Sashe 28
Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ita kewa Cele,in banda Jan magana da masifa ba abinda Cele ta iya,sai da ta Isa Shiga makaranta Suka sata a primary tana karatunta tana gama primary Allah yayiwa Attine rasuwa tayi mutuwar farar daya,sabo da na basu Cele halak malak sai nace Kaka yasan yanda zaiyi da yarsa ya riketa Amana tasa ce,yayi murna Kuwa dalilin Cele ya sake auren wata bazawara ita kuma sai tazo tana gallazawa Cele azaba iri iri a wannan dalilin ya saketa ya sake auren wata itama dai ba irin wahalar da Cele bata Sha a hannunta ba dan ma Cele jajirtacciya ce,Watarana su Bilkisu idan zasu je su shigar Mata hanasu nakeyi nace ba ruwansu na rigada na bayar da ita,sabo da Haka ake son kyautar yaro idan ka bada to ka bada shi tsakani da Allah ba ruwanka da shishigi wajen marikinsa,sabo da yanzu abinda wasu keyi sai su baka dansu amma Kuma a sa ma Ido ana bin diddigi Yaya kake rike shi,duk abinda kake Masa ba'a gani sai ace kana zaluntarsa ba dama ka Masa fada idan yayi laifi uwarsa ko danginsa na uwa da uba duk sa Ido suna Munafunce munafunce amma idan danka ne ko kashe shi zaka yi babu me magana Dan riko Kuwa shi Kansa kana Masa amma baya gani tunaninsa Kawai zaluntarsa akeyi aike ko aiki baza ka sa yaro ba sai ace ka takura masa,ko uwar yaron suyi ta munafunci suna zuga yaron sai kaga yaro ya Raina marikansa Yana musu wulakanci iri iri. Nidai nasan dukkan Yan uwan Cele suna makaranta amma Kaka Malam Jibrin bashi da kudi da kyar ma suke ci su Sha Watarana ma Ina aika musu da abinci dama Attine ce me Neman kudin shi nasa sana'ar bata kirki bace Kuma ya tsufa,baya so a takurawa Cele shi yasa ma ya saki matar tasa bai Kuma kara aure ba daga shi sai Cele har ta Zama budurwa,batayi secondary ba ni Kuma banyi shishigi ba nayi Kara Kar Kaka yace na nuna ya gaza, duk yarana babu me zafin Nema irin Cele babu kuma me jaraba da masifarta,tun tana karama take Sana'a iri iri Kaka Yana bata jari har ta Fara kosan siyarwa safe da yamma,da rana Kuma tayi fanke da miya,dama Kuma tun tana Karama tasan mune iyayenta tasan Yan uwanta ba a boye mata ba labarin komai ta sani,ganin Yan uwanta suna zuwa makaranta sai tazo duk da Abba baya kulata Kamar ba shi ya haife ta ba haka Uwa ma,haka Cele take zuwa tace dan Allah a sata a makarantar boko amma sai dai ma ya daddaketa ya koreta Yana zaginta,Uwa ma haka tun tana hakuri har ta daina kyale su,in tazo gaishe ni ma Sai ya koreta yace ke tafi gidanku Yana kyararta,Uwa ma Haka take hantararta,inyi ta kuka ita kuwa Cele Allah ya bata jarumta bata damuwa,Watarana tazo gaisheni da yamma ta iske Abba a waje ya tareta yace ke gidan ubanwa Zaki shiga tace gidan Ubana,yace to baza ki shiga ba tace sai na shiga ko Kai baka Isa ba,baki ya rike yace ni din ? tace Kai waye ai ba ubana bane kai Allah ya kiyaye ace Kaine ka haifeni,yace to uwarki cikin Shege tayi ta sameki,tace ae ai gwara Yar shege ta tafi zata shiga gidan ya rukota Cele tace ita kuma sai ta shiga ya Kama yarsa da kokawa Suka dinga kokawa da Cele Kamar sa'arsa sai da ta shiga gidan Uwa ta samu a Hanya ta dauketa ta kaita cikin toilet ta jefata a ciki ta fito abinta. A haka Cele ta Raina su kullum tazo fadansu baya karewa ita Kuma baza ta kyale su ba data sake girma ma idan tazo duk inda taga Uwa to idan Uwa bata gudu ba sai ta dauketa tayi waje da ita ta ajiyeta a wajen ta kulle kofar gidan sai Sanda ta Gama abinda takeyi zata fita sannan Uwa ta shigo,wanka Cele bata Isa tayi a gidan ba sai sun ci Mata mutunci shi yasa itama bata daga musu kafa gashi bata taso tare da su ba Babu wannan shakuwar kuma ma su ba Wanda suka kyale a yaran sabo da Mata ne su, Ni Kuma tunda Suka girma sune farin cikina su suke min komai haka Cele Yar Albarka Sana'ar nan tata kusan kullum sai ta kawo min kudin kashewa,sabulun wanka sabulun wanki omo duk suna tafe zata kawo,Yan uwanta ma Slifas ma tana siya musu har Uniform ta Sha dinka musu na school da kudin sana'arta ta min dinki bazai irgu ba,da tazo taga ba abinci a gidan zata Aiko min da su taliya Yar macaroni ko ba yawa Yar shinkafa kwano daya biyu haka,har su Bilkisu kafin su gama secondary sai data biya musu Rabin kudin waec da kudin da take sawa a asusu sauran Kuma na cika tunda Ina sana'ar Alala da kunu nima. Ko ni Cele ban Isa da ita ba Matukar akan su Abba ne,Uwa dai itace ta sa Muazu ya sake sakina,Yana sakina Cele ta shigar da Kara Kotu akan Uwa tace sai na bar gidan,Muka je kotu aka zube zance Alkali yayi Nasiha ya jawowa Uwa da danta Aya da hadisi ya fada musu Allah sannan yazo ya musu fata fata yace ba inda zanje,Cele tace to azo a nunawa uwar mu wajen zamanta,Alkali yazo da shedu ya ware min dakina biyu da Palo da bedroom Dole Su Uwa badan sun so ba nake zaune a gidan,Cele ita ko da yan uwanta basa Zama lafiya Sabo da idan tayiwa Abba rashin kunya Su kan Mata fada sai ta hada dasu karshe ma ta tsani kowa tace duk bamu da hankali bamu san me muke ba bamu San yancin mu ba,ta daina zuwa gaishe ni amma duk da Haka tana aiko min kudin da sauran abubuwa,aka zo bikin Bilkisu Cele kayan kitchen da yawa ita tayi su ashe tunda aka sa bikin take tari ta sake dagewa da Sana'a badan cele ba da munji kunya a bikin Bilkisu Kuma ko bikin bata zo ba ,Bilkisu ta auri mijinta Yaseeer,har gida naje wajenta taki kulani sai da Kaka ya sa baki sannan ta kulani,Dariya Muka Yi har su Nawwar, Bayan shekara itama Nazifa da Nazira Suka samu Miji amma duk har na Bilkisu basu da karfi talakawa ne,Nazifa mijinta Usman,Nazira kuma Ishaq, suma dai sai rufin asirin Allah amma suna zaune lafiya. Cele da tace zata tafi Saudiyya Neman kudi babu yanda banyi da ita ba tace sai taje ai da bama sonta bayar da ita muka Yi kyauta sabo da ba a kaunarta sabo da Haka ita ta gaji da takaici tafiyarsu zasuyi ita da Kaka,Shima Kaka biye mata yake idan tana neman kudi to girki ma shi yake musu ta hanashi Neman kudi tace ita zata dinga yi shi Kawai ya dinga girki Kaka ya Zama shine macen ita Cele itace Namijin,amma ke Rabi Uwa itace ta jefar da ke koma Ina ta kaiki ta fimu sani. Nawwar ne yace a kirata,Omaira ta fita ta Kira Uwa da Abba suna tattabe baki Suka shugo, badan Nawwar ba ma baza su shugo ba,waje aka basu Suka zauna Nawwar yace Uwa dan Allah Sanda Kika dauke Yar uwar Cele Rufaida Ina Kika kaita,Uwa tace na manta memory na kwakwalwata ya goge lokacin bana iya tunawa kasan tsufa,Ni miracle Nace karki Raina mana hankali ki fada mana bamu da lokacin saurarar zancenki,Abba ya min tsawa yace ki kula ba a taba min Uwa,Uwa ta fashe da kuka tace kowa sai ya zageni tana matse hawaye,Miracle tace wannan kukan fa sai kace kinyi Zina ance za a jefe ki kinga wallahi Wallahi tun wuri ki Fadi gaskiya kafin na ebo Miki gayya guda su tara Miki gajiya ni kadai ma na isheki kafin nazo Miki da gayyata wallahi ba abin kunya bane in Miki zigidir, Uwa tace ni din? Ke dinfa kin San gwagwarmaryar dana Yi Kuwa,to bazan fada ba ki sa kaina gabas ki yanka ni dan ubanki,badai ubana ba,sai dai Nawa? Naki cewar Rabi,Uwa ta fashe da kuka,nace tabara idan ban ruguje Miki Baki ba shegiya nake kaji mata,Abba yaga Nawwar me kudi yayi mukus,Nawwar ne yayi magana yace Kinga dan Allah ki fada mana wannan kiyayayar ta Isa haka,shegu kudi me kudi ya sa baki Uwa tace dan Ina ganin mutuncinka ne Kawai a can kauyen Ungoggo naje na ajiyeta a jikin wani masallaci na dawo gida ta fadi sunan garin su Dagaci. Na kalleta nace Amma ban taba ganin marar Imani irinki ba Kuma wallahi sai Allah ya saka mana,ko a gidanku ana iya kera ko hanci ne bare mutum sabo da Kawai Allah yayo mu Mata,ke mecece ai sai ki canja kanki ki koma namiji,ki kerawa kanki Antenar maza kawai ki saka ki koma namiji,ke me yasa kika zo a mace? Da nasan haka kuke da wallahi da zuga guda zanzo muku su tara Miki gajiya,Ni dama ban sanku ba ke da Wanda Zan wuce a kwararo duk daya bare na daga Miki kafa,Ina ma na sanku da wuri Kuna yiwa Umma haka sai na kawo wani ya dirka Miki ciki,Uwa ta bude baki tace ku kashe ni ku huta,Nace Inshaallah bakin cikinmu sai ya kashe ki azzaluma,Kai Abba baka Yi dacen uwa ba wallahi bata kaunarka sam tunda bata son jininka,Jahila ce Kawai kaima ka biye mata,mu da Allah ya Mana baiwa masu tausayi da Jin kai,ka raine mu ka bamu tarbiyya karshe mu Zama sanadin shigarka Aljana duk abinda Allah ya lissafa akan niimar mace baka ji Ina almajirantar taka take ko ba karatun kayi bane aikin gadi kayi a gidan Hajiya,dama wasu almajiran kaga sun Dade shekara da shekaru ko izu biyar Basu haddace ba sai yawon bara da iya shege kala kala,ni na taba Jin ma irinku sai kace Wanda aka haifo ku ana dura ashar babu Bismillah,Uwa na nuna da hannu nace duk yanda akayi lokacin da za samu cikinki Oven din da za a shiga shedan ne ya Fara shiga sannan baban Suka dinga gwamutse da Shedan Yana Jin dadi shedan ma na ji ta ta Zaki Yi Imani. Umma ce ta bige min baki tace Kinga bamu labarin naki bana son fitsara,Zama nayi na dinga Basu labarina kaf komai da komai ban boye musu komai ba,Umma