San ma kishi take ba,ta ja Auta cikin bedroom dinsa tace zauna ya zauna tace me zaka ci? Auta shi mamaki ma yake matar da watarana Idan zata bashi abincin ma sai da masifa,yace yau na koshi ya furta Kallonsa tayi da sauri tace me? na koshi yau ya sake fada,Salma tace ai kasan Ina maka girki ko shine kaje ka fita Kaci a waje wa ya sani ma ko wasu Yan matan ka Kai joint to sai Kaci ko cikinka zai fashe Allah ta juya ta fice,Auta ya zaro wayarsa yana dannawa yana murmushi,tana fitowa tace Omaira an kusa bikinki ne? Omaira tace a'a ni dai Ina da Wanda nake so amma ba lallai a barshi ya aureni ba iyayensa sun ce yayi yarinta Kuma fa wallahi ya ma fi Auta shekaru,Salma tace ke karki yarda duk yanda za ayi ki auri Wanda kike so,ke aure akwai dadi ni dake ne wannan zancen sabo da ni kin min a rayuwa jininmu yazo Daya,Omaira tace Nima Ina sonki,Salma tace ke tun wuri kiyi aure kiji dadin da ake ji kema,soyayya akwai dadi ki dafa abinda kike so kici kiyi iko da mulki a gidanku yarinya Malam sai ma dare yayi,Omaira itama yarinya ce bata gane Salma wayo take mata ba wai kar ta so Autanta tayi aurenta kawai,Omaira harda mikawa Salma hannu suka tafa tace ke Allah kice akwai harka? Salma tace ta gaske karki bari kanki ya kulle,tace kin ganni sakata nake na Wala,Omaira tace shegiyar gari ai gashi nan kuwa kin kwace Auta ke kinga irin kallon da yake Miki nace jar Uba kina fama,Salma tace ai missing dina yake shi yasa kwana daya baiji Industry ba,Omaira itama harda washe baki tace ke karki sake a kwace Miki shi ki tarairayi abinki,Salma ana kasa da muryar irin munafuncin nan low down your voice abeg surukata tana nan,Omaira tace tsiyar zama da suruka waje daya kenan,tace Dan ma mun samu ta kirki ai Mami ta waye tsakaninmu da ita sai Addua,kinga bari na Kai masa abinci,Omaira tace iceko kin hada juice? tace tuni ma ai no kidding,Salma yau a abinda ma ta zubawa Auta abincin na daban ne ya sha kyau,Omaira tace gantsare Baby chest ya yo waje baya ma out,kin san kan gari dole muyi kawance,su Rahma ne suka shigo Omaira tace Kai ku fita zancen manyane muke Yara sai shegen son zance ana zance kuna kallon bakin mutane,Raheemah tace dama munyi waya da Umma tace Cele ta dawo a fada muku zata zo ma suna,Omaira tayi murna tace tab ni wallahi tsoronta nake ji tunda ta fasa min Kai fada da ita baya mutuwa tana zuwa na shiga uku,da su Aunty Bilkisu zasu zo ai bata Isa ba,Celen lallai to Cele ba Wanda ta dagawa kafa,Rahma tace Kuma Umma tace tana nan da bala'inta inda kisan bata zaga dakin Allah ba,Omaira tace Ina ga shedan ta jefa ya rama suka yi dariya tace muje wajen Aunty Rabi,tace cab mijinta ya manne da shi ake karbar barka wannan bala'i wallahi zai mata wani cikin da wuri, Mami ma tayi fadan ta gaji,to muje muyi kallon tv. Salma ce ta shiga dakin Auta dauke da abinci sai da ya bi flasks din da kallo ya sha mamaki,ta zuba a plate tace to zan baka a bakin? Auta harda shagwaba nace na koshi fa,itama fuska ta shagwabe ta kwaikwaye shi tace nifa wlh sai ka ci harda shure Shure,Auta bai san sanda ya fashe da dariya ba,Mami ce tayi knocking taji suna ta faman dariya ta juya ma bata shugo ba Kuma basu Bude ba sai driver ta aika ya siyowa Rabi wani nama me Dadi. Auta yace bani dai naci kadan ta dire gwiwoyinta a kasa yana bakin bed tana bashi a baki yana ci,Baso ne ya dinga Kiran Salma ta Kalli wayar my love bata canja suna ba,Auta ya kalla ya sake lekawa cokalin da zata bashi abinci ya bige yayi fatali da shi da abincin gaba daya tayi watsa watsa a dakin ya mike ya fice,Wayar Salma tana ta ringing ta dauki wayar a fusace ta danna wajen kashewa da karfi tana jijjiga wayar kamar zata fasa ta tace Dalla Malam Daina Kirana ta ja tsaki ta jefa wayar a kan gado ta kwantar da kanta a saman bed ta fashe da kuka. Mami suna Palo da baki Auta ya fito fuuuuuu kamar zai tashi sama ya fice,Mami ta kalle shi kawai,da Nawwar suka hadu a hanya ya wuce shi rai a bace,Nawwar hannunsa ya rike ya juyo da sauri,yace Auta lafiya ne wai? Auta kamar zaiyi kuka yace wannan yarinyar ce Yaya can you imagine tana da aurena tana sawa wani my love a wayarta mahaukaciyar Ina ce ita,Nawwar yace Baso ne fa,Bason banza Bason wofi ni wlh inda kasan mutuwata haka na tsani Baso,Nawwar yayi dariya yace Soyayya ta kama Auta fa, Auta in love,Auta yace Allah ya kiyaye na so wannan yarinyar ko zan fara sonta sai na roki Allah ya yaye min wannan wacce irin jarfa ce, Nawwar yace calm down su fa mata ba a musu haka ba da fada ake samun soyayyar mace ba Auta,wannan Kai ka dakkowa kanka tunda kasan tana son wani,wlh tayi kokari ma yarinyar nan ka duba horon da aka mata ko Yan aikin gidan nan basu aiki haka,ta tura gate ta karfi ta zama me gadi,aka bata duk wani aiki na gidan nan,aka canja mata abubuwa da yawa na wahala Idan wata fitsararriyarce zata yi wannan Kuma tasan bata sonka,Amma bata taba Raina wani naka ba ko Abu zata maka sai dai Kai da ita,Ka duba yanda bata gajiya tana girmama iyayenka da duk Wanda ya shafeka wallahi lokacin da na dakko miracle Idan itace baza tayi ba duk da tana girmama mutane amma rashin kunya ma ta Isa a kyaleta,yanzu bata yi kokari ba,sabo da iskanci abinci ma a baki ake sawa ta baka tana da kunya ba a nan ta taso ba haka ta daure take maka har kace sai ana shafa maka gashi ,Sabo da kawai kaga ta sawa Baso My love,Iyaye ma suna sawa yayansu my love,lovely Mum,wayata fa Sweetheart na sawa Mami, Auta yace ai Baso ba muharraminta bane kuma kasan sonshi take ta ya zaka ce hankalina ya kwanta,Ka fara sonta Auta itama naga Alama tama fika kamuwa,mace ce Mai rauni sai anyi hakuri shine auren ai,Yanzu ka koma ko baza ka kulata ba kawai ka koma kayi hakuri,haba Autan Mami duk mun zaci I yanzu ta samu ciki ma,me kakeyi ne wai baza kaji dadin ba,tuntuni ka dame mu aure aure kace ka balaga tuni ko ba haka ka fada mana ni da Baffa ba? Auta yace hakane ai Kuma na balagan ko ban balaga ba Kalli gemuna ya kusa fin naka ma,Nawwar yayi dariya yace to aini banga balagar ba Auta kaje ka bata Service,Auta yace Yaya wlh har tsoron yarinyar nake ji fa,ba dama nayi sukuni,Nawwar ya dinga sheka dariya yace kwailar? Yace ni naga sharrin kwaila wallahi sunfi manyan gyara Namiji, kana gani Yaya ya bigi kirjinsa ni Auta Autan Mami
Chapter 56 · 0% Book details