← Book details Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 93

Sashe 29

Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tace wannan barikin da Kika je bakin babanku ne gashi nan bazan ce komai ba wlh shi yace Yan bariki na Haifa a haihuwarki da Cele,ya kalli Cele tana jaririya yace sai tayi cikin Shege a gabana Kuma Allah ya taimakeni yaga zuciyata da zuciyarku Babu Wanda ya lalace Cele tafi kowa taka tsantsan da kame kanta nasan duk inda taje ba abinda zai same ta akwai kamewa. Uwa da Abba ne Suka tashi suna bata rai suna tsaki Suka fice suna cewa ayi mu gani ko a jikinsu Babu alamun nadama,Kallon Umma nayi da Yan Uwana nace ya Naga bakuyi min kuka bane Kun gama Jin labarina a banza ai ya kamata kuzo ku rungumeni kowa ta fashe da kuka Yan Uwa sun hadu Yar uwarku ta dawo amma kunyi kiyau miyau har Umma ma Ni baza ayi kukan ganina ba,Dariya sukayi Suka ce tab ai mu a jajirce muke ba komai ke bamu kuka ba,Kawai Dan mun ganki sai mu Fara kuka sabo da me,Nawwar ya kalli Auta shi tuwonsa yake ci ma Yana Shan lemo ba abinda ya dame shi,yace Kai sai ci ka iya ana ta labari kana nan,yace to labarin dogo yunwa nake ji,Aunty Bilki tace a'a kyale shi, Auta yace Yaya ka bar Aunty tayi ko kwana biyar ne,Nawwar yace to in tana so ta zauna,nace dama ka gaji dani daga tambaya sai kace to ai shike nan wlh zaka ga tsiya,Auta yayi dariya yace to ke ba a iya miki shike nan ki taho mu tafi tunda bakya son Umman taki, Nawwar yace zamu Zo dasu Mami sai mu koma tare ai,Auta yace Zan zauna Nima,Nawwar yace a Ina zaka kwana to yace a dakin su Omaira su bani gadon su koma kasa su sai su kwanta ni ba ruwana da mace yaro ne ni haka kuka ce,Omaira tace Allah ya kiyaye,Auta yace haba kawata harda ke,tace sai dai a kaika shagon Sagiru gashi nan makwafcinmu,yace ae a kaini Zan zauna akwai toilet hadaddiya bana son kazanta ni a unguwa sabo da toilet ba ko Ina nake kwana ba,Raheemah tace gidan su Sagiru me kyau ne ko Ina tiles dakinsa ma me kyau da toilet dinsa,ai kune kuka ce shago sai kuce dakin Sagiru,Rahma tace kuma Yana da tsafta Kamar mace,Auta yace ku fadawa Sagiru abokinsa ya zo, dariya Suka kwashe da ita,Nawwar yace Wai a Nan zaka kwana karya kake yanda Muka zo Haka zamu koma idan zamu Zo da su Mami ka dawo,Umma tace ka kyale shi Mana tunda Yana so,Nawwar yasan Auta Yan matan da ya gani ne ya makale sai ya zauna shima ba yanda ya iya da shi haka Suka Kira Afif zai maida Nawwar Airport, Nawwar ya bawa Umma dubu dari,dubu dari ya bawa su Bilkisu yace su raba ba yawa kafin nan gaba suna ta godiya,a gabansu na rike Masa hannu Muka fito tsakar gida zai bawa Uwa nace wlh kana bata munyi fada kasan da ya kamata Zan sa ka bata da ita da Abba ko kwabo sai uwata ta jika tukun muje na tura shi ta baya nace muje muje,dariya yayi yace Umma fa tana kallonki zasu ce bamu da kunya,nace muje ni dai,Uwa taga samu taga Rashi a gabanta na Hana a bata ko sisi wani Takaici ya sake kamata,Muka fito yace Abba fa nace Ina bazai ci kudina ba ai cewa Suka Yi basa son Mata,shiga mota please na bude Masa gaban mota ya shiga yace sai munyi waya,nace Bye yace I will miss you,me too My love su Bikisu suna Masa Allah kiyaye Auta yazo yace Yaya banzo da kudi ba ka bani kudi,yace bazan bayar ba,Yaya nifa na gano maka Dangin matarka shine kake min Haka,Zan maka transfer yace ni cash zaka bani, yace Auta baka ji wlh ya zaro kudi ya bashi yace Yaya Dubu ashirin kacal da me zanyi chilling a garin nan Ina fa da abokai,Nawwar yace muje Afif,Suka tafi aka bar Auta a wajen ya Kira Baffa ya tura Masa kudi ta account Kuma ya tura Masa,yasan Mami baza ta bashi ba ma. Ciki Muka koma da Auta nace Kai da kake da abokai ma Kar dai su dauke Mana Kai,yace ai Ni yanazi nan nazo ba wajensu ba zadai su zo muje yawo ya kalli Raheemah yace kece kadai karama a gidan Nan ba tsayi ba kiba sai kace kece Cele da baki Sha nono na sati biyu bama ga Cele a hoto ma katuwa ita da Bata Sha nono bama ke kin Sha na shekara biyu amma sai kace me cutar yunwa gaskiya kiyi tsayi da Yar kiba haba,Raheema tayi dariya tace Rahma ce ta min kwari ance itace ta kwace girman,yace to ke Rahma ki dawo Mata da nata ku raba biyu,Umma tayi dariya tace Kuma ita aka fara haifa,Na jawo tuwon gaban Auta nace ku bani Mai da yaji,Umma tace ki bari a Miki wani abin mana Raheemah dafa mata wani abin,Nace ayi min danwake,Umma tace to ai Kuwa Babu kayan yi zo ki karbi kudi ki siyo nace a'a akwai kudi na zuge jaka aka bawa Omaira ta taje ta siyo,Muna ta hira Ina Basu labarin kawayena su Star da gidan su Nawwar a hankali Ina ta karasa musu labarina,sai magriba Muka Yi Sallah Auta tuni ya fice yawo da abokai sun dauke shi a mota. Sai Bayan Sallar Isha masu auren Suka tafi gidajensu sabo da Bilkisu yaranta biyu duka maza,Nazifa mace,Nazira ma namiji,Sai wurin 9pm Muna hira Auta ya shigo yayi sallama nace Auta Dadi aka siyo min naga leda,yace Yaya ne yace fa a siyo Miki kaya baki zo da Kaya ba ya Mika min naga dogayen riguna guda Uku masu kyau nace dama gobe nake cewa Zan siyo ko kala biyu ne kayan Omaira sun min kadan na Umma sun min yawa,dama Zanin Umma na daura da t-shirt,nace shi ya fada ma size din? Yace ae ya Mika min Daya ledar ta take away na kaji da Yogourt da lemo yace na Umma ne na siya mata ba naki bane karki Fara murna,Umma tace an gode dan Albarka,Omaira ce ta raka Auta gidan su Sagiru dama sun gayawa Sagiru,Suna Hanya Auta Yana bayanta Yana Kare Mata kallo. Cele Fitowa tayi ta a fusace tana hawaye cike da bacin rai ta nuna Maheerah da Yatsa tace Ittaqillah dan kutmar....ta tafi Kamar walkiya Maheerah ta zaci wajenta ta nufo tace bari na Fara cin uban Uwarki me warin tafarnuwwa tukun tayi wani mugun tafiya da Babar Maheera Kamar guguwa ta hada kanta da bango,ji kake kummm ta shaketa ta dinga jijigata ta jefar da ita a kasa,Maheera zata gudu tayi kanta Ahsan ya riko Cele ta juyo ta Kai Masa duka ya saketa ba shiri ta damko Maheerah ta gwarata da bango nan take ta Fadi ta sume sabo da kanta ya bugu Kuma cele bata hakura ba ta haye ruwan cikin ta tana dukanta baban Maheerah yazo zai masge Cele Ahsan ya rike hannunsa da sauri cikin larabci yace karka sake ka taba ta dashen ciki tayi mata ba izininta kuma budurwa ce bata San Namiji ba Kuma kudin Dana bata ko kwandala bata bata ba ai zalunci ne wannan, Baban Maheerah ya fisge hannunsa yace sai me akan anyi Mata dashen ciki wasu ma suke zuwa suna karuwanci su haihu bare dashen ciki,ita wacece bakar fata da ita bayi,Cele tashi tayi daga Kan Maheerah ta shatulo kafafun Baban Maheerah dake banbamin masifa ya Fadi kasa tim yaji targade a kafarsa, Ahsan ne ya rike ta ganin duk ta haukace tana ta kuka tana kwacewa tana fisgewa taga Babar Maheerah ta tashi Zata sake masgeta ya riketa sosai Yana lallashinta ya rungumeta sosai a jikinsa yana lallashinta,Kansa ya Dora a dokin wuyanta yana lallashinta Yana Bata hakuri,Babar Maheerah ruwa ta samo ta kwarawa yarta ta farfado Suka tashi jiki ba kwari da kyar Baban Maheera ya iya tashi Suka mike a gigice Suka bar gidan gaba daya. Ahsan sai da ya lallashi Cele ta dan daina kukan sannan ya shirya ya rubuta takardar saki ya tafi gidan su Maheerah zai Kai misu,Yana tafiya kuma Cele ta tattara nata ya nata kaf ta Masa rubutu da hausa normal ta ajiye a kujera, ta shiga dakinsa ta Bude inda yake ajiye kudade ta iba zasu Kai dubu dari uku a nan Nigeria tayi tafiyarta ta bar gidan,tana Fitowa Mota ta shiga taxi tace a kaita garin Makkah tasan acan Inshaallah zata hadu da hausawa Kuma Nigeria zata dawo baza ta zauna a Saudiya ba ta Gama Zama a Saudiya har abada, so take tana zuwa ta samu me wuce Mata gaba ta dawo Nigeria ko taga Kaka ko Bata ganshi. Mairo Kuwa watan yarta biyar a duniya baza ma ta bari ta yaye ba akace ga wani balarabe amadina yake zaune bakar fata yake Neman Dan yemen ne zai biya kudi harda sarkar Gold,nan take tace ta yarda Indai zai aureta da yarta,shi dama Local government Kawai yake nema yace ba matsala ya biya kudi aka daura auren Mairo da Mahmud tsohon mijin Mami data Aura ta gudu shi Mairo take rawar kafa zata aura ance me kudi ne zata samu arziki,aka daura aure yau ango yazo ya dauki Amaryarsa da Kansa Yana zumudi ya samu sabo jini. Ina godiya MRS CHIEF AsmaBaffa 08061929616l 'YAR AIKIN KARUWAI 2 MATAFIYA BOOK2 36-40 Official AsmaBaffa SADAUKARWA NE GA ZAINAB USMAN MASU AUDIO WANNAN BOOK NA SIYAR DA SHI, BAN YARDA A JUYA MIN NOVEL AUDIO BA GARKUWAR MATA *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar
Chapter 29 · 0% Book details