← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 158

Sashe 44

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ba yanzu ba Sheik baku isa riqe waya ba amma zan chanza muku PS 5 gobe kuma za’a kawo muku” ya fada yana zama akan kujerar da take kallon wadda nake kai. Sabon ihu suka dauka harda yan biyu dan suma sun koya musu Game, ba damar a samu zama a gida anyita buga PS sena gaji wani lokacin na dauke.

Ina kallon yanda yake ta wani murmushi yana jin dadi ganin yaran na murna an shirya kenan, yana kallona na sake hade girar sama data qasa, sen miqe ma ina cewa Farida idan sun gama tura hotunan da sukeyi daga wayata ta miqomun na shige dakina a jikana ina jin yanda ya bini da kallo amma ban waiwaya ba.

A dakin ma ban zauna ba, wanka na shiga nayi shirin bacci, sena dakko Backpack din da nake zuwa office da ita na fito da kayan ciki ina dubawa dan nima ranar Monday zan koma aiki in Allah ya kaimu, gajiya da jiran Farida nayi sena leqa dan ina so na kwanta har sannan suna zaune Bashir na nuna musu ko menene oho a wayarsa.

“Farida bani wayata, bazaku tashi kuje ku kwanta ba ko gobe akwai school fa” na fada daga bakin qofa. Seta taso da gudu ta bani ta sake komawa,

“Oh ina magana duk kunyi mun shiru ko” na sake fada, se Bashir ya dago yace
“Babu aiki gobe Workers day”
“Au toh, seda safen ku” na fada ina juyawa ciki.

Harna kwanta naji message ya shigo wayata, kamar bazan duba ba sedai na janyota, Bashir ne
“Ina son magana dake” ya rubuta. Guntun tsaki nayi na maida wayar na ajiye naja bargo na,

Befi minti uku ba tsakani kira ya shigo, sauri nayi na sakata a silent, ina kallo seda yai kira uku nai likimo abuna dan bazan dauka ba, wato nice baze lallaba ba tunda ya shirya da yayansa shikenan ba ina cikin wannan tunanin naji an turo qofa.

Luqus nayi harda wurga qafa gefe dan fitila a kashe take ni a dole bacci nakeyi, ina jinsa ya kunna hasken ya tsaya akaina yana kallona.

“Ma’u Ma’u” ya fada yana bubbuga pillow da nake kai, senayi miqa tareda qantsarewa ina salati irin an tashen nin nan nayi mici mici da ido ina kallonsa nace “Lafiya zaka zo kana tashina a bacci”.

Seda ya zauna gefen qafafuna ya wani kumbura baki yace “baki ga message dina ba da calls dina ba?”

“A mafarki ka turomun halan” na fada ina tura baki gaba. Se da yayi kwafa sannan yace “saboda abinda ya faru yasa kika dauki fushi dani, naga wanda na doka din ma mun shirya se kece zaki ci gaba da gaba dani”

“Ni kuma inyi fushi dakai ana me Baban Ali space dai na baka ka gama zaman makokin idan ka dangana kayi tawakkali se mu ci gaba da magana” na katse shi ina gyara kwanciya, gajeran tsaki yaja kafin yace

“Oh banida tawakkali kenan”

“Ni awa ince baka da tawakkali, hausa nayi maka bawai abinda nake nufi kenan ba” na fada ina danne dariyar dake neman kufce mun ganin yanda yai kinini da fuska yana jan iska.

“Gobe da asuba zamu tafi Delta inaga zamuyi kwana biyar ko sati saboda tafiyar nema yasa ban tafi Gombe ba”

“Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya” na fada a qagare dan na fara jin baccin gaske, se ya miqe yana cewa “ta so muje can, ban hada kaya ba kuma ina so nayi bacci kinga fitar Asuba zamuyi”.

“Yi gaba gani nan” na fada ina miqewa kamar zan shiga bandaki, yana fita na rufe qofar na murza key, a fili nace “Dan rainin wayo sedai ka tafi babu kayan kuwa” nai hayewata Gado na kwanta ina jinsa yana kiran suna na yana kwankwasa qofar a hankali nayi biris dashi harya gaji ya tafi, duk randa ya koyi karbar laifinsa, ya iaya bada haquri ma shirya.

Da Asuba da muka hadu kamar kububuwa ya wuceni ya shiga kitchen, ya gama diri dirinsa ya fito daman nasan ba abinda ze iya tsinanawa mutumin da inaga ruwan zafi kadai yasan yanda ake dafawa. Amna ya kwalawa kira ta fito daga dakinsu yace maza ta soya masa kwai.

Ina kallonsa ya shiga dakin ya fito yana doka uban tsaki ya kalli inda nake ya sake komawa seda ya shiga sau biyu ana ukun ne yace “Dan Allah Ma’u kizo ki hadamun kaya su Musa har sun kusa qarasowa”

“Au wai baka hada kayan ba me kake jira toh” na fada ina tashi zaune akan kujera.

“Kin sani ban iya ba ke kike hadamun, please Ma’u”.
“Badan halinka ba muje” na fada ina miqewa. Kusan rabin wardrobe din ya watso su qasa, cikeda takaici na shiga hada masa kayan a qaramar akwati na gama ina zugewa ya shigo da kofin shayi a hannunsa ya ajiye akan mudubi yana cewa “har kin gama”

Ban amsa ba na shiga kwashe na qasan ina mayarwa, horn da muka jiyo daga waje yasa na dakata na daukar masa Laptop bag dinsa shi kuma yaja akwatin muka fito, Jafar na tsaye a kofar dakin su ya gaishe shi yace “Abbi a kawo fa”

“Za’a kawo Sheik ina sauran yan uwanka”

“Sun koma bacci Abbi”
“Ok idan sun tashi ka gaya musu na tafi Delta zamuyi waya idan na sauka” ya fada yana tafiya.

“Allah ya tsare Abbi” Amna da Jafar suka fada. Daga bakin qofa na tsaya ya miqawa Driver Akwatin ya karbi jakar hannuna bayan na masa Adawo lafiya naja kofar na koma ciki. Seda na kwashe kayan da ya zubar tsaf ina mita “Abinda ko Su Muhammmad baza suyi mun ba shi yake yi, da yake buqatar kansa ce ai ya iya roqa a masa mtsw” naja tsaki.
A dakin na kwanta na qarasa baccina.

GOMBE

Acan Gombe kuwa ranar talatar da safe Bashir sukayi waya da Naziru ya gaya masa yaje Asibiti ya karbi Iman daga nan ya wuce da ita gurin Dada kafin ya gama yanke abinda za’ayi.

“Ni se nake ganin yaya da kayi haquri, be kamata ace ka raba Uwa da yarta ba idan kayi haka kamar ai bakayiwa Amirah da ita kanta Babyn Adalci ba. A yanayinta tana buqatar dumin uwa da kuma Nono ko dan ingancin lafiyarta” Naziru ya fada bayan da ya gama jin umarnin yayan nasa.

Shiru Bashir yayi, Tabbas gaskiya Nazirun ya fada amma toh amma meye amfani mayar mata da ita ma yanzu bayan ta riga ta yaye ta kusan sati bata sha Nonon ba se madara ai dakyar ma idan zata karba yasan, kuma fa shi ya gama yanke hukuncin sa ta hakane kadai ze hukunta Amirah taji a jikinta yanda gobe bazata sake gwada yin abinda tayi ba.

“Kaje kawai ayi yanda nace, na rigada munyi magana da Dadan, zuwa Next week idan na samu dama zanzo nan Lagos zan dawo da gurin Ma’u”

“Anty kuma? Ita tace zata riqeta?” Naziru ya tambaya cikin mamaki. Se Bashir din yace

“No, bata rigada ta amsa ba amma ai gida nane ina da ikon sawa da hanawa ko”

“Hakane” Naziru ya fada sukayi sallama, a ransa yana mamakin wannan zallar rashin Adalci irin na dan uwan nasa. Tayaya zaka taba jaririya da uwarta ka dauka ka kaiwa wata wadda ita kanta tana da buqatar me taimaka mata. Ÿaÿa Bakwai nefa a gaban ta take kula dasu ga shi sannan kullum seta fita aiki ai wallahi ko ita kanta yanzu kamata yayi yace ta dakata da haihuwa ta ji da abinda yake a gabanta balle har ya dauki raino ana zaune lafiya ya kai mata.

Daman lokacin daga wanka ya fito dan haka ya zura rigarsa ya cewa Dada bari yaje Asibitin ya karbo yarinyar “Amma fa Dada kiyi masa magana idan ba haka ba wallahi ze janyo abinda za’a zo ana samun sabani daga qarshe kuma ace za’a ga laifin Anty Ma’u” ya fada yana tsaye daga bakin qofa.

“Ka rabu dashi Naziru, gurin uwarta za’a maida ta, shi a ina ma ya taba ganin anyi haka? Idan so yake ya kaita cikin yan uwanta se ya bari idan Allah ya rayata ta isa sakawa a makaranta a sannan yana da hujjar da ze iya dauketa ya maida ita can ko dan ta samu ilimi irin na sauran amma ba yanzu ba. Ni wallahi na rasa me yake damun Bashir, mutum tamkar wanda yake da wani motsi a kansa”.

“Ba wani motsi wallahi Dada tsabar samun gurine tunda yaga duk sharar daya debo kina goya masa baya shiyasa”.

“Yanzu dai jeka, idan ka dawo se muje tare can gidan nasa, dukda ya kamata na kirashi ma yabar yarinyar nan ta koma gida tayi jego ko ta dawo nan dole se an taimaka mata kafin ta saba ai” Dada ta fada, Naziru yayi mata sallama ya tafi Asibiti.

Yana zuwa ya tarar da wannan tashin hankalin, bashida karfin guiwar kiran Bashir dan haka likitan ne ya kirashi shi kuma ya kirawo Dada ya gaya mata.

Bayan an gama cike ciken takardu ya saka hannu aka bashi gawar, be iya tafiya ba seda Ya kira Sa’ad Yayansa da yake bi yazo suka tafi tare suna kaita gida Dada tace suje su dakko Amiran sannan ta kira Ummi a waya tace suzo ita da Addah yanzu.

Fadar tashin hankalin da Amirah ta shiga bata baki ne dan sumanta uku ta ringa kururuwa tana ihu kamar wadda ta hau bori, se da Goggo Ladi qanwar Alhajin su Bashir tayi mata tatas sannan aka samu ta lafa da ihun amma fa bata dena kukan ba.

Addah kanta tasha kuka fadi take daman yan baqin ciki basu so aka haifeta ba gashi yanzu anyi manaqisar da seda aka rabata da duniya su dai Allah ya isan su bazasu yafe ba.

Babu wanda ya ko bi ta kanta, da dare yayi zata tafi da Amirah Alhajin su Bashir ya hana yace ta barta acan dan yasan idan sun tafi ma a maimakon ta taishe ta Allah kadai yasan abinda zata je ta kitsa mata kuma.
Chapter 44 · 0% Book details