Sashe 53
Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a bani abinci? Zama tayi a gefensa ta bashi a baki yana Dana wayarsa,Salma tace Enjoyment Allah ya biya dai Auta. Yana gama ci tace wanka fa,ya tashi ya shiga toilet,ta fito masa da kayansa na sawa,yana fitowa ta shiga toilet garin wankewa santsin tile ya kwashe ta damfara da kasa ta bige kwankwasonta da jikin sink,kasa tashi tayi,Auta yaji faduwar Abu yace lafiya? Kuka ta saki ya shiga toilet din tana cewa wayyo kuguna ta rike kugu tana cewa bazan iya tashi ba,Auta ya dauketa ya kawota saman bed tana kuka wayyo kuguna,Auta yace Sorry ba tarbiyya,yasa hannunsa a kugunta yana murza mata yace Babu lafiya yanzu haka nan ma duk part of industry ne ko? Hannunsa ta bige yayi dariya yace ki tsaya na iya gyara targade inji karyar Auta. Hannaye yasa a mazaunanta ba inda ta bige ba can tudun mazaunan yace wannan ai mountain ne me zaman kansa,tace tsauni Kuma gaskiya Kai Dan duniya ne dama abinda zaka min kenan haka ake gyara targaden? ta kifa cikinta ta nuna masa daidai kugu ba mazaunai ba tace nan ne fa,Auta yaki tafiya yace ai a faro shi tun daga tushensa harda tofa mata Addua tup tup yana lagudewa yarinya mazaunai,dariya ta fara tace wlh kamar kana min cakulkuli wannan ai ba haka ake yi ba,Auta yace ke Addua ta karye ba a magana Idan ana yi ni sai an dawo farko,ni nawa lakanin haka yake ba a magana kiyi shuru tam,sai da ya lagwigwite mata mazaunai yace yarinya dake sai abubuwa haka tashi saura na tsaye, tace har na tsaye Kuma,yace ke Zaki koya min aikina ko me zan fadawa Baso,Salma tace bazan iya tashi ba da zafi ka daga ni ,Auta ya riketa ta mike tana dingishi,. Jikinsa ya manna a nata sanye cikin boxers yake kacal,ya tallafo mazaunanta,Salma rudewa tayi jin Antena a bayanta ga Auta yana ta gyaran mazaunai,tace ya gyaru haka naji sauki,Auta ya fara fita ma a hayyacinsa da kyar yake magana yace ai ciwon zai waiwayo ki nan gaba a ka'ida sai an yanka kaza nake gyarawa mutane amma sabo da kece ma ake Miki kyauta yanzu sai nayi sadaka da kudina,Salma wani bakin ciki ya kamata tace yanzu haka kake yiwa mutane gyaran targaden har mata? Cele suna zaune a Palo ita da kaka tana duba yanda ake aikin hajji ingantacciya a cikin wayarta suna karantawa tana koyawa kaka,Kaka yace yanzu dawafin bankwana bazan juya na Kalli ka'abah ba kallon karshe Idan zamu tafi? Cele tace babu kyau Idan akaje dawafin ban kwana ba a juyawa a Kalli ka'abah kana gamawa fita zaka yi ba juyowa fahimtun? Kaka yace Na'am. Bayan aikin hajji Yazo su Cele aka dauki niyya suka harami suka fita,su Mairo ma duk sun fita aikin hajji,Ahsan ma yana ciki da shi ake aikin hajji bana sabo da Cele,motar da zasu tafi filin Arfa shi yasa karama aka dauke su Basu sani ba,haka suka yi aikin hajji ingantacciya cikin kwana uku kaka yayi aski Cele ta Yanke gashinta dai dai Gabar karamin yatsa sabanin su masu gashi kawai sharbe shi suke yi yanda suka ga dama,Cele anci sa'a dake aikin hajji ne bata yiwa kowa masifa ba sabo da kar ta bata aikin Hajjin ta har sai da suka gama lafiya sun gama duk wani Shirin dawowa Nigeria Cele ta fara zazzabi sosai,Hammad driver Ahsan yana ta Kira ba a daga ba ga Kaka ya tafi yiwa mutanensa Sallama Idan tafiya ta tashi kawai sai dai su wuce,Hammad jin ba a daga ba sai ya tafi gidan ya buga shuru ba a Bude ba,kofar ya Murda ya shiga ya samu Cele tana kudundune a bargo tana rawar Sanyi,dawowa yayi gida da sauri yace Ahsan na samu Cele bata da lafiya tana ta rawar Sanyi da Alama zazzabi take,Ahsan hankalinsa ya tashi ya dinga yiwa Hammad masifa Kuma sai ka taho ka kyaleta haka Idan ta samu matsala ya ja tsaki ya karbi key ya fita da sauri a mota,yana zuwa direct gidan ya shiga,ya Samu Cele ta sume ma bata hayyacinta,hankalinsa tashe ya sunkuceta sai asibiti,aka bata gado yana ta zirga zirga ya rasa inda zai sa kansa. Komai da sunansa aka cike mata,bata Dade ba ta farfado ta Bude idonta sai ga likita ya shugo bakin fata ne yana jin Hausa sabo da Cele Ahsan ya nemo shi,ya tsaya a kan Cele yace sannu kin tashi jini ne ya Miki karanci a jiki bakya shan magunguna,Cele tace ai na zaci abinci ya Isa jinin yayi yawa,yace ai dole sai kin sha magani,Bai Kai a Kara Miki jini ba amma sai kin sha magani dole,yace Wanda ya kawoki Ahsan dama ya damu yana zaune baida sukuni sai zirga zirga yake ya rasa inda zai sa kansa,Cele tace Ahsan Kuma? Yace ae balarabe ne shine ya kawo ki,yanzu Ahsan ne ya kawo ni? Yace ae bari a turo Miki shi,Doctor ya fito ya samu Ahsan ya rasa inda zai kansa,likitan yace zaka iya shiga ta tashi Dan Allah a kula da ita ta dinga Shan magani,yace Inshallah ya nufo dakin da Cele take a hankali ya turo kofar ya shigo,Cele farin ciki ya cikata amma a zuciyarta,a fili Kuma harara ta watsa masa ta dauke Kai,Murmushinsa me tsada ya sakar mata. Kujera ya samu a gabanta ya zauna tare da dora hannu a wuyanta Hausa taji yayi yace ya jiki,mamaki ya kamata tace la kaji Hausa,yace yanzu ya jikin? tace da sauki naji normal yanzu za a iya sallamata,yace anjima zasu sallame mu,hannu ta Mika masa ya rike suka damke hannaye waje daya,tace Ina bakar kadara? ba komai yake ji a hausar ba yace dai wa? tace Maheerah,tsaki ya ja yace kar ki sake min zancenta,Hammad ne ya shugo Cele ta Bude Ido tace Karka cuceni masoyina Yazo Karka sake naji bakinka kace kana so na a gabansa ni wannan nake so,Ahsan tashi yayi ya koma gefen Cele ya zauna kamar zai hadiyeta,Hammad zaiyi magana Cele tace ahir Dinka taimakon da ka mana ka kyauta mun gode Dan Allah Karka kashe min aure,dariya Hammad yayi,tace Idan kana yiwa Allah ka kama gabanka harda hawayenta,Hammad yace hear me out please ki saurareni. Ya fara bata labarin komai yace ni fa bani nake Miki kyauta ba ni yaron Ahsan ne komai kike gani shi ya turo ni,yace har sadakar da aka taba tareku aka baku shi ya tura balaraben,gidan da kuke,siye awararki,kuje Shopping ace an biya muku duk shine ba ni bane,dama sani yayi sabo da ya sake gwadaki kina da son kudi ko babu Zaki so ni ko a'a,sannan ya auna irin son da kike masa,Cele ta Kalli Ahsan tace to bazan zauna a saudiya ba sai dankwali yaja hula Idan kana so na sai dai ka siya min gida a Nigeria ko muyi 50-50 Idan muka yi wasu months a Nigeria sai mu dawo nan muyi watanni sannan sai da kaka a kusa Dani ayiwa kaka bangarensa,Ahsan murmushi yayi yace yanda kike so,yaushe zaku tafi? tace nan da sati biyu,yace a daura mana aure sai ku tafi zanzo bayan satikai,Cele tace ba matsala da larabci,ana sallamarsu daga asibiti. Aka siya mata magungunan, Ahsan mota ya Bude mata ta shiga ya rufe bayan motar ya shiga shima su biyu a baya,juyowa tayi zata saci kallonsa Shima ya juyo suka hada Ido,Cele tayi fari da Ido,hannu ya Mika mata ta Miko masa hannunta zoben Gold ya zaro a aljihunsa a cikin gidansa ya sa mata a Hannun,Cele tayi masa godiya tana kallon yatsunta Suna zuwa gida suka iske Kaka yayi tagumi baiga Cele ba,ai ganinta da mutane yace Ina kika shiga batan kai kika yi? Cele tace kasan ka fita bani lafiya ta kwashe labarin komai ta fadawa Kaka, tace Wanda na gani nace maka kamar Ahsan ai kuwa shine din,Kaka yace Alhmdllh Masha Allah,ya bawa su Ahsan wajen Zama suka zauna,,ya Kalli Hammad ya masa ambola dakuwa yace ungo nan,Ahsan ya kalle shi Shima kaka ya masa dakuwa yace Kaci ananinka zaka yi wasa da kwakwalwar mu,Kaka yace Cele to ke yanzu kin yarda Zaki aure shi? Cele tace dari bisa dari Kaka,a nan wajen akayi maganar aure da kaka da kudin da za a kashe. Kaka yace to mufa duk sharudanmu sai ka cika har lefe,Ahsan yace ba matsala Idan Yazo kasar Nigeria zai taho da lefen karsu damu. Sai dare su Ahsan suka tafi, Cele tace Kaka na karo wulakanci Yasin,Kaka yace yo ai ba ke kadai ba Nima na karo wulakancin harda rashin mutunci ma, Cele tace dole na gayyaci Yan madugo Yasin suzo suga yanda ake abin arziki. Washe gari da yamma Ahsan ya dauki wanka na kirki Yazo zance,Cele harda kwalliya aka Saka sabuwar Abaya kamar a Nigeria ta fito tana taku dai dai,Ahsan ta hango shi yake driving ya harde a jikin motarsa yana kallonta yana wani murmushi,Cele tana karasowa dama suma ba ruwansu ba wata doka suke bi ba, ya rungume ta a jikinsa Cele tana shakar kamshinsa me Dadi kiss ya mata a goshi yace ta shiga mota suje yawo,to akwai freedom, ya zaga tare da Bude mata mota ta shiga ya rufe ya koma ya shiga Shima suka tafi,suna tafiya suna Hira yana cewa dagewa yayi ya koyi Hausa wajen Hammad,yace Kuma na shiga Makarantar turanci zalla yanzu Shima yana tsinta. Wuraren shakatawa ya Kai Cele,suna nishadinsu ,da zasu dawo Cele tace ya kaita tsohon gidan su na yan lesbian,Bai san me zata yi ba ya kaita ta fita ta shiga gidan da gadara ta kwala Sallama tace Yan Iskan gidan nan ku fito Ina gayyatarku bikina ranar Friday daurin Aure kuje za ayi walima,fitowa sukayi tace da gaske nake ana daurawa washe gari zamu wuce Nigeria,yanzu ma tare muke da shi,sabo da gulma sai da suka dinka lekawa suka ga hamshakin balarabe,Meenal tace na yarda ai kin Kai a so ki nima ba gashi Ina cikin jerin masoyan ba,suka ce sai munzo,Cele tace Idan ma baku zo ba kanku kuka yiwa domin za a bankare raguna za a soke rakumi ato, ta juya ta tafi,ta shiga mota ya mata take away na kayan makulashe ya sauketa a gida. Ranar juma'a kuwa Kaka da Wanda ya sani takari maza suka je masallaci inda Yan uwan Ahsan da abokansa mutum biyu