← Book details Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 93

Sashe 48

Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nawwar ya fada min ai gashi nan, da a baya Ina nasan wani tunani a rayuwa,na taba zaton akwai abinda zai iya hanani bacci a duniya,har na zauna Ina tunani sai wannan banzar, horn din duniya taki kulashi Idan ta koma Kuma ta fadawa Mami ayi masa fada. Fitowa yayi da niyyar mammaketa ya fito kenan wani me machine ya taho a dari ya takewa Auta kafa faduwa yayi ya rike kafar yana Kara da ihu,mutane suka taho Salma juyowa tayi ta Ganshi a kasa yana ihu ta Riga kowa tsallakowa tana cewa wayyo Sannu ta rike Auta tace kaga halinka ko sai fitina me ya kaika tsallakowa wlh baka jin magana yanzu gashi ka jawo an take ka,Auta yana murkususu yana rike da kafa cikin masifa yace ba ke kika jawo ba sai naci ubanki,Sorry ai ban San machine zai takaka ba ta furta, Yan school ne suka dauki Auta,Me machine yana ta bada hakuri Salma tace Kai Dalla yi mana shuru aikin banza sai ku dinga sharara uban gudu gidan wa zaka je haka ko sama zaka tashi ko matarka ce zata haihu ai sai haka ta ja tsaki ta shiga mota aka tafi da ita asibitin wani Dan ajinsu ne ya ja motar. Mami ta Kira ta fada musu kafin kace an cika Private hospital kamar wani Dan Gold,Mami ta tambaya me ya kaishi tsallaka titi,Salma tayi Miki Miki a hankali tace rigima fa irin tasa,fitinar tsiya baya ji,kowa dake wajen sai da Salma ta bashi dariya kamar itace Yayar Auta,Auta yace wlh itace gata nan ya kwashe zance ya fadawa Mami,Mami tace Wise Kira min Baso aka Kira Baso,Salma duk ta tsure,Mami da kanta ta fita sukayi magana da Baso yace ku sa masu gadi su huta ta dinga Bude gate tana rufewa sannan ta kula da Auta har ya warke abinci da komai nasa ita zata yi sannan ku kaita gadin gate,Mami ta dinga dariyar muguntar Baso,ta mikawa Salma waya yace kina ji na? Tace ae,yace gobe zanzo Zaki ci ubanki,Salma sai kuka Baso yace zaizo, a ranar aka yiwa Auta aiki wasu kasusuwansa na kafa sun goce kafar har ta kumbura sumtum. Washe gari da wuri sai ga Baso yayi kyan gani yanzu da gani ya samu canji,ya samu Salma tuni ta fara kuka tana bashi hakuri tace ko mene zanyi indai zaka hakura,Yace yanzu kullum da asuba gate Zaki tafi ki dinga tura kofa kina rufewa ga duk Wanda zai fita a gidan nan,Sannan abincin Auta duk kece Zaki yi,sannan ki kula da shi har ya warke,Salma tace haba Yaya Baso yace ke kinci....zanyi zanyi wlh, tsaki ya ja yace na sa a fada min Idan baki ba zan sani karki bari na bar abinda nake na dawo gidan nan sabo da ke wallahi baza kiji Dadi ba ya juya ya fice ko Sallama yayi tafiyarsa mota ya bi. Mami taji komai tana wajen,tace to gamu duk shedun Baso ne Idan kika ki yi zamu fada masa,Baffa ma da Papa da suka ji suka dinga dariya gaskiya Baso ya iya punishment ai gwara haka ko ta yi hankali,ba Wanda ya goyawa Salma baya Kuma kowa ya fita harkarta kamar yanda Baso yace musu, ba Wanda ke kulata a gidan yanzu. Washe gari aka sallami Auta an bashi sandunan karfen ya rike suka dawo gida gaba daya har Salma,tana fitowa Mami zata dauki jakar Auta,Baffa yace kyale Salma zata dauka,takaici ya kama Salma amma haka ta Bude mota ta dakko tana kunci,Baffa yace muje Honey Salma zata raka shi ciki ya janye Mami,Mami bata so a zakunci danta amma ta hakura suka tafi aka bar Salma da Auta,yatsa tasa ta taba shi wai muje tana turo baki,yana tafiya da sanda tana binshi a baya a hankali har bedroom dinsa rike shi tayi ya zauna a gefen bed ya kalleta yace abinci zanci na sha magani,me? ta tambaya, da fada yace abinci nace zanci na sha magani duk ba a dalilinki na shiga wannan Halin ba,ficewa tayi taje kitchen ta samu anyi girki ta zubo komai a tire ta shugo tare da ajiye masa a saman bed ta juya tayi ficewarta tana cika tana batsewa,Auta yayi murmushi kawai,yaci abincinsa ya sha magani ya kwanta,har ta zauna Wise ta shugo tace baki ji horn bane a gate kije ki budewa mutane gate,Salma ta tashi ta tafi tana hawaye ta hau tura gate tana fushi,Nawwar ne ya shigo ta rufe gate, duk babu masu gadi an basu hutu,Nawwar ya kalleta tace Ina kwana Yaya ya amsa da fara'a Shima yasan komai ya wuce ciki abinsa. Wani horn aka sake yi tazo ta bude tana faman yarfe hannu zafi wai hannunta Mami da Baffa ne zasu fita ta dauke Kai gefe daya,Baffa glass ya sauke ya mata horn taki juyowa yace hey gate woman juyowa tayi ta danyi murmushin gefen baki,suna fita ta tura gate ta rufe ta koma kujerar masu gadi tare da zama. Kitchen ta Koma tana girkin Auta tana zuwa bakin gate ko za a shigo sai faman zirga zirga take daga part din Mami zuwa Gate,tana sani ta zazzagawa Auta yaji da yawa a cikin abincin har ta gama ta hada komai a tire ta dauka ta nufi dakinsa yana kwance yana bacci tace Malam tashi ka jefa ni a masifa kazo kana wani bacci,Ido ya bude a hankali ya kalleta kawai ya ja tsaki yayi murmushi,ya kalleta again yace zan tashi zaune ya Miko mata hannu tazo ba musu ta taimaka ya tashi zaune tana fushi, yace kafar tana kaikayi a min massage kadan,kamar ta daki Auta zama tayi a gefen bed din,ya dora kafarsa a saman cinyarta,ta kalle shi da sauri ta turo baki ta kama kafar Auta me kyau ta fara masa Massage a hankali har da lumshe Idonsa, tana Dan yi yace ya Isa haka na gode,mikewa tayi yace a wanke min kaya ayi min guga sannan azo a taje min gashi,ni na Saka tara gashin wai ta juya ta koma kitchen ta ebo abincin itama ta tafi baki gate da shi tana ci a can tana turawa masu shige da fice gate,Sabreen ce tazo zata fita da motarta ta sauke glass tace me gadi a bude gate fast please sauri nake,Salma ta mike tana doka kafafu ta tura gate,Sabreen ta fice ta Maida ta rufe ta koma taci gaba da cin abincinta,tana gama ci ta koma ciki ta gyarawa Auta dakinsa ya shiga wanka lokacin,Fitowa yayi daure da towel rike da sandunansa yana dogarawa da kyar,ta wuce toilet din ta wanke Kal ta fito fuuu,ta dauki Cumb tace zauna Malam,Auta yace bai bushe ba, ya Mika mata karamin towel yace ki tsane min na gaji,tana hararsa ta karba ta dora a gashinsa tana tsane masa gashin har ta gama ranta a bace,ta dakko handrier ta fara busar masa da gashi har ya bushe ta dakko man gashinsa t a shafa masa kamar ta dake shi haka take ji, ta fara taje masa gashi yace da zafi fa irin wannan cisga haka,ya saki Kara tsayawa tayi tana kallonsa cikin kunci sannan taci gaba da tajewa a hankali ta gama tsaf ta dakko man lebensa na maza ta shafa masa tace oya yi haka ta hade lips dinta,Auta yayi yanda tace,ta gasa masa harara tace fitinanne ta doke shi kadan a gadon baya wani tasss tace ladan aikina. Wanka tayi a gurguje ta shirya cikin Atamfa Riga da skert maroon ta koma jikin gate da botikan wanki da kayan Auta ance Kuma baza ta wanke a washing machine ba tana zaune tana cin uban wanki kayan da yawa dan ma ba dirty,Mami da Baffa ne suka dawo ta mike ta Bude musu gate ta koma taci gaba da wankinta,Mami tace Allah yayiwa Baso Albarka ya kawo mana maganinta yar banza irinsu sai da wahala suke ganewa. Tana ta wanki ta daga boxers din Auta tana bata rai tace bari Muji ta shinshina ta sake cewa bari Muji saitin wajen Abar inda take zama ta shinshina tace Allah ya taimakeka suna kamshi,da gani wannan tasa karama ce ko ta Baso baza ta Kai ba,yo sau nawa Ina ganin ta Baso a wando katuwa tafi karfina ma ta Baso,gashinta ta Sosa tayi dariya tace Allah ya shirya ni la'ilahaillallahu ai na Kalli ta Baso a wando na more bai sani ba. Kafin ta gama Mami ta fito ta fito tace gobe da sassafe ake bawa flowers ruwa da garden ki tabbatar kinyi,Salma kamar zata yi kuka haka tace to. Tana gama wanki ta shanya ta koma bedroom din Auta tace na gama maka Malam? yace yes you can go yana kunshe dariyarsa, tace yanzu da yajin nan ka cinye abincin nan? Yace ae mana au yayi yaji dama? Ido ta zaro tace tab wani takaici ya kamata shi bai ma San da yaji ba,Auta kuwa da kyar ya iya ci Kuma yana sani ya nuna mata ba yaji sabo da yasan dan ta bata masa rai tayi to ya nuna Sam baiji yajin bama. daure fuska tayi ta fice. Tana gama aikin nata tayi Shirin bacci ta fada saman bed sai bacci a gajiye. Umma ce taga kayan Abinci ana ta sauke mata mota guda wai inji Miracle,murna ta ishi Umma, Omaira tazo tace na Umma ne ita kadai Wanda basa son mata ai Bai kamata suci kayan mata ba ta sa aka shigewa da Umma kayan Abinci kaf dakinta,sai sutura gasu nan iri iri wai Umma ta Dinka suma su Omaira da nasu,ga kudin cefane.sai murna suke har su Bilkisu wahala ta Kare,Abba da Uwa sai zare Ido suke sun rasa inda zasu sa kansu, Washe gari Nawwar ya turo abokinsa Khaleel ya dauki Umma zuwa cikin wani katafaren gida na gaske yayi kyau matuka a unguwa me kyau Umma taga komai an zuba furniture da komai na more rayuwa tace gidan waye wannan kuma? Khaleel yace naki ne inji Nawwar ki dawo ciki ki zauna takardun gidan ya Mika mata,Umma harda kukan farin ciki da ta tuna irin wahalar data sha a rayuwa da haihuwa a gidan Abban su Omaira,Khaleel yace ai ba kuka zakiyi ba Umma sanda kuka ga dama ku tare,Umma tace wa? Dannan ai nazo kenan tace na dai yi waya yaran su kwaso kaya suzo nikam ban
Chapter 48 · 0% Book details