← Book details Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 93

Sashe 37

Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nake,gashi nasan kowa amma abinda nake gani daban sai na ganni a garin Kaduna,anjima na ganni a Kano jiya ni a cikin dajin falgore na ganni,dazu fa sai na ganni kamar a sambisa Allah Kaka amma yanzu sai naji Ina ganinka na dawo dai dai kaka za ayi burar....Dani,sai Kuma ta tuna Ahsan tace Kaka yau dai jikarka tana son wani a duniya,Kaka yace Allah jikalleta waye me sa'a haka? Ahsan mana yanzu Allah sarki na taho na barshi bai sani ba,Kaka yace Idan ma Bai nemeki ba sai mu koma,ita kuwa Maheerah matarsa Allah yayi mana maganinta ta cuceki jikata,Cele tace ba komai Kaka kaddara ce sannan bakin Abba ya bini yayi min ma da kyau da cikin ya zube,Kaka yace ai ni yanzu farin ciki ya samu jikata ta dawo,Cele tace kaka ka bani labarinka bayan mun rabu,Kaka ya furta Allah ya takaita ni da aka so ayi farfesu na sau biyu ana siyar Dani kaka ya bawa Cele labarin taji tausayinsa tace wallahi kuwa da sun samu nam me auki kanka kadai kaka ya Isa ya cika musu tukun ya,Kaka yace to abu ne kamar fanteka,Kaka yace yanzu akwai kudi ki huta sosai kafin ki fara sana'a,Cele ta zumburi baki tace gaskiya mu koma Nigeria zama a nan baida amfanin face wahala da zubar da mutunci kadan ne suke dacewa gaskiya. Hakane Cele amma saurayin naki fa a Ina zai ganki mu Jira mu gani,tace to Kaka ba sai in yana so na ba,bafa cewa yayi yana so na ba nice kawai nake sonshi kadan,ni ko bai zo ba kawai muci gaba da rayuwar mu a kyale shi,yace to Allah ya zaba na gari,Cele duk ta kumbura bata da jinin kirki. Ahsan bai Farka ba sai washe gari sai da ya gama Shiri fes ya fesa uban wanka ya fito ya zauna a Palo yana jiran Cele shuru,shuru har rana tayi nisa 12pm tashi yayi ya leka dakinta wayam,ya fito ya Bude daya dakunan amma shuru,gidan ya duba ko Ina wayam ba kowa,hankalinsa tashi yayi gaba daya mussamman da ya tuna fa a rude take bata da lafiya ga rashin jini a jikinta ga magungunanta ta barsu,hankalinsa yayi mugun tashi ya fito cikin sauri ya shiga bakar motarsa yana bin layi layi yana dubawa amma Babu alamarta,rasa inda zai sa Kansa yayi gaba daya,parking yayi a gefen hanya ya kifa Kansa a saman sitiyari ji yake kamar yayi hauka,Innalillahi wa Innayhirajun yake furtawa kawai kafin daga bisani hawaye suka fara sintiri a kumayunsa,hankali ya tashi a fili ya furta da larabci bazan iya rayuwar ba sai da ita, directly ya wuce gidan su Maheerah yana zuwa akace Maheerah tana wajen aiki iyayenta sun zaci biko Yazo sai kawai ya Mika musu takardar sakin da ya Dade da rubutawa bayarwa ne baiyi ba sai yau ya mikawa mamanta yace Idan tazo a bata,mamaki ya kamasu suna tambaya ko lafiya yace lafiya lau kawai na saketa bana bukatar sake ganinta a rayuwata na tsaneta,dama makantar karya nayi bayan na kamata da idona. Yana gama fadar haka ya juya ya bar unguwar,gidan abokinsa Husam ya nufa ya nemo shi yana bashi labari suka tafi can garin Makkah ko zasu dace. Cele kuwa akwai kudi a wajen Kaka cewa tayi kawai Kaka mu koma gida Nigeria,Kaka yace a'a an kusa fita aikin hajji ki tsaya Idan muka sauke farali sai mu koma gida lokacin Idan saurayin naki Yazo shike nan,Cele tace ina sonsa amma ni wlh bana son zama a nan Sam ni bazan iya aurenshi ba gaskiya sannan Kaka jikinsa yayi ja da yawa kullum na dinga ganin Jan nama,dariya Kaka yayi yace yanzu akwai kudin da aka bani sadaka muci dadinmu muyi tsaraba ana gama aikin hajji mu gudu kasar mu,Cele tace gobe sai na samu gidan da mata suke na zauna a can ko? Kaka yace kwarai kuwa ai zamana a nan na Saba da mutane da yawa amma yau kwana zamuyi muna hirar haduwa,ai kuwa kwana suka yi suna Hira suyi bacci su Farka Cele tayi shimfida a kasa Kaka yana saman Katifarsa su biyu ne a dakin dama kaka kudin da ya samu daki ya samu shi kadai yana jin dadinsa. Washe gari da yamma Kaka da Cele suka yi wanka suka fito gari Cele murna ta kamata yau gata ga kaka ta rike Hannun Kaka suna tafiya harda cewa Kaka ba'a wakar soyayya a Makkah ne? Kaka yace Ina fa akeyin soyayya kina kusa da dakin Allah sai dai wakar yabon manzo, Kai zan yiwa Kaka masoyina,wajen Taron askarawa suka karaso wajen da motarsu suna tsokanar Kaka da larabci sabo da kaka ba laifi ya iya da yawa sabo da yawonsa,tambaya suke yarsa ce? Yace ae,suka dinga cewa suna son Cele,haka da suka je ma kanti Cele zata siyi kayan sawa kowa yace ga kudi Dan Allah yana so a bashi ita zai aura,harda masu alkawarin Sarkokin gold ganin Yan Nigeria mayun kudi da Gold ne,suna hanyar dawowa wasu askarawan sun fito Kame cikin sirri,Kaka ya gane yace Cele gyara kafarki wancen kame sukeyi wlh,ai kuwa sai gasu sun biyo su Cele suka take a million Cele mamaki irin gudun Kaka yake ya fita gudu ita da take sabon jini ma,da mota suka biyo su Cele suka bi ta lunguna ga kaya Kaka ya rungume Wanda suka siyo,wani me shegen gudun tsiya ya kama abayar Cele tana juyowa ta masa wani shegen Elbow da gwiwar hannu ya saketa ba Shiri ya tsuguna a wajen yana Sosa hancinsa ya sake harzuka yace ba komai ai ana gama aikin hajji za ayi kazamin kame har gida gida bakake zasu shugo sai sun koma kasarsu,yace Cele zata ci ubanta Idan ya kamata ai sai an kaisu sijin inda ake cewa kurkuku Idan suka kama mutum sai an fara kaishi can kafin Nigeria to sai ya sa an gana mata azaba tunda ta masa wannan dukan. Cele gidan su Samira Kaka ya samo mata wajen kwana su uku ne duk daki bai San Yan madigo bane,Cele ta tafi da kayanta gidan wasu manyan mata ne a gidan sunfi shekara ashirin a can suna matukar jin larabci su kansu takari dake gidan basa Hausa sai jefi jefi larabci suke yi,Samira ma zama a ciki yasa nan da nan ta iya larabci sosai, Cele tana zuwa tayi sallama wata Hajiya wacce itace ta samowa Cele wajen kwana ta amsa tace bakuwar alkhairi barka da zuwa ta nuna mata dakinsu da gadonta a gefe, dama sun biya kudin da komai. Matan gidan sai kallonta suke suna lashe baki sai kace mayu,Cele tace wai Meye haka ne kamar karnuka sai wani lashe lashe kuke ba tsofaffi ba ga yaran kalau? Kafin ta rufe baki taga Samira dakinsu Daya,dama tare suka zo kasar,Samira tace Cele wai kece? Kin ganeni wacce muka zo kasar nan tare,na ganeki Kuma ai naga kin koma fara ne kinyi wata kiba,Samira tayi dariya tace uwar sana'a ke Kuma gani nayi kin Kara budewa kin Dan kumbura Kuma gaki fara kin Kara yin wani jakin fari tas anya kuwa Cele kina da jini? Cele tace naje asibiti suka ce jinina yayi kasa sunce na koma a rubuta min maganin na bar Riyad na dawo nan,Samira tace tab ai jini ba abin wasa bane akwai wata likita tana nan takari ce zan rakaki ta rubuta Miki magunguna ba a wasa da rashin jini,Cele tace na gode. Tunda Cele tazo sai dai taji suna ta larabci sun San bata ji amma Basu mata Hausa ko ta gane ko kar ta gane sai dai tayi ta tambaya tana cewa me akace sai a fassara mata a haka take koyo,da Samira suka je wajen likitar ta duba Cele tace sai kace wacce ta haihu, Cele tace ko daya ta boye labarinta ta dai rubuta musu maganin suka je suka siya ta dawo tana Shan abinta. Ahsan ya dira a garin Makkah tare da abokinsa a airport wani driver yaje ya dakko su Dan uwan Ahsan ne babban mutum ne amma shi a Makkah yake zaune, Hotel ya kaisu suka kama dakunan shi da Husam sannan ya kawowa Ahsan mota dalleliya me kyan gaske sabo da zasuyi amfani da mota dole sai da driver Wanda ya fisu sanin garin Makkah, shi yasa aka hada su da wani bakin fata bahaushe ne amma haifaffen garin Makkah ne yana jin both Hausa da larabci,mota suka shiga bayan sun sha Shiri Husam yana gaban mota Ahsan ya kame a baya ya wani harde kafa sanye cikin jallabiya fara Kal me tsadar gaske,takalminsa baki agogonsa baki me tsada sai uban kamshi da sheki yake,gashin ya sha gyara Baso kuwa Salma ya kwalawa Kira ta fito jikinta yana rawa yace kinga bana son hauka ko baki ga gidan nan ba ruwa bane? tace na sani zan ebo ne,uban me kike yi da baza ki cika gida da ruwa ba,ki tafi tun wuri ki Tara ruwa banza shashasha wa ya sani ma ko tsuntoki akayi za a hadani dake ace na aureki,ke Dalla tafi can uban me zan ci dake bana sonki,Salma ta fara hawaye ta tsani ace Baso baya sonta ko da wasa,ba wulakancin da dukan da baya mata amma indai Baso ne ko a jikinta,baza ki wuce ki tafi ba kin tsaya kina kallonsa bakar yar iska ya kai mata wani duka Allah yasa ta fada daki da gudu ai kuwa ya rufa mata baya ya hau jibgarta yana cewa Dan uwarki ni kike yiwa kallon Soyayya? Salma tana ta ihu tana bashi hakuri tace wallahi bazan sake ba kayi hakuri. Mahaukacin da suke taimakawa shine ya shugo dakin da rarrafe yana jan kafar Baso alamar ya bari,Baso juyowa yayi yaga mahaukacin ne dama ya Saba Idan yaga suna fada Yazo ya rike kafar Baso,Baso da maganar Yan daba yace na hakura na hakura Uban gidana ka fada mata kar ta sake yawwa bana sonta ni ya juya ya fice,Mahaukacin ma da rarrafe ya fito ya shiga harkarsa aka bar Salma tana kuka har ta gaji ta fito ta tafi ebo ruwanta tana hawaye ta gaji da aiki amma ya ta iya. Yayan Salma wato Umar Baso kullum sai ya Kira Auta akan Business dinsu,Shi Auta ma karatunsa yake ko bi ta Kansa bai yi sai dai yace zaizo
Chapter 37 · 0% Book details