Sashe 97
Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Asma’u kenan, baki da aure domin suffarki ta nuna kamala. Babu yanda za’ayi ki fito da irin shigarki ta yau alhalin kina da aure dukda hakan ba wani abu bane ga amma na tabbatar da ko shi mijinki baze taba bari ki saka kayan da zasu bayyanar da kyanki haka ki tafi qulla alaqar kasuwanci da wasu maza ba ko da yake bansan irin mijin da kike aure ba”.
Mamaki ne ya kamani kwarai, ya akayi ya san sunana sannan har ana iya gane macen da bata da aure daman tunda dai ni banyi kala da budurwa ba bare yace sannan daga kira ka fara zayyana mun wani zancen aure harda wasu matansa uku ni Asma’u ce zan fita daga gidan me daya na fada wa uku Allah ya mun tsari.
Kai duk ba wannan ba Allah na tuba ina ni ina wannan mutum haka firit kamar ruwan aski? Ai wallahi ko qaruna ne shi qarewar kudi yanzu dai in rabu da Namiji Kamar Bashir naje na auri wannan busashshen da na kasa tantance tsufane ya figeshi haka ko kuwa abinci ne baya ci kai qilama sickler ne kaga kuwa Bashir se yayi mun dariya dakyau.
“Kinyi shiru Asma’u baki ce komai ba” ya katse mun shirun. Dabara ce ta fado mun ta yanda zamu rabu lafiya tunda dai shi wannan ya wuce mutumin da zance zan wulaqanta ko na kora dan haka nace masa
“Tabbas ranka ya dade mun rabu da mijina amma gaba daya be wuce sati biyu da faruwar hakan bama kaga ban gama iddah ba yanzu baze yuwu na saurari wani namiji ba”.
“Hakane, toh babu damuwa zan jira dan na yaba kuma rabona ce ke, ki turamun da account Number dinki yanzu za’a saka miki saqo”
“Babu komai na gode Rabka ya dade na dazu daka bamu ma ya isa”
“Ni nayi niyya idan kuma baki turo ba zanyi waya har kamfanin naku yanzu su turamun daga can” ya sake fada, gaba daya maganar tasa ta gundureni, dan haka da sauri nace
“Toh shikenan zan tura maka yanzu, Nagode Allah ya qara arziqi” qit na kashe wayar ban ajiyeta ba seda na dannan masa block, na dakko katin daya bani nabi duk numbobin jiki nayi saving dan karma ya kira da wata Number na daga ban san shi bane.
“Haka kawai toni ko auran zanyi ai ba irin ka zan aura ba” na ringa mita ni kadai na shige bayi.
Ina sallar Isha su Abdallah m shigo da gudu yacemun wai nayi baquwa, seda na sallame kafin na fita wajen da hijabin jikina ina mamakin wacece wannan zata zo mana da dare haka.
Turus nayi ganin Amirah dake tsaye farar fuskar nan tayi jajir kamar ma mari tasha. Cikeda fitsara ta waiwayo tana cewa
“Wallahi kijawa Yaranki kunne dan ni ba jakar su bace da zan ringa dafa abinci su tsallake au qi ci kuka ubansu yazo yana mun fada kuma wallahi duk abinda aka mun akan su zan rama ehe”.
“Yanzu qara kika kawo ko jan kunne kika zo kiyi mun? Wai ma bana gaya miki karki sake shigowa gidan nan ba? Ina ruwana da shirgin ku mena hada dake da zaki shigomun gida kina fadamun magana.
Naga alama kin kwana biyu jikin ki be fada miki ba toh kiyi a hankali idan ba haka ba kuwa sena ladabtar dake tunda naga ke baki da hankali ba kuma ki da tunani, abinci kuwa a gidan ubansu suke ko suci ko kar suci dole ki dafa ki ajeye musu idan kuma kinqi kinsan sauran base na gaya miki ba, wuce ki fita tun ban lakada miki na jaki ba anan” na qarasa ina nuna mata qofa, nazata zata sake magana se naga ta juya tana qunquni ta fita a fili na fuskar ta
“Mara kunyar banza, ai da kin tsaya na koya miki hankali. Ku kuka (na juya kan yaran) daga yau ku ringa tsayawa a gidan ku kuna cin abinci idan baqu qoshi ba se kuzo nan ku qara kunji ko”.
“Wallahi Mami bata iya abinci ba, jiya fa data saka wani kifi a spaghetti har yanzu ina jin qayarsa a wuyana qarshe fa a bola ta juye abincin kowa yaqi ci” Jafar ya fada kafin nayi magana Faridah tayi caraf tace
“Waifa doyar da bamu ci da safe ba ta dumamawa Abbi shine ya ringa mata masifa, yanzu ma yana daki a kwance Kamar Bashida lafiya ina ga kuma yunwa yake ji, Mami ki bamu abinci mu kai masa dan Allah”.
Tsayawa nayi ina kallonta, dagaske Bashir bashida lafiya to me ya same shi? Na san dai yunwa tana iya kwantar dashi dan sam bashida jimirinta toh amma ni ina ruwana meye nawa a ciki shida ya dakko yar gwal ai seta dafa ta bashi.
Da zasu tafi Faridah da shegen naci seda ta dibar wa Bashir Friedrice da pepper chicken din da Amna tayi ga hadin kosulo abin dai ba’a magana na qara musu da zobo roba biyu sadaka nace ta kai masa.
BASHIR
Gaba daya haka ya wuni a office ya rasa me yaje masa dadi, ga damuwar rabuwarsa da Ma’u da se yanzu abin ya fara dukansa daya tabbatar da ta kufce masa se yayi da mugun gaske kafin ta sake dawowa hannunsa.
Ya rasa wa ze gayawa damuwarsa, a wannan karon be karbi shawar Bala ba gani yake kamar bazata fiddashi ba, amma wani lokacin idan ya tuna irin son da Ma’u takeyi masa se yaga kamar duk buyagin iska kawai takeyi na dan lokaci zata sakko su koma zaman su.
Wai ma shi me yayi mata ne? A iya saninsa laifi ta masa ta qi bin unarninsa kuskure daya da yayi shine daukar matakin saki a cikin fushi kuma har biyu, daya sani hutu ya bata na lokaci ya fita sabgrta har se ita da kanta ta dawo ta nemi shiri ta kuma yarda da sharadin daya bata kafin su daidaita amma yanzu ya lalata komai, ya bi rudin shedan ya rabu da Ma’unsa.
Ita wadda Shedab din yayi masa kururuwa akanta gashi nan ya dakko ta idan bada gasha shi babu abinda take yi ko iya horon yunwar da take masa aka barsu na shekara daya yasan dakyar idan bazatayi ajalinsa ba wai shi wannan wane irin bala’ine yake tun karar rayuwarsa.
Wayarsa ya dauka ya shiga neman Number Amiru qaninsa da tun ranar da zancen sakin Ma’u yaje Gombe ya kirashi dan yaji menene gaskiyar zancen ya kuma tabbatar masa da anyi daga ranar basu sake magana ba.
Ya kirashi sau ba Adadi amma Amirun baya dagawa daga baya ma blocking dinsa yayi, haka Naziru ma baya amsa wayarsa to yan uwansa ma kenan kuma shi bashi da sauran wani shaqiqij Abokin da ze tattauna wannan matsalar in banda Balan se Abubakar da ko giyar wake yasha be isa ya tun kare shi a yanzu ba.
Abdulkarimu ne ya fado masa a rai, ba bata lokaci ya danna masa kira kuwa akayi sa’a ta shiga seda ta kusan tsinkewa kafin ya daga wayar
“Alhaji Bashir yaushe rabon da ka nemeni tunda giwa tayi lafiya ka samu kan Madam shikenan ka watsar dani” Abdulkarim ya fada bayan da suka gaisa. Seda Bashir yaja numfashi kafin yace
“Abdulkarim ina cikin Bala’i na rasa yanda zanyi wallahi ka taimaka mun”
“Allah yayi mana maganin abinda ya damemu, lafiya dai Bashir meya sameka haka kake dangana kanka da Bala’i?”
“Abdulkarim hau ce ta hauni, nabi dokin zuciya na saki Ma’u gashi yanzu harta gama iddah ban mayar da ita ba na rasa inda zan kama ji nakeyi kamar zan haukace, yanzu har ta fara kula wasu Mazan sau biyu ina ganin ta a motar Maza Abdul” ya qarasa maganar kamar ze fashe da kuka saboda yanda yakejin zafi a duk sanda ya tuna ganin da yayiwa Ma’u na jiya dana yau din.
Salallami Abdulkarim ya ringayi yana cewa
“Ka saki Ma’u Bashir wace irin hau ce kai kuwa take binka haka ka rasa matar da zaka saka a rayuwa se Asma’u, Asma’u fa Bashir toh wallahi babu ruwana, abu daya zan iya maka inyi maka Addu’ar Allah ya taqaita maka wahala na kuam roqeshi karya maido maka da Asma’u rayuwarka dan baka san darajarta ba”
“Idan Allahn naka ne seka roqeshi karya dawo mun da ita din, na kiraka ka bani mafita shine zaka zageni kayi mun fatan tsiya ko? Daman nasan ba qaunar zama na da ita kake yiba, to dakai da duk sauran masu jin dadin abinda ya faru kuna kallo Ma’u zata dawo mun sedai baqij ciki ya kashe ku ku mutu”.
“Allah ya yafe maka Bashir” Abdulkarim ya fada kafin ya kashe wayarsa.
Bashir kuwa hada kansa yayi da teburin gabansa yana sauke numfashi, babu abinda yake cizon zuciyarsa irin idan ya tuna ganin da yayiwa Ma’u da wasu, Matarsa Ma’u da wasu qartin maza da sunan zawarci.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, Allah ka kawo mun dauki, Allah karka barni da iyawata” ya fada a fili yana sake wawurar wayarsa, dole ya ajiye duk wani abu a gefe ya kira Baba, ko ze zageshi kai idan ma ta kama yaje ya tsugunna a samowa Baban bulala ya zane shi duk ya yarda indai ze saka baki Asma’u ta haqura ta dawo masa dan yasan a yanzu dai su biyu ne zasu iya shawo masa kanta babu musu ta yarda daga Baban se Goggonta, shi kuwa dai rashin kunyar tasa bata kai ya tunkari Goggo a yanzu ba dan yaci ace kafin ya saki Ma’u ya tuno da karamcin matar amma duk ya hada ya take to wai shi me tayi masa ne ma??
Sallamar da Baba yake ta faman kodawa ce ta dawo dashi hankalin sa ashe wayar ta shiga tuntuni yana can zurfin tunani be sani ba.
“Barka da rana Baba, ya qarfin jikin?”
“Barka dai Bashari, jiki Ahamdulillah idon ka kenan se yau zaka kirani ko da yake kaida kake da Amarya ai dole ayi maka uzuri” Baban ya fada babu wata damuwa a muryar sa.
“Ayi haquri Baba” Bashir ya fada yana gyara zama, yanda yaji Baban a sake ya qara masa kwarij guiwar fadar abinda yake ransa.