← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 158

Sashe 96

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

MAGANIN BREAST WANDA ZAICIKO MAKI DA TUWON NONO DAN ALLAH KIJARABA ZAKIZO KINA GODIYA DAN DUK WADDA TA GWADA SAITA DAWO MANYAN MATA SUKE GYARA KAMAR YANDA KUKASANI 8K YAKE ZANKARA TALLATA MAKU SHI KI BIYA 4K KI MALLAKI NAKI
KI BIYA TA WANNAN ACCOUNT DIN KITURA MAN SHAIDAR BIYA
3968303018
ZAINAB SHU AIBU
FCMB
08162859027🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 46

ASMA’U
Bacci nasha sosai abuna se Asuba na farka zuciyata wasai kamar wadda aka daukewa wani nauyi daga kanta. Yanzu babu wani sauran abu a tsakanina da Bashir, aure dai ya qare shima kuma yasan da hakan sedai muyi Addu’ar Allah yasa hakan shi yafi mana Alkahiri gaba daya.

Muna cikin karyawa da yara da tun sassafe suka zo Abokin aikina Prince Yemi ya korani, shaf na manta da yau zamuje gurin wasu mutane ne da muke nema su saka saka hannun jari a kamfanin mu seda ya kirani yake tambayar na shirya tunda wucewa zamuyi base mun biya ta office ba.

Mota ta jiya can na barota dan haka nace masa dan Allah ya biyo ya dauke ni kawai tunda muna ta Area daya ba a wani dade ba kuwa se gashi yazo.

Haka kawai ranar naji ina son yin kwalliya, kodan yanzu na tabbatar da bani da wata igiya akaina ne oho.
Straight gown na saka ta Atamfa blue datayi bala’in bin jikina amma bata kamani ba nayi dauri na a gaban goshi na yafa shantili yellow daya dace da Atamfar na kawo baqin takalmi hill da yar jaka itama baqa na saka, nayi kyau kwarai kamar wata yar late twenties idan ka ganni bazaka ce na ajiye tarin yaran da suke gabana ba.

Tare muka fito da yaran dukka sanda Yemi yazo dan nasan duk inda Bashir yake yanzu ya yi shirin fita shima. Dukda qasan zuciyata se naji kamar be dace yau ma ya sake ganina tareda wani ba amma babu yanda zanyi haka na fito, Yemi yana da faran faran da kuma tsokana, yana ganina nan da nan ya shiga tsokanata wai nayi kama da sarauniya, ya karbi jakar hannuna harda bude mun qofar mota na shiga Yara natayi mana dariyar ganin yanda abinda Yemin yakeyi, to su ina ruwansu basu dauki hakan da wani abu ba ko dan wai ace ina da aure be kamata yayi mun haka ba.

Ina kallon yanda Bashir ya bimu da kallo da yanda ya zaburo mota yabi bayan mu sedai Alah yasa tundaga gate din Estate muka rabu kowa ya kama hanyar sa. Muna tafe muna tattauna abinda zamujeyi lokacin, seda muka sake biyawa ta gidan Olivia muka dauketa tana ganina se wani washe baki takeyi ni kuwa daga gaisuwa ban sake kulata ba muka ci gaba da tattaunawar mu da Yemi.

Mun isa Guest house din mutumin da zamu je yiwa tallan, tun daga Bakin qofa zaka san me gurin ya ci ya tada kai. Harabar gidan kanta cike take da motoci na alfarma kana ganinsu kasan ba hawan su akeyi ba kawai dai an siya an ajiye saboda an rasa abinda za’ayi da kudin haka aka shigar damu wani palour me kama da reception muka zauna muna rarraba Ido dan gaba dayan mu wasu qauyawa muka zama da ganin Aljannar duniya.

Olivia kuwa da Patrick da muka tarar a can Selfie suka shiga dauka abinsu nida Yemi ne wai mukan dan kame kan mu muna kallon gurin seda muka kwashe awa biyu cif muna jira kafin aka yi mana iso gurin mutumin.

Wato wata hadaddiyar daula muka sake tararwa, palour ne qaton gaske na alfarma da fadarsa ma bata bakine kaini fitulun da aka saka ma kadai sun ishe ni kallo wallahi haka muka nemi kujeru muka zazzauna su kansu irin na yan gayun nan ne harda wani guri da ake dannan wa su koma gado ga abin tausa kai masu kudi dai sunji dadi abinsu.

Anan ma seda muka sake jiran kusan minti Ashirin har seda muka fara qosawa sannan mamallakin gidan ya fito, Farine sosai dan tsurut dashi dagani ya hada jini da fulani seka rantse dan aiki ne, badan hotonsa da yake a palour ba da bazan yarda gurinsa muka zo ba.

Cikin girmamawa muka gaishe ni ina ta mamakin wai yanzu duk wannan uwar daular ta wannan dan firit din mutumin ce, yana nan lange lange kamar baya cin abinci se kudi kamar zasu kashe ni.

Nice me bayani, haka na dage na ringa watsa masa bayanai akan muhimmancin saka hannun jarin da zeyi da kuma ribar da ze samu akan hakan, na gama bayani na tsaf yana ji se gyada kai yake kamar qadangare yana kallona, seda na qare tas na zauna Yemi ya dora da nasa se mutumin nan jin mu kawai yakeyi bece komai ba.

Gaba daya se jikin mu yayi sanyi, sosai kamfani yake da buqatarsa mun kuma saka rai da samun nasa amma da alama bayanan namu basu shige shi ba tunda gashi ya mana shiru, haka muka fara tattare takaddun mu kowa fuskarsa ta chanza yanayi, wayarsa ya dauka yayi kira ko minti biyar ba’ayi ba sega wnai mutum ya shigo daganinsa kaga Lawyer.

“Kuje dasu ayi ku kammala deal din a zuba ko nawa suka buqata babu matsala” mutumin ya fada har sannan idonsa akaina, ai kamar zamu taka rawar murna haka muka shiga zuba masa godiya yanda kasan wadanda yayiwa wata gagarumar kyauta ko da yake kyautar ya mana dan Allah kadai yasan kudin da zamu zamu akan qulla yarjejeniyar nan.

Muna shirin tafiya ya tsayar damu, PA dinsa ya kira se gashi shima da jaka ya ajiye a gabansa, da ido ya nunawa PA ya budeta se gani mukayi yana zaro rafofin daloli ya miqawa ko wannenmu daya sannan ya sake dauko complement card aka bani se kawai na karba ina juyashi a hannuna dan basan me zanyi dashi haka dai mukayi sallama muka tafi tareda Lawyer muka wuce kamfani.

Ranar cikin farin ciki na dawo gida jakata cike da daloli, a hanya na tsaya wani shopping mall na siyawa yara kaya kowa set biyu designers masu kyau nima se gani ina lissafi da dollar irin na yan gayu, seda na gama diban kayan idona ya sauka akan wasu singlet da boxers na maza, har na kai hannu na dakata zuciyata na tambayata

“Wa zaki daukarwa?”
“Allah sarki Baban Ali, da yanzu harda kai za’aci kudin nan” na fada a fili ina wucewa bangaren turaruka na dibi wanda nake amfani dasu sannan na quce gurin takalma na daukarwa Amnah wani me shegen kyau da zata hada da gown din prom din su da za’ayi wannan Juma’ar me zuwa.

Sosai na kashe kudi, niqi niqi na wuce gida da kaya ina zuwa na tarar da yaran duka suna nan muka shiga dasu ciki, plates din Abinci dana gani ya sakani cikin sigar wasa nace

“Wai ku baku iya zama a gidan mu sedai kuzo nan ku cinye mana abinci kullum toh gaskiya ya isheku haka kun mayar da Yah Amnah kuku meye amfanin Antyn ku da bazata girka muku ba”.

“Tab ai wallahi Mami bata da amfani kuwa, ni tausayin Abbi ma nakeyi kar ulcer ta kamashi dan rabon danaga yaci abinci a gidan nan tun kina nan fa” Jafar ya fada yana zaro kayan cikin ledar, ban tankashi ba, na bisu da kallo yanda suka rude suna murna kowa yana daga kayan sa se kawai na shige dakina na barsu.

A gefen gado na zauna ina tunanin meyasa Amirah bata girki? Su yara basu da matsala tunda gashi suna ci a nan amma Bashir fa me yake ci shi da sam bashida jumurin yunwa
“Ina ruwanki idan ma ruwa yake sha” zuciyata ta rayamun, sena miqe ina qoqarin cire rigata wayata dake cikin jaka ta hau qara.

Cirota nayi na duba, Number ce wata irin special Number kamar me ita ne ya zabi abarsa dakansa na dubata dakyau batayi mun kama da wadda na sani ba dan haka na mayar da wayar na ajiye dan ban fita daukar wayar da ban sani ba.

Message ne ya shigo bayan data katse an rubuta “ki daga wayar, wanda kukayi yarjejeniyar kasuwanci ne” se nayi saurin nemo Number zan kira dan a zatona Barrister dazu ne a raina ina Allah yasa ba wata matsala bace ta faru kuma dan har an karbi account Number mu a kamfani za’a saka mana kudin aikin mu na kuma gama lissafin kudin sabuwar motata zan cika dasu yanzu idan aka fasa ai mun ga bonu.

Kiran daya sake shigowa ne yasa na dakata, na daga tareda yin sallama.
Seda akaja aji kafin wanda ya kira yayi magana cikin harshen hausa yace
“Meyasa baki kira ba tun bayan da muka baki kati dazu”.

Wayar na cire daga kunnena na sake dubawa, number ce idan kuma banyi qarya ba kamar wannan dan tsamurmurin mutumin da mukaje gurinsa dazu sena mayar da wayar kunnena, cikin dari dari nace

“Bangane wa yake magana ba”.

“Oh babu laifi, sunana Ambassador Mutallab Ali” ya fada

Seda na zauna akan gadona na qara riqe wayar dakyau kafin nace

“Ranka ya dade barka da dare, ina fatan dai ba wata matsala aka samu da takaddun da muka bayar ba?”

“Aa, idan da harkar data shafi aikice ko kudi wasu ne daban suke gudanar mun da ita, wannan kuwa abune daya shafe ni ya shafi rayuwata dan haka ni da kaina zanyi shi. Ba tareda bata lokaci ba tun zuwan da kukayi dazu na ganki kuma kinyi mun a matsayin matar aure, idan kin aminci ina so na cike mata ta hudu dake amma dukka matana ba tare suke ba, kowaccen su qasar da take zama ta banbanta data yar uwarta dan haka kema zaki zbai inda kike so ki zauna ne ni bani da damuwa da hakan”.

“Ikon Allah se kallo” na fada a zuciyata, a fili kuma sena samu kaina da cewa
“Ranka ya dade kayi haquri amma ni matar aurece”.
Chapter 96 · 0% Book details