← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 158

Sashe 69

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani lokacin ma har kwana takeyi idan Addah tayi dare bata dawo ba ko Bashir yace ta tafi ta zauna a gun Sauran Matan gidan se nace Yabarta kawai dan har ga Allah ina son yarinyar daman rashin jin ta ne ya ke hadamu nima kuma zuwa yanzu na fara sha’awar ajiye nawa Dan dan duk su Alawiyya sun haihu shekarar mu daya da kusan wata takwas yanzu da aure amma ni shiru.

Akwai ranar da na taba yiwa Bashir maganar nace masa ko zamuje Asibiti yace muna Aa

“Komai lokacine kuma bamuyi dadewar a har zamu ce zamu Asibiti ba, mu qara haquri Allah yasa jinkirin ya zama Alkahiri” ya fada dole na haqura.

Da zaman haka da nakeyi akwai wata makaranta a qasan layin mu nacewa Bashir zan nemi koyarwa acan be hana ni ba kuwa dan da kansa ma yaje ya tambayarmun suka ce naje ai kuwa aka sauke ni zan ringa koyarda yan JS1-3 Computer Science, qarfe 8 nake shiga 12 na gama classes dina in tafi gida kuma sosai nake jin dadin aikina haka yaran suna ganewa dan Allah yayi mun baiwa ta iya magana, sannan yanda nake da Sakin fuska yasa muka saba sosai da dalibaina.

Cikin hukuncin Allah se gashi na samu ciki wanda sam ban san dashi ba seda ya kai kusan wata uku a jikina sannan naje Asibiti saboda rashin ganin Al’adata na tsahon lokaci se gashi gwajin farko an tabbatar mun ina da ciki bayan an yi scanning aka gayamun watanninsa.

Tun ina Asibitin na kira Bashir na gaya masa, sosai kuwa ya nuna murnar sa yace na tafi gida na huta kafin ya dawo haka muka kwana ranar cikin farin ciki kamar mu ciro dan haka muka ringa kallon hoton scanning din da ba ganinsa ake yi sosai bama.

Kamar kuwa cikin nan na jiran a san dashi se Laulayi ya taso ni gab, kuma wani abu safiya nayi idan Bashir ya fita haka zan wuni da zazzabi da ciwon kai amma duk inda La’asar tayi kafin ya shigo gida na ware dan haka ko nayi masa qorafin baya yarda musamman idan ya dawo banyi girki ba ya ringa mita kenan in ce bani da lafiya kuma yace shi be gani ba.

A daidai lokacin kuma Admission dina ya fito, wannan karon na samu daman Business Administration na nema sun bani Level two haka na fara jigilar zuwa makaranta ga ciki ga karatu dan ma farkon semester ne, randa naji ba kanta kwanciyata nakeyi a gida naqi zuwa, haka muka ci rabin zangon, an tafi hutun Midsemeater aka tsunduma yajin aikin da ba qaramin dadi abun ya mun ba na ringa Addua Allah yasa kar a koma sena haihu.

Haka mukayi ta lallabawa, ina rainon cikina, Addah kullum tana tafe da kayan kwalamar da tasan zan so amma fa idan tazo ita ma haka zata koma da niqi niqin tsaraba dan duk abinda idonta ya kai se ta dauka ni kuma bana hanawa sedai Bashir yayi ta fada idan ya gani ko ya tambayi abu nace babu dan yasan ita kadai ce take zuwa ta dauka.

A lokacin su Fainusa sunyi candy dan haka suna zuwar mun sosai wata ran ma ni zan kirasu idan naga kwana biyu basu zoba haka zasu wuni suyi warkaja min su son rai, kayan sawata da duk suka mun kadan saboda ciki haka zan tattara in basu, kayan kwalliya turare duk zuwa da abinda zan basu har seda ta kai ta kawo ko bikin qawaye zasuje gurina za’ayi aron su takalmi, jaka sarqa wani lokacin in suka karba nace su barshi.

Lokaci daya maganar auran qannen Bashir Mata su ukun ta taso. dafarko auran Afiya aka saka, wane tudu wane gangare se ji nayi a bakin Addah wai ai gaba dayansu za’a hada”.

“Ni nacewa Nafi a hada yaran nan dukka kawai lokaci daya a huta to me za’a jira tunda duk da tsayayyun maneman su gasu da garin jiki ai bata jerasu a gaba su zamar mata kamar wasu kishiyoyi ba.
Tana wani ya za’ayi hidima zatayi yawa bayan ga Bashir Allah ya rufa masa asiri aikin Banki fa yakeyi har a tsaya ana wani zancen kudi” Addahn take gaya mun.

Niko banda “Allah ya sanya Alkahiri” ban ce mata komai ba dan mamaki take bani yanda take ji da aikin Bankin nan na Bashir seka rantse wani babban Manaja ne a CBN idan ba haka ba ta yaya za’a tattago auran yaya mata har uku kuma a dan qurarren lokaci kwata kwata wata hudu fa suka saka rana. Ai ko bashi da nasa hidindumun a bashi isashshen lokaci ya shirya balle ga hidimar haihuwa a gabansa dan kusan lokaci daya bikin ze kama da haihuwata.

Haka Bashir ya ringa mita kullum ya zauna saurin me akeyi da za’ace su uku za’a hada ina laifin Afiya da Sadiya dan duka duka Fainusa bata cike sha shida ba kawai girman jikine yasa aka mata tsallake a makaranta suka gama tareda Sadiyan.

Haka naci gaba da rainon ciki na a can kuma suna ta shirin biki, Alhajin su yayi iya qoqarin sa ya bada kudin gadajen Amaren kowa daya harda katifa dan shi kansa ba’a san ransa aka saka auran duka ba amma bala’in nacin Addah da har ta zuge Dadan itama ta hau ta zauna dole yasa musu ido sannan ya kira Bashir ya gaya masa karya kuskura ya takura kansa su saka shi yin hidimar data fi qarfinsa akai kowacce da abinda Allah ya hore tunda sun nace se anyi.

Dan haka gaba daya dan Albashin nasa da duk wani saving dinsa ya basu akayi musu kujeru gudummawar da aka samu daga sauran yan uwa da abokan arziqi suka harhada aka yi abunda ya samu.

Ido kawai na zubawa Bashir ganin har cikina ya kusa fita daga wata na takwas amma ko pant din jariri be siyo ba ko ya bani kudi yace na siya se hidimar auran qannensa yake yi. Raina ya sosu da abin har na kasa haqura wata rana nayi masa magana se ce mun yayi

“Ma’u kenan saurin me kike yi ki bari a haihu mana ko bakiga hidimar data ke a gaba na bane duk qoqarin da nayi kina kallo kullum da sabon abunda zasu ce akai ni gaba daya ma na gaji Allah Allah nake ayi bikin nan kowa ya huta”.

Sosai naji zafin maganar sa a lokacin, cikin bacin rai nace masa “Amma shima wannan abu me muhimmanci ne kuma kasan dai kaine meyi sannan ba yau kasan ina da ciki zan haihu ba tun ma kafin maganar bikin ta taso cikin ne a gaba yanzu kake cewa a bari a haihu tukunna cikin da ko a yanzu za a iya haife shi amma ko rigar da za’a saka masa bamu tana da ba ai shikenan” na tashi na bar masa gurin.

Nakuma qudurce a raina bazan sake masa magana ba dan daman tuni na sissiyi wasu wasu kaya unisex dana gani suka mun kyau se kawai na hada akwatina ta zuwa Asibiti na jingine in yaso naga iya gudun ruwan Bashir.

Wannan Abun yasa gudummawar danayi niyyar bayarwa ma na maida abata tunda a take takensa nasan ba abin arziqi zeyi mun idan na haihu ba nayi amfani da kudin na toshe wata kafar, Addah tayi shaguben harta gaji akan biki nata matsowa wai matar babban Yaya bance komai ba, ai ni ma ina da wayona ni na iya bauta musu amma abinda yake doke ayi mun saboda tasu buqatar tafi tawa ana nema a tauye ni sannan na kwashi gudummawa na bayar lallai ma se kawai nayi dariya nace mata

“Ai babban yayan ya wakilce ni yayi komai sedai mu jira Allah ya kaimu musha biki”.

Ana saura sati daya bikin Matan gidan nu suka aika wa Dadan da saitin Kuloli manya guda uku, a ranar ta kirani a wata tana ta godiya wai an kawo kula masu kyau da tsada daman suna ta yanda za’ayi a qara musu duk wanda suka siya ba wasu na arziqi bane yanzu gashi an samu sun gode sosai.

Haka kawai kuma se naji nauyin qin bayar da komai din da nayi, dan haka washe gari naje Awo da yake da mota na fita dan Asabar ce Bashir yana gida sena Biya na siyi wasu kulolij masu kyau guda uku da zannuwan gado manya masu abun rufa suka uku na wuce gidan Dadan na kai mata.

Taringa zubamun godiya amma qiriqiri Addah dana tarar ta nuna sunyi kadan, har tana cewa “Yanzu a matsayin ki guda a nuna wadannan kayan ace ke kika kawo ai se a raina ki ni dana ga wadanda akace an kawo daga gidan ku inji su hudun duka se naji wani iri nida na dauka mota za’a sauke mana” da wasa da dariya tayi maganar amma duk me hankali ai yasan me take nufi. Dan haka nima cikin wasan na mayar mata da martani nace

“Yo Addah kin manta ance taqamar mace gidan mijinta kudin uba ai ado ne kawai, kuma a iya qarfin mijina nayi wannan ai kuwa na kai a yabamun su kuwa da suka bayar fa kara suka mun bawai dole ya zamar musu fa se sunyi ba”

Washe garin ranar muka tashi da Alhinin Rasuwar Aliyu Abokin su Bashir, mutuwar ta dake ni kwarai dan A jiya bayan na dawo a gidan na tarar dasu shi da Bashir harda Bala suna hira, yana ta tsokana ta wai bana jin nauyin jikina nake iya tuqi nace masa ai Laifin abokinsa ne da be kai ni ba, na wuce ciki na barsu yana ta faman yi mun Addu’ar sauka lafiya ashe rabuwar kenan da safe se kiran Bashir akayi wai ya rasu da Asuba anji shi shiru be fita Masallaci ba Qaninsa ya duba shi aka tarar babu rai.

Mutuwar Matashi akwai firgitarwa musamman ta mutun irin Aliyu me mutunchi da mutunta Jama’a ya samu shaida ta kwarai sosai, haka muka tafi Jana’iza Allah sarki Mamansa se Kuka takeyi su biyu ne Yayanta daga shi se qaninsa haka budurwar da ze aura da suka zo Abin tausayi gaba daya se jikina ya sake yin sanyi da lamarin duniya.
Chapter 69 · 0% Book details