← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 158

Sashe 127

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba kowacce mace ce take da qarfin zuciyar daure wasu abubuwan ba, wata koda ba ta sigar fasiqanci ba, wata da sunan aboki zakaga ta hadu da wani namiji da zasu zama kamar wasu Qawaye ko Aminai duk wani sirri nata daya kamata ta yi shi tare dakai shi ze maye mata gurbi ya zama abokin shawararta se kaga matar aure wai tana da wani Besty duk waya ja Mijinta kuma ka tabbatar duk dakon zunubin da zatayo tare za’a kasafta muku dan kai ka yanka mata tikitin da har zata kula wani banza can da auranka.

Ka duba yanzu ko a gurin aikin mu yanda mata suka lalace matan aure kaga suna qazamar rayuwa suna mu’amala da wasu mazan a waje da bana auransu ba a kaso goma idan ka tarasu bakwai wallahi mazansu nada sa hannu cikin fadawarsu wannan halakar saboda basu da ma lokacin su ballantana su san damuwarsu har su maganta musu ita da yawan maza muna dauka kudi shine maganin ko wacce matsala idan ka wadata mace shikenan ka gama mata komai wanda sam abin ba haka yake ba dole ka kula da matarka ta kowanne bangare ka tabbatar da cewa ka toshe mata duk wata buqata idan kayi haka kuma kaga wata matsala ta faru seka qaddara cewa jarabawa ce kuma daga ubangiji amma ba wai dan kai ka bayar da qofar faruwar hakan ba.

Dan haka nidai shawarata Bashir ka canja takunka, ba Asma’u ba ko wacce mace zaka zauna da ita dole ne kasan qima da martabarta. Ka sani cewar ba Alfarma kayi musu daka auresu ba ballantana ka dauka dole suyi haqurin zama dakai da halinka Aa zamane na ibadah da Allah ya hadaku kowa yana da haqqi akan dan uwansa”

“Haka ne kuma zanyi qoqari na gyara kuskurena Musa dan ina buqatar Ma’u a rayuwa ta wallahi” Bashir ya fada bayan daya sauke tagumin da yayi.

“Au saboda ka dawo da Asma’u zaka chanja hili kenan? Bashir bari fa na gaya maka gaskiya Halinka cikin goma bakwai basu da kyau ta fannin zaman takewa. Kai bafa matanka ba kadai mu kanmu haquri muke dakai wani lokacin saboda shi hali zanen dutseaka ce ba’a chanza wa mutum shi amma a wannan karon in har kana so lamuranka su daidaita dole fa seka daidaita sahu a to.

Kai in banda ma halinka Bashir a zamanin nan ka samu mace kamar Asma’u bafa ajinka bace wallahi in ma gaya maka gaskiya Allah ne kawai ya kashe ya baka ka samu tana sonka take hidimta maka da jikinta da Aljihunta, matar nan fa ko daure fuska kayi se hankalinta ya tashi. Ka tashi ka tafka mata kishiya ta wulaqanci koni Namiji naji zafin abinda kayi ballantana ita sannan ka qara mata da tukwuicin saki kai ni idan ta haqura da wuri ta dawo maka gaskiya bata mun daidai ba”.

Daure fuska Bashir yayi tamau yana kallonsa yace
“Karka kuskura kace mun kaima kana son matata dan shine mafi girman kuskuren da zaka aikata, mu kadai ne a gidan nan yanzu zan murqusheka ka mutu Ba wanda yasan meya faru”.

Dariya Musa yayi harda fadowa daga kan kujera kafin yace

“Maida wuqar Malam ashe daba ka fara ban sani ba. Ai ni idan zan so Ma’u bazaka sani ba, qila se kaji nayi aure kawai kazo gidana ka ganta a matsayin matata amma ni sam ba haka nake ba, babu kuma haka a tsakanin mu kawai dai ina nuna maka irin girman asarar daka tafka ne a rayuwarka kuma idan baka hanzarta ba kana ji kana kallo sedai ka mutu kana cizon yatsa da daka sani ka mayar da yayanka marayun dole ka rabasu da uwar su haka kawai”.

Ganin da yayi daga shawara kuma abin na Musa na neman ya koma wulaqanci yasa yayi masa sallama ya kamo hanyar gida, a hanya ya tsaya wani guri da suke siyan Shawarma da wani Gas meat da Ma’u take bala’in so ya siya da yawa ya hado da Madarar ruwa da kwali itama kalar wadda take sha kafin ya kamo hanyar gida.

A qofar gidanta ya ci burki, a waya ya kira Amnah yace tazo ba tareda ya fito ba ya ce ta bude bayan motar ta kwashe ledojin ciki.

Ya dade a mota kafin ya fito qafa daya da takalmi daya babu ya dauki tasa ledar Naman da Madarar ya shige gida, Hajia Addah na zaune a palour ta tasa Amirah data gama zaman dakin ta fito a gaba har sannan dai zancen dubu goma yaqi ci yaqi qarewa.

Kallo daya ya musu sanda Amirah ta masa sannu da zuwa ya wuce daki tabi bayansa, tun dazu take jira ya dawo ita dai ya taimaketa ya biya Addah kudinta kota samu ta shaqi iska a gidan yana shiga dakin kan ya rufo tayi wuf itama ta fada ya kuwa balla mata harara ta sunkuyar da kai se ya wuce ya ajiye ledar hannunsa ya shiga bandaki.

Tana zaune se hadiyar yawu take saboda qamshin naman da duk ya cika dakin ya fito, kamar munafuka tayi qasa dakai tana gaishe shi ya amsa a taqaice yana cire rigar jikinsa ganin taqi fita yace mata

“Lafiya?”
“Am daman Yaya an sallamo mune na kiraka da wayar Addah lokacin baka dauka ba na kira Samuel shima yace mun...”

“Na sani na aike shi ba gashi kun dawo ba se akayi yaya to?” Ya katseta murya a cunkushe, qasan ransa har yana tunanin wane hankali ne yazo mata da har tayi tunanin zuwa ta duba shi kodai Addah ce ta sakata dan yasan a kalar nata tunanin dai bazatayi ba, maganar tace ta katse shi da take cewa

“Daman Taxi muka hawo ta dawo damu, shine seda muka zo yace wai kudin motar dubu Ashirin tunda drop muka dauka to Addah ce ta biya tun safen take ta mun masifa akan na biyata kudinta kuma ni ko sisi bani dashi nayi ta kiranka ma dazun kana rejecting gata can wallahi ko abincin kirki ta hanani naci da masifarta”

Wani mugun kallo me nuna zallar bacin rai yake aika mata, wato kudi take da buqata tun dazun dalilin kiran da ta ringa masa kenan, qonewar da uwarta taja masa ma bata dameta balle taji ya qafarsa kawai kudi ze bata a mugun fusace ya nuna mata qofa ba tareda yayi magana ba.

Amirah dake ta Addu’a a ranta Allah yasa ya bata goman ta ajiye dan tunda tazo sile biyar bata hadasu ba kai ko katin waya bashi ne kusan dubu biyar taci na Mtn saboda ya dena saka mata, da tana Gombe kuwa duk satin Allah yar dubu dayar nan dai seya saka mata wani lokacin ma biyu ga yar cuwa cuwar da takeyi ta karbi kudi a hannun Naziru na cefane anan kuwa shi yake siyo komai kuma se abinda ta gani kawai dan waca wacar nan data san anayi a gidan bata san me yasa yanzu kusan komai a qididdige yake ba ba yanda ta saba ganin sanda Anty tana nan komai na danqare a Freezer ba sedai su bude su diba.

Ita da yake ya raina mata hankali se abinda yaga dama yake siya ya ajiye kuma idan ya qare abinda yake ci ze siyo da wuri, daman nama ne yafi damuwa dashi, tana son kifi amma tunda tayi masa wani farfesun kifi ita kanta dai ranar data ci haka qarnin yayi ta taso mata be sake siyowa ba tayi nacin harta gaji to tunda ta samu ciki ma ya dena cin abincinta, daman yaran ba ci suke ba sedai su dafa abinda suke so ko su shigo dashi daga can gidan sedai tayi ta qara qararta ita kadai ga cikin me dan banzan kwadayi haka zata yita hadiyar yawu idan ta jiyo qamshin abincin makwafta.

Tsawat daya daka mata ce ta dawo da ita daga tunanin data tafi dan ashe yana ta mata magana ma bata ji ba, da sauri ta tattari qafarta tayi waje tana fita suka kusa karo da Addah dake labe a bakin qofa cikin matuqar takaici Amirah ta kalleta kafin ta wuce dakinta wata kwalla na sakko mata.

Bashir kuwa sallah kawai ya tayar dan idan ya tsaya takaicin Amirah yana iya shaqe shi kawai aga ya fadi, so kuma yake yayi isha ya zauna ya tsarawa Ma’u Saqo ya tura mata dan ya qudurce indai soyayya ce matsalar to kuwa ko Sharukan se dai yazo ya kwashi kos a gurinsa a wanna karon.

ASMA’U
Bayan dana dawo daga rabon abinci sallah kawai nayi na kwanta dan na gaji sosai bani na farka ba se dab da magriba. Kiran Yaya Abubakar na gani guda biyu na shiga bandaki na wanko fuskata da bakina kafin na dawo na zauna na danna kiran lambar sa.

Bayan mun gaisa yake cemun
“Dazu Bashir ya kirani a waya wai yana bani haquri, ban san rashin kunyarsa harta kai haka ba se yau tukunna nadai ja masa kunne akan karya kuskura ya sake kirana in ba haka ba yasan sauran”

“Lallai Baban Ali shi har yana da qarfin guiwar kiran ka kenan, haka fa jiya yazo qofar gidan nan wai yana bani haquri harda durqusawarsa” na cikin mamakin tsaurin idon Bashir.

“Asma’u” ya kira sunana da sautin da yake nuna muhimmancin abinda ze gaya mun sena gyara zama dakyau na amsa ina sauraronsa yaci gaba da cewa

“Kafin ki auri Bashir kin taba tambayata abinda yasa bana farin ciki da auran ku ko to yau zan baki amsa. Bashir Abokina ne kin sani tun na yarinta dan haka nasan halinsa ciki da bai, halayyata da tashi sunyi kamanceveniya ta wani bangaren saboda dani dashi murdaddun mutane ne da ake shan wahalar gane gaban mu.

A bangaren auratayya muna da buqatar samun tsayayyar mace me taurin zuciya da ra’ayin riqau ta yanda dole sedai ko mu zubda makaman mu mu bita ko kuma ya zamana anyi 50 50 ma’ana kowa ya riqe bangare daya bawai wadda zamu taka yanda muka ga dama ba kuma ta biyu.
Chapter 127 · 0% Book details