Sashe 18
Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
hakane a bari to ta Kara kwana ukun zai fi Bangaren Mami kuma Jin Baffa bai zo ba shuru Shuru sai hankalinta ya sake tashi a Haka ma tana kokarin dannewa sabo da kunyar yaranta. Auta ne ya shigo bayan Sallar Isha da Sallama anci wanka cikin kana nan Kaya hannunsa Daya a cikin Aljihu Daya Kuma da ledarsa,Mami tana Palo a zahiri kallo take Amma a zuciyarta ta fada tunani,Auta ta gani tace Nawaf daga ina haka? ya gaida Mami ta amsa ya ajiye Mata ledar yace Mami gashi siyo Miki nayi,Mami tana dariya ta bude ledar ta duba sai taga tsire lafiyayye yaji hadi da fruits salat da wasu snacks,Mami tace Autana na gode Allah ya maka Albarka a Ina ka samu kudin? Ni shike nan ban Isa nayi abu ba sai ace Ina na samu kudi to Baffa ne ya bani,Ni yanzu sai abinda nake so a wajen Baffa yace zai siya min mota kwana nan,Mami tace to na gode Auta a wajen ta bude tsirenta tana ci Mami akwai son tsire,tace ka je wajen Nawwar yace yanzu zanje ,jeka ka dawo muyi hira yace to ya mike ya fice, motar da kankabarsa ke sawa ya dakko ta ita ya koma ya Bude ya dakko wata ledar ta su Nawwar ma tafi girma Wai su ba mutum daya ne zai ci ba,Muna Palo Nawwar yayi matashi da cinyata Muna kallo Muna hirar mu Auta ya dinga Danna door bell sai da Nawwar ya kule yace wai waye ya shigo Mana,Auta ne ya shigo yace wlh nasan sai kai,yace to gidanku na ango da Amarya ai ba tsari na fado muku ciki Baku shirya ba ko,Uhm munji sarkin iya zance cewar Nawwar,Nawaf Zama yayi ya kalli Nawwar yaki tashi Yana kwance yayi matashi da cinyata,kasa kasa yace da wani ne da yanzu an dame shi ance bashi da kunya, Aunty Ina yini? Nace lafiya kalau Auta ya gajiya ya labarin aurenka ne,Auta yace hmm ya Mika min Leda tare da cewa gashi Aunty,Nawwar yace ya fasa Auren ai,inji wa? Auta ya tambaya da sauri yace aure Yana nan ba gudu ba ja da baya,Nawwar yace yaro rikon aure da wuya kawo kawo ma ta isheka me aiki babba ma yaya ya Kare bare Kai,yace karayayye ba shine ke tsoro ai Allah ne yake ciyarwa ba dabara da wayon mutum ba,Kai nufinka kudinka ne yasa kake ci da Aunty kana bushasha, Nawwar yayi dariya yace a'a kudinka ne Auta, yace Allah ne dai da badan Allah yaga dama ba sai ya baka kudin Kuma ya hanaka ka bawa iyalinka Aunty da yanzu kyawun Nan ya fece ta dagargaje ta lalace da idan ance ma ka kwanta a cinyarta baza ka je ba,amma yanzu Allah ya baka ikon kula da ita shine zaka ce ni bazan iya ba to Allah ne zai bani nima,Nawwar yace 1-0 Auta Ina ta dariya na dauki ledar nace Auta mun gode,yace kullum ke ba a Maganar kirki dake sai yawu sai kace maye yaga wani ransa ya biya,nace Nifa bana son wulakanci Auta Kai ba a abin kirki da kai sau daya fa kazo kaga yawun nan shike nan ka sani gaba,Nawwar tashi yayi ya bude tsiren Auta Muka durfafi tsire da ci,yace Yaya yau anci madari,Nawwar yace Allah naso na kalli wasan nan,yace Wasa yayi baka ga yanda aka wulakanta Madrid ba yau,modric duk kyansa yau jahilci yayi, suna ta hirar ball har Auta ya tashi yace wajen Mami zai je,Nawwar yace to mun gode Auta yau anyi abin kai,Naga alama ko na mutu Auta zai rike matata,Auta yace in aureta kuwa wlh ba ruwana mantawa zamuyi da Kai tsaf,Nawwar Yana dariya yace to bazan mutu yanzu Dan Iska Ina nan sai na tsufa tukuf ni da ita,Nace Inshaallah aniyarka ta bika Auta,yace Ameen tunda aniyata me kyau ce ni bana gudu ta bini, yau a bangaren Mami ya kwana dakinsa daban bai koma gida ba Suka Sha hirarsu. Iyamami ce taje Kauye ta samo yarinya bazawara sakin Wawa a danginsu ta kawota har gidan bangarenta tace ta samowa Papa matar aure lallai sai ya aure ta,Papa yace wallahi bazai Aura ba Iyamami ta dage sai Papa ya Kara aure ga Sabreen ta samu Iklima sun hade kai sai sun kori Wise,sun hana Wise sakat a gidan nan tun bata damuwa har ta fara damuwa a ranta,Seraline ta Kira tace tazo Dan Allah sabo da Indai Shawara ce sai Seraline Allah ya bata fasahar yin abu cikin hankali idan Kuwa Star ce cewa zatayi Kawai aci ubansu a musu dukan tsiya,Nima Haka zance,Yar Zabil ma bare Mandula mijinta ne Kawai ya Isa da ita shima darajar so ne tana mugun sonsa shi yasa sai yanda yayi da ita,Seraline ce ta Kira Sabeer ya tafi Katsina wajen Yan Uwansa baya gari tace Baby dan Allah yau zanje gidan Wise,yace ban son yawo kin sani kullum fa sai Kun hadu a makaranta,da shagwaba tace kirana tayi fa matsala ce shi yasa yace to shike nan kije da motata karki kai dare tace to,da Yamma ta shirya taje,bayan sun dan taba hira Wise ta bawa Sera labarin komai,Seraline tace ki kyale su tunda uwarsa tana ciki kin San uwa tana da power zata iya yanke hukunci ko shi Mijin naki sai ya Mata biyayya ke me ya dameki suyi ta Yi miji shi Zaki rike duk abinda zasuyi a banza yaran dai idan Suka Miki kici ubansu wannan Sabreen din naga Alama bata daku bane,Wise tace zanyi bariki a gidan nan,Seraline tace a'a karki Yi please dariya Suka Yi tace kinga Iyamami da ace ba uwarsa bace da yanzu na canja Mata kamanni Mata da budurwar zuciya kullum zo kiga kwalliya ta wani saka jambaki harfa kitso ake Mata da Attach wallahi Rannan cewa tayi sai an sa Mata Attach,Seraline ta dinga dariya tace na gani ai,tace ni ai da dangin Sabeer sun Fara min wulakanci ya taka musu birki da Kansa ya kwatar min yanci shike nan ai Yana Jin harka a local government yaci ubansu kaf. Wise da Sera suna Hira Suka ji hayaniya lekowa Suka yi Suka ga Auta da Iklima bakuwa matar da za a aurawa Papa suna kokawa, Namiji da mace karfi ba daya ba sai gashi Auta ya fasa Mata Hanci da baki jini Yana fita,Fitowa sukayi da Sera suna tafawa Auta wise tace Auta another punch Auta Kamar dan China haka yayiwa Iklima budu budu tana ta ihun agaji,Iyamami ce ta fito da gudu tana zagin Auta tace ubanka ta maka yanzu zaka Yi kisan Kai Dan iskan yaro marar tarbiyya dama uwarku bata muku tarbiyya ba,Auta yace ai ke shi yasa naga tarbiyar ce dake ke naki Iyayen tarbiyyar Suka Miki ai da sun Miki tarbiyya da baki abinda kike ba Kuma wallahi ta sake cewa zata aikeni sai na karyata baras,au au yanzu dama akan Kawai tace zata aikeka shine ka Mata wannan dukan,yace ae ni sa'anta ne ko kece bazan je ba bare wata kucaka kazama,ta kirani wai Kai yaron nan nine yaronta ko kanin ubanta ne ni,ko Papa kanin Ubana baya min wannan Kiran sai ita sabo da kin kawota Zaki cusawa Papa ya aureta baya so ta tafi gidan ubanta wallahi baza a sata a gidan nan ba ai ba gidanki bane kema Iyamami,Dan ubanka ko ubanka bai Isa dani ba bare kai,ai Ubana Yana tsoronki aljanarsa tana kafarki ni tawa a kafarki take? a kafar uwata take bazan biki ba idan Kinga dam ki tsine min ma,ai Kuwa idan na tsine maka sai ta kamaka yanda na Sha wahalar rainonka da goyaka a bayana ga shegen kukan tsiya haka nake goyaka kayi min fitsari da kashi duk na wanke maka,Auta yace Iklima take ko wa bata da waje a gidan nan baza a aureta ba, Iyamami tace to na gani idan ka Isa sai mu gani mace daya tayiwa Dana kadan wannan Karuwar ce zata bar gidan nan bana kaunarta. Auta ya nuna Wise yace wannan da kike gani hadin Allah kenan mace Daya tamkar da dubu ai akan ki aurawa Papa Mata goma to gwara ki bashi Wise guda daya,baki ji sunan bane Wise ta ko Ina Wise ce duk ta cike gurbinsu su goman ,kainuwa dashen Allah ita da Papa sai Allah, yau naga dan iskan yaro haka ka koma cewar Iyamami, Auta yace Kuma sai ta haifo mana yara Papa ya samu yaran kirki masu Jin Kansa ba irin Sabreen ba ciwon Kai hawan jini da Kansa to Sabreen kenan, Auta ya kalli Wise yace kina haihuwa na zama Dan raino, ki share su Iyamami ba Arabic ba boko baza su gane ba ko Papa ya sakeki Ina nan zanyi ciki dake ni a haka ma Ina so,Iyamami salati ta saki tace au kwarto ka koma Kuma to wannan sai an sa Ido a kanka tunda ka Fadi haka zaka iya zagawa dama kaga Karuwa ce shike nan kwartonki a gida, Auta yace ke ma da kinyi wa ya san irin zalamar da Kika Yi a zamaninki, ki dai gyara tsufanki ko Kya samu ki cika da Imani yanzu mutuwa ma Yara dauke su take ba sallama bare ke da kin tafi gangara idan baki tuba ba sai yaushe, kin girma kisan kin girma,ki sani gadararki ke Kika haifi yara to suna da hakki a kanki wallahi sai Allah ya tambayeki tunda Amana ya baki,Dan Adam guda aka zabeki aka baki su gasu nan har Mata da maza aka hada Miki matan sun gujeki sai sunga dama suke zuwa daga su sai yaransu sabo da duk kinbi kin watsa Kan yaranki da kanki Aunty Rukayya da Aunty Binta ko gaisheki basa zuwa sai suyi shekaru sai da dalili suke zuwa Babu zumunci Sam yaransu basu sanmu sosai ba muma Haka to a haka kike so idan kin mutu muyi zumunci zuriarki su hada Kai a haka,yanzu Maman Sabreen duk kin jawo yanzu anyi baran baran,komai kin lalata Baffa ma da Papa badan Allah yasa ba da yanzu sun farrake to a haka ke son yaranki kike Yi? Ai ke ce ma makiyiyarsu,kina ta shiga hakkinsu kin hanasu zaman lafiya da matansu,takala na bala'i me kudi nayi mene amfaninsa sabo da koshi ya Miki yawa Zaki ci abinda kike so Allah