← Book details Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 93

Sashe 44

Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tana ta uban bacci,sai ga Auta ya shugo da Sallama ya ganta tana bacci,Mami ta kalle shi tace Yan Makaranta,yace Naam na dawo ya mikawa Nawwar hannu suka gaisa,ya nemi waje ya zauna yana satar kallon Salma yana Galla mata harara Mami tana kallonsa duk abinda yake Nawwar tayiwa signa da Ido Auta harda turo baki yana kallonta yana auna mata zagi a hankali,Nawwar da Mami suna ta masa dariya a boye har Salma ta Farka tana tashi taga Auta itama Ido ta faka ta zabga masa harara har da ce masa Yan Yan Yan kasa kasa a boye,ta murguda masa baki tayi fari ta masa wani up and Down,Mami suna ganin komai ga Auta ya nuna kamar baida hadi da Salma itama haka ba ruwan wani da wani,ganin Mami zata gane su sai Salma tace sannu da zuwa,Nawwar yace lallai yarinyar nan ta iya munafurci ta gama hararsa,Auta yayi murmushin dole sannan yace tashi mu tafi oya come come let's go,ta mike tace Yaya ka gaida Aunty yace to,Auta harda sakalo hannunsa ta wuyanta suna fitowa ya hankadeta saura kadan ta fadi,ta juyo a fusace tazo ta hankade Auta da karfi ta wuce tana tsaki. Mami kuwa tace ka gani ko ji yanda suke harar juna,Nawwar baki ya tabe yace matsalarsu ce ki kyale su kawai. Salma kitchen ta shiga ta dakko juice zata sha Auta yace mayunwaciya look at you kinga banza ta fadi kin wani dakkowa mutane lemo ya fisge ya Maida kitchen,tace ai Kai Kam baka gaji iyayenka ba wlh marowaci akan lemo kalleni tsaf na maka kama da yar yunwa,Kai kana da kudin siya ne? Ba su Mami bane suka zuba maka komai ba ina kaga kudin ko zaka iya siye ne? baza ka iya siyan ko tissue da kudinka ba komai sai an maka Kai tafi can Kuma lemo ne sai na sha sai dai ka mutu,ta Koma kitchen ta dakko, sai ga abincin Mami an kawo musu ,tace nikam na shiga uku komai sai anyiwa me gida bashi da ko taro,Auta ya tsaya kawai yana kallonta sabo da ta buwaye shi ta rainashi da yawa, ta jawo abincin tace mutum komai sai dai ayi masa na zama matar ladan Noma,flask din ya fisge yace ai ba daga gidanku aka kawo ba,hannu tasa itama zata fisge ya rike gam ta kama hannunsa ta gartsa masa cizo,Kara ya saki ya saki flask din ta kwace tace sai na ci to Dan bakin ciki sai dai ya mutu,Auta yana yarfe hannu yace hungry girl mayuwanciya ko kunya bakya ji,tun Ina yarinya na siyar da kunyata ni Kuma a gidana ba Wanda ya Isa ya hana ni cin abinda nake so gidana ne dole inyi abinda nake so yawwa ehe sai dai ka mutu,Auta ya rasa ma me zai ce sabo da haushi yace na tsaneki,Nima haka ta furta tana cin fried rice dinta da kaza tana wani zukar kemo harda wani Jan lemon yana Kara zuuuu zuut tashi daya ta shanye karamin kwalin guda tace Dan jeka kitchen ka dakko min wani,yace baki da kunya ya juya haura sama,sai da yayi wanka ya shirya cikin kana nan kaya marasa nauyi ya fito yana zuwa ya samu taci iya nata ta kwashe komai ta maidawa Mami sauran,tace ya naga kadan aka ci? tace yace ya koshi shi yaci a waje,Mami tace Autan? tace ae yace yaci a school,shike nan cewar Mami ta juya ta tafi ta iske Auta a zauna yana latsa waya yace Ina abincin? Na mayarwa masu shi tunda Kai komai sai dai ayi maka baka San ka nemi na kanka ba,Auta baki Bude yake kallonta yace Amma dai wiwin Baso ta taba Miki kwakwalwa kema? Karka dameni bani da lokacinka,kwafa Auta ya ja ya fita tace yaro karami kusan sa'ana sai Iyayi da nawa ya girmeni ta gyara zama tare da harde kafafu tana cewa wahala ma sai ta sa ka sakeni na koma wajen baso na. Auta bai je wajen Mami ba tunda ta Riga ta fadawa Mami ya koshi sai ya shiga wajen Wise yace wai abinda baya so aka dafa taliya,Wise ta zuba masa abincin ya ci ya koshi yayi tafiyarsa ya bar gidan gaba daya. Bacci taci ta koshi, kamar taci kafar Kare haka yamma nayi tayi wanka ta shirya cikin shadda ta tafi bangaren Wise suna ta Hira tana rage tunani. Washe gari ma haka suka yini fada da Auta ba ji ba gani,har suka kwashe sati biyu a haka fada baya karewa, basa Shiri Sam ganin haka Mami tana fahimta taji tsoro tunda Yara ne kar azo ayi saki, Auta ta samu Yazo gaisheta,tace fada min uban abinda kake boyewa wallahi ko na fita harkarka,yace me kuma Mami? Karka raina min hankali nifa na haifeka nafika sanin waye Kai wallahi Idan baka fada min dalilinka na auren wacce baka so ba to ba ruwana da Kai Karka sake zuwa inda nake,Auta badan ya so ba kawai yace kiyi hakuri Mami ya bata labarin Salma kaf ya fadi gaskiya,Mami tace Auta baka da hankali ashe,Matar da bata sonka kasan kuwa kiyayyar mace Idan ba ta son mutum,me ya kaika wani biyan kudi ka aureta bayan kasan wani take so,Auta yayi mukus Mami ta dinga zazzaga fada,yace Idan kin yarda nan gaba ai zan rabu da ita ma,shut up zaka Raina mana hankali mu ai wasa muka maka ba cewa mukayi zamu yi maka auren dole ba shine ai gashi Kai ka yiwa kanka auren dole Mafi Muni ma,wacce zuciyarta wani take so,to ko da wasa ba saki kayiwa kanka wlh baka Isa ka sake ta ba sai kuyi ta zama a haka matsalarka ce,Mami taji zafin Salma bata son danta dama,amma Kuma Auta shi ya jawa kansa. Zuwa Mami tayi tace Salma ta dawo part dinta kawai aka kwaso kayan Salma na sawa aka bata dakinta a kasan Mami,Shima Auta ya dawo part din Mami da dakinsa,Mami tace kowa yayi harkarsa muga abinda Allah zaiyi. Salma kawai sai ta mike kafa kamar gidan ubanta a gaban Mami ma fada suke yi da Auta. Yau Auta yana zaune Mami tana gefensa tana Yanke masa farcen hannu, Salma ta biyo ta saitin kafarsa tayi fatali da kafar Auta,Mami ta kalleta kawai harda shagwaba kamar uwarta ce Mami tace a canja min channel,Auta yace wai gidan ku ne kin fa ishe mu kina gani Mami ta min ball da kafa Autanki guda kisa ta bani hakuri,Mami tace ke Salma ki Daina haka Mijinki ne fa,Salma tana dire diren kafafu tace ni Allah Allah...shike nan sorry ta zauna ragwaf a kujera,Auta yace bata da kunya fa Mami shame on you ya furtawa Salma,tace na karbe hakuri na Dana baka nafi karfin na baka hakuri,yace ke Dalla kucaka,tace ai gwara ni kaifa kwaila da Kai zaka iya siyen tv ne ko tv Kana da kudinta ta fisge Remote din,Mami tana jinsu bata ce musu kala ba dariya ma take a ranta ana mata maganin Auta,haushi Auta yaji yace Mami kina jinta ko garin kwace hannunsa Mami ta Yanke shi kadan da razor Auta kamar Wanda aka kwadawa Adda ko wani takobi haka yake yana yarfe hannu,Mami tace Kai Kam Allah ya sawwake maka kamar ba Namiji ba,tissue ta sa tare da danne masa wajen,Salma tana masa dariya tace sai kace ba Namiji mu kayi mana shuru. Yace Mami bani ruwa na sha ko na ji salama,Mami ta mike zata dakko masa ruwa Salma tace Mami da kanki kamar wannan ya aikeki ki zamanki ya tashi da Kansa ya sha ya dawo,ke da uwata Zaki rabani marar tarbiyya ya ja tsaki,Salma ta dauke Kai taci gaba da kallonta. Salma Allah ya yita da gasa sabo da yarinta da kuruciya Idan taga kusan sa'anta yana abu sai ta fara yi itama,Auta ta Raina an mata kananan kaya sunfi akwati biyu sabo da su can normal ne ana sawa bare Kuma matar aure,ganin Auta kullum cikin kana nan kaya yake sai itama ta koma sawa su normal ne amma sabo da ita ba a can ta taso ba tana ganin ko mace ce ta shugo sai taje ta Sako katon Hijab,komai Auta yayi sai tace sai tayi itama,Idan Mami ta masa abu itama fa sai anyi mata,daga gani Mami ta taje masa gashi,sai bayan kwana biyu tazo gaban Mami ta durkusa har kasa tace Mami kin iya kitso ki min Nima? Mami tace na iya,tace kalaba nake so,tace to bari ayi Sallar la'asar tace to,ita Salma tana birge Mami sabo da biyayyar ta da kunya sannan ga addini Sallah bata wuce,Auta 4pm ya dawo daga school ya shigo ya dora Kansa a cinyar Mami sai ga Salma ta fito ta bata rai tace matsa min,ko kulata baiyi ba,tace Mami kice ya matsa min ai kitso za a min tsaki ya ja ya tashi ya koma daya kujerar kasa kasa tace kwailan Miji kawai tana turo baki,Mami dariya ta kamata haka yake cewa Mata ko wacce yace kwaila ce yau gashi an ramawa su Omaira cikin ruwan sanyi,ran Auta Idan yayi dubu to ya baci kamar zaiyi kuka zaiyi magana Mami tace enough haba Enough of this nonsense ku kullum fada ke Salma Mijinki ne fa kike masa, haka kikaga anayi akan banzan tunaninki,sabo da bakwa son juna ku zauna lafiya mana,bana son rashin kunya Salma Mijinki ne fa ke ana lallaba Miji ana masa biyayya ke Banda ke kowa haka kika ga yana yi,Kai ma ba ruwanka da ita kowa yayi harkarsa, Auta yace dama matsalar da nake gudu kenan da auren kwailar yarinya indai ka hada harka da kwaila to ka shiga uku yanzu babba me hankali wacce tasan me takeyi zata yi abinda wannan sharar takeyi wannan tarkacen,indai mace ta mallaki hankalinta Ina zaka ga wannan shirmen,Ya Isa haka kayi hakuri kuyi hakuri da juna shi yasa fa na dawo daku nan gabana wato ban Isa ba ko bani da amfani,Salma zama tayi a kasa a gaban Mami tace kiyi hakuri Dan Allah tana so tayi kuka,Mami ta cire mata dankwalin gashinta dogo baki yala yala da shi ya bayyana yana sheki Mami tace Masha Allah Auta ya tabe baki tare da dauke Kai,Ita Kuma Salma dama ta Saba da kuka a gida tunda kullum sai tayi ita da Baso,Basonta ta tuna ta fashe da
Chapter 44 · 0% Book details