← Book details Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 93

Sashe 75

Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya Basu su kyautata musu su nemi lahira amma ku itace Abar wulakanta uwarku guda,tayi wanki da guga a kanku,tayi kosai har ta Kare rayuwarta a tasha ta Kare sabo da rayuwarku ta inganta amma ita kadai gidan zama ya gagari uwarku,dakin kwana ya gagareta,ga matarka ga danginta ga uwar matarka a gidanka suna abinda suka ga dama,ku hau motar da kuka ga dama kuje kasar da kuke so uwarku gini ya fado mata sabo da rashin kula gashi nan kafarta za a Yanke mata an fada muku likita ya bada option za a iya kaita Germany ba sai an Yanke ba zata warke amma Kana bani wani dubu ashirin ya watsar min da kudin ya juya ya tafi abinsa,nasan gaskiya ya fada ban iya cewa komai ba. Sai bayan sati daya naje na iske wai makwafcin da matarsa sun siyar da wata kadararsu sun hada kudin sun kaita Germany suna can,Alhaji Kutama shi Nan take ya shiga jirgi ya bisu can ni kuwa gida na koma naci gaba da aikina. Alhaji Kutama yana can aka mata aiki bai dawo ba sai da ta warke ras amma tace da makfacin kar ya sake ya karbi ficikar Alhaji Kutama,Alhaji Kutama ya dinga kuka yana Neman afwarta da kyar tace ta yafe masa ta hakura ba komai,suna dawowa yace zai dauketa ta koma gidansa Kano tace bata so ta gode gwara ko aikatau tayi ta ci da kanta,tace Itakam Alhaji Ashiru da matarsa Fa'iza sune yayanta yanzu gidansu taci gaba da zama,Alhaji Kutama duk sati sai yaje da shatara ta arziki yana ta bata hakuri ko yaushe yana hanya yace ya tuba ya gane gaskiya wallahi matarsa tayi masa nasiha ya gane gaskiya,haka da matar tasa suke zuwa ko yaushe har suka samu ta hakura ta sauke tace zata bisu amma ita Alhaji Ashiru da matarsa sun Fi a wajenta a hakan ma sai da Ashirun ya sa baki sannan ta bisu ta hakura suka koma part dinta daban. Alhaji Kutama yayi dacen mata itace ta maye gurbin bata barin Mama tayi komai jin dadin duniya ta samu,Kuma kayan sawa komai tsadarsa haka za'a siyo da ita ko me ta Saka sai an siyawa Mama na dai dai kudin,Aikin Hajji ma tare suka je itace ta kula da ita,kasa kasa Alhaji Kutama yake samun lokaci su tafi da Mama ta ga duniya,Katsam yace zaiyi aure lokacin da ya ganki kenan Rabi. Mama tace wallahi Bai Isa yayiwa matarsa kishiya ba matukar tana Raye,yaje ya taho da dangin Babanmu aka daura aure ba sanin Mama tace wallahi ba shi ba ita sanda taji labari yana wata kasar ma tunda yaji haka shine ya rubuta takarda ya bayar aka kawo miki,Mama ce ta samu suruka ta gari bata so a mata kishiya a bata ran matar Alhaji Kutama kinji dalili,Alhaji Kutama shi matarsa Allah ya bashi ta gari. Ni kuwa Matata kawai danginta ta sani,bayan Mama ta koma Kano Alhaji Kutama Yazo da Kansa ya dinga min fada ya kawo min babban Malami yayi wa'azi sosai a wajen na dinga kuka na daga waya na Kira Mama tana dagawa da taji nine tace waye? Nace Danki ne Mukhtar Dan Allah kiyi hakuri,tsaki ta ja tace nayi da nasanin haihuwarka Mukhtar da haifar da irinka gwara Babu,irinka dai da na haife shi gwara na zauna bani da yaro ko daya,mahaukaci ya fika amfani a wajena,Hankalina ya tashi muka tafi can Kano Amma bata saurareni ba,a takaice naje yafi sau talatin taki ta yafe min,Matata Kuma ko a jikinta,wataranar asabar na sake tafiya a Kano domin Neman gafararta shine nayi hatsari na haukace na bazama duniya,Babu Wanda ya sake ganina,ni nasan hakkin mama ne ya bini duk da cewa kaddara ko ba komai takan fadawa Dan Adam amma ni nasan hakkin Mama ne,Jama'a muyi kokari mubi iyayen mu mu kyautata musu. Alhaji Kutama yace bayan an neme shi an rasa Mama Kuma tafi kowa damuwa tayi kuka kamar zata mutu ta dinga cewa na yafe masa duniya da lahira,Allah ka yafewa Dana Mukhtar tana kuka kullum tana masa Addua ba dare ba rana har ya warke ya bayyana tafi kowa murna,ni naci gaba da kula da dukiyarsa har ya bayyana. Bayan ya dawo Kuma matarsa bata so taji yayi zancen mama sai dai iyayenta da Yan uwanta so take ya sake juyawa Mama baya shine ya saketa kawai ya karbe yaransa hudu maza biyu mata biyu suna gida ne sabo da Babu amfanin zama da mace irin wannan face ta kaika ga halaka, babbar ribar Namiji a rayuwa yayi dacen mata mata ta gari,kuyi kokari ku dinga nusar da mazajen ku Idan zasu kauce hanya. Labarin ya bamu tausayi matuka haka muna ta tattaunawa Baso ya silale ya ja Nawwar, Nawwar yaje ya Kira Omaira yace tazo Baso ya a Kiranta a palon Mami,taci kwalliya cikin doguwar rigar material golden tasha kyau tayi Sallama ta shigo. Cele kuwa gidan Kaka ta fara Kai,Kaka ya ishi Ahsan da tambaya Yaya Shari mansir? Ahsan yace lafiya,Shari sittin fa ka bi ta can? ya ka baro shi?Ahsan ya sheke da dariya yace lafiya,Yace ya kuwa kantin Yabalash?yace an tashe su,yace Allah sarki,to Darul tauhid hotel fa ana nan ana ta hada hadar dana sani? Ya aka baro dakin Allah? Bakiyya tana can da bayin Allah kwance ciki? Ahsan da ni muna ta yiwa Kaka dariya na rungume kaka nace I miss you Kaka,Ahsan harda rada min Haram,yasan halin Kaka Idan yaji shi sai yaci ubansa sol ba kyale shi yake ba shi yasa sai rada yake min,amma duk da haka Sai da Kaka yace uban me kake rada mata? Ahsan sun dade a can sannan sai gidan Umma,Umma ta dawo daga Unguwa taga motoci harda securities sun tsaya a kofar gidanta,Cele ce ta fara fitowa tace Umma sannu da zuwa muna ta jiranki, Cele ke da waye haka? tace Umma Ahsan fa,Baki ta bude tace har ya Kai haka dama,Ahsan ne ya bude ya fito,Umma ta saki baki tana Shan kallo tace yo aini wannan sai naji tsoron haskensa ke Cele bakya jin tsoro,Cele tayi dariya tace Umma tare ma muke kwana a can ta fada direct,Umma tace to fitsarriya,dariya Cele tayi tace ai gaskiya ce a ranta Kuma tace wayyo Umma Dan baki ga Jan Antena bane ni nake ganin me nake gani,a fili Kuma ta rike Hannun Ahsan tace zo muje Alhaji Ahsan me komai dozin. Su Raheemah sai murna suke suna kus kus akan haduwar Ahsan, Rahma tace za a ga yanga a Makarantar mu Yayar na auren balarabe wallahi na Daina kula su Iklima,Umma tace to me zai ci? Cele tace har tuwo yana ci Auta ya min maganinsa, Ahsan dariya yayi Cele ta mike ta tashi ta kawo masa lemuka da ruwan roba dake Miracle komai available baya yankewa a gidan,Ga Umma tana ta koyar motarta ita da su,Ahsan ya Kalli Umma har da zuwa ya durkusa a gabanta ya dora Kansa a cinyar Umma wai Yazo Neman Albarka,Umma kunya ta kamata tace mu bama haka,Cele ce Kuma ta zuga shi wai yaje a sa masa Albarka tun a mota ta fada masa wai haka suke yi,Umma ta mata tace baza ki fada masa mu muna da kunya bama haka,Cele tace to ai kin zama Ummansa kema,Ahsan dai ko a jikinsa ya dawo ya zauna,Umma sai kunya take ji tace kuje Wajen Abba. Suka tashi suka je can mamaki ya kama Cele ganin ana ta ginawa Abba sabon gida me kyan gaske,Suka yi parking Abba yana wajen ginin ya bude baki ganin Cele ta fito daga shirgegiyar mota ga wasu da securities,Ahsan yana fitowa Abba yace ta tabbata ta tabbata Allahu Akbar ya daga hannu sama yana kabbara yace Allah na tuba Allah na tuba ka yafen nayi butulci gashi tun a duniya Ina gani tun kafin Cele ta karaso gabansa ya fashe da kuka,Cele tana zuwa ta rike Abba tace Abbakati namu lafiya? Wai Abbakati bai San ma yayi dariya ba jin tace masa Abbakati,tace Abbatitiya yane gini naga ana yi waye? Yace Yar Albarka Miracle washe garin ranar da kuka tafi aka kawo kayan aiki,zanen gidan ma sai da na zaba tace ana gamawa zata siya min mota Kuma ta bani jari million biyu,Cele tace taci ubanta baza ta karasa ba duk ta kwashe mana ladan komai sai dai naji tayi wlh bata Isa ba sai dai na karasa maka gidan nan Kuma motar ni zan siya maka na kaiku Makkah da su Umma haka naji har su Bilkisu ta canja musu kayan daki,wai shi Nawwar komai bata yake ne Yar iskar yarinyar nan uban mene a local government dinta Wanda mu Babu sai wadaka take yi,Abba yace ai Rabi har local government ce da ita a gidan ubanwa zata mallaki local government,Cele a ranta tace wlh na gane me yasa Nawwar yake mata komai Yar bariki ce Rabi sun gama sanin kan tsiya,Nima zan dage bari na Saba na samu Ahsan na Maida shi cikakken Sallamammen Sullutu,Cele bata San shi Nawwar dama can yana da saki hannunsa a bude yake wasu banza ma taimaka musu yake bare iyayen Rabi,Su Star duk shine ya musu komai. Abba Bai San mene local government ba,yana ta murna yana ji a Kan farin cikinsa har kokawa ake yi, na gane gaskiya mutum kawai yace Allah ya bashi masu Albarka na gari ko mace ko Namiji,Shiga muka yi ciki Uwa tana zaune tana gyara tabarmarta data ganmu sai murna nace lallai su Uwa an saduda an San darajar Kai,to kin San darajar kanki mana tunda kema macece bazan ce kin San darajar mata ba tunda harda ke kina cikin matan,mace bata son a haifo mata kinji kunya Uwa kin dinga cin arzikin mu kenan,Har da jefar da Rabi to gashi tana muku gini tana saki cikin suturar da ku kuka kasa kuka jefar da ita,Cele ta dafa kirjinta tace Wai Uwa ni Zaki ce Zaki jefar an haife ni sai Kaka aka bawa ni ya rikeni rukon da ko Wanda ya haife ni bazai min ba,Uwa wallahi gori sai in bamu hadu ba,Uwa tayi mukus tace Dan Allah kuyi hakuri ku yafe mana gashi yanzu Rabi har abinci tasa an kawo mana ba abinda bata kawo ba,Cele tace a'a duk dai Rabi muna tare Amma bata
Chapter 75 · 0% Book details