← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 158

Sashe 13

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna gama cin abincin dakin suka koma, ta gaji tibis dan haka ta haye gado ta kwanta yana matsa mata jikinta. Wayarsa ce tayi qara, a tare suka duba sunan Amira da ta gani yana yawo yasa ta dauke kanta. Satar kallonta yayi karaf kuwa suka hada ido, haka kawai yaji wani abu kamar nauyin Asma’u ya kamashi cikin son basar wa ya dauke idonsa ba tareda ya amsa wayar ba.

Kiran da ya yanke wani ya sake shigowa ya sakata cewa “ka daga mana ba kiranka akeyi ba” seya dauki wayar, be zauna anan ba ya fita falo. Da kallo ta bishi tana qoqarin hana shedan yin tasiri akanta “Itama matarsa ce matsayinmu daya da ita” ta fadawa kanta sejin hawaye kawai tayi suna bin fuskarta.

Bata san randa zata dena jin zafin yankan bayan da suka mata ba. Da ace wata can Bashir ya aura koda cikin dangin nasa ne damuwarta bazata kai haka ba amma fa Amirah, Amirah data dauka tamkar Amna. Yarinyar da ta gama sanin sirrinta ciki da waje ita ya auro mata a matsayin kishiya se kawai ta rushe da kukan takaicin da duk sanda ta tuna yanda auran Bashir ya kasance seta yi shi.

Babu wanda ze gane zafin da takeji se wadda aka kwatantawa irin abinda akai mata, se yanzu take ganin dalilin da yake saka wasu matan aikata abubuwa da dama akan kishiya ko ma mijin kansa dan wallahi in akayi maka wani abun in ba me qarfin imani da tawallaki ba se kaji kamar bazaka yarda ba se ka dauki mataki. Har bacci ya dauketa Bashir be shigo ba se Asuba ta farka ta ganshi a bayanta.

Ko a fuska bata nuna masa komai tayi sallah a dakin sannan ta fita gurin yara dan jiya basu samu ko yin magana ba. Seda ta hada musu abinci suka shirya tareda zama suka fara breakfast sannan ta koma dakin ganin Baban Ali be fito ba.

A tsaye ta ganshi yana zuge jakar da yake tafiya da ita Gombe, dauke kanta tayi kamar bata gani ba tana cewa”Sun shirya fa gasu can sun fara cin abinci basu jiraka ba” tayi gaba da niyyar shigewa toilet dan bata so yai mata maganar tafiyar sa sedai tun kafin ta shiga ta jiyo shi yana cewa

“Ke zaki dauko su daga school yau zan wuce Gombe ne daga office bazan dawo ta nan ba” ba tareda ta juyo ba tace masa “Allah ya tsare ka gaishe su” tai shigewarta abinta.
Bin kofar yayi da kallo kafin jiki a sanyaye ya dauki Laptop bag dinsa da jakar kayan ya fita, seda ya kaisu mota sannan ya dawo shima ya hau Dining din amma se ya kasa taba komai.

Shiru yayi yana kallon yaran suna cin abincinsu har suka gama Ahmad ya kalleshi yace “Abbi ina Mami zamu tafi”
“Kuje mu tafi wanka take yi” ya fada yana miqewa. Har sun fita ya juyo zuwa cikin gidan, Bayaso su rabu da bacin rai kodan albarkacin farin cikin data bashi a kwana biyun nan. Harya kama Handle din dakin shegiyar zuciyar da take masa famfo ta zugo shi “to me kayi da zaka ke bata haquri ma?” Zuciyar ta raya masa, Seya saki qofar ya juya kawai.

Asma’u da ke zaune tana jiran tsammanin zuwan Bashir ya rarrasheta, ajiyar zuciya ta sauke jin an taba qofa harda qara narke fuska tana ayyana abinda zatayi ta gigitashi se taji shiru, the next thing ko se jin tashin motarsa tayi ta yaye window da sauri har sun wuce se qurar daya tayar, baki bude take kallon motar harya qule mata, “Hmmm” ta sauke numfashi kawai ta shiga shafa mai, bataso ta tuna abun ma bare ranta ya baci ita dai addu’arta idan Bashir nada rabon ganewa to Allah ya maido shi kan hanya.

Gombe gidan Addah
A daren ranar da Bashir ya turo musu da kudi tayi ta kiran Number da Malam Wizy ya basu bata samu ba, bata haqura ba tayita gwada Number har washe gari amma shiru gashi ta kira wayar Hajia Balaraba ma a kashe.

Jikinta dabe gama warwarewa bane ya hanata fita ta bari akan zuwa talata tasan ta warke seta je gidan Hajia Balaraban ta dai ci gaba da kiran wayar tasa ko zata samu cikin Sa’a kuwa ranar Laraba da safe tana kira ta shiga.

Ta gama ringing ba’a dauka ba seda ta sake kira aka daga. Muryar wata tsohuwa taji daga ji taji duniya har ta gaji tana cewa “kai ku duba nan waye ya bugo, Wizy da qaninsa Iliya suna zaune a dakin Kakarsu daidai lokacin sunzo gaishe ta, miqa wa Wizy wayar tsohuwa tayi tana sake cewa ya duba ga gani.

Sallama Adda ta sakeyi, fes Wizy ya gane muryarta se yai saurin datse kiran ya miqe yana cewa Kaka yana zuwa.

Can wani lungu ya buya yayi recharging wayar kaka ya dannanwa Adda kira.

“Salamu alaikum malam ina wuni” ta fada cike da zumudi
“Lafiya lau dawa nake magana” ya tambaya irin be gane ta din nan ba
“Nice Malam wadda Sani ya kawo mu (sunan da Me Napep ya gaya musu kenan)
“To to hajia ya gida naji ki shiru da alama buqata ta fara biya kenan”
“Wallahi malam na danyi rashin lafiya ne kwana biyu kuma na kikkiraka ma wayar a kashe” Addah ta fada

“Eh wallahi kwana biyu kam na kashe waya dan na shiga halwa ne inata ayyukan ku dafatan ana ganin haske ko”

“Sosai kuwa Malam ya fara samuwa”
“To haka ake so yanzu to ya akayi?” Ya sake tambayarta.

“Dama na samu wasu kudin ne nace bari na turo a ci gaba da aikin mu sameshi gaba daya”

“Kin kyauta kuwa ai ina tabbatar miki idan aiki ya kammala hajia nasan indai kin riqe amana har ni dinnan se kin mun kyautar kujerar hajji” Wizy ya fada yana tsallen murna jin wata banzar zata fado.

“Insha Allahu kuwa malam yanzu dai ka bada akawun a tura kudin nan ayi a ci gaba”

“Ba matsala da mun aje waya zan turo miki” sukayi sallama yana qara karanta mata qanzon kurege.

Harya fara typing account details dinsa wani tunani ya kawo kansa, idan ta tashi fa za’a Iya tracing dinsa ta banki, se yai saurin gogewa ya danna mata kira. Tana dagawa yace

“Hajia nace kudinnan ki cire su, akwai yaro da na aika qauye ya siyo ragunan wasu aiki bari naji in be tafi ba se ya biyo ya karba kawai ya wuce” da haka sukayi sallama.

Minti kadan ya sake kiranta yace ze turo yaro, nan ta zayyana masa Address ashe ma basu da nisa ya ma gane gidan daya daga cikin yaran mijinta abokinsa ne. Isma’il me Napep ya dannawa waya suka tafi tareda wani qaninsa me suna Nasiru da yai shigar me zuwa kasuwar qauye. Ko kafin su Iso Adda ta aika Ummi an ciro mata 80k kudin rago biyu yaro na zuwa ya shiga har palour ta ta bashi kudi ya jefa a buhu ya fice.

Gaba suka qara aka tsaya kowa aka bashi rabonsa ya zuba a Aljihu Malam Wizy ya zare sim din Kaka ya ballashi biyu ya zubar yana cewa “mun tatseta ya isa haka” suka sheqe da dariya.

To Addah Allah ya maida Alkahiri ya kiyaye na gaba 🤷🏽‍♀️🤷🏽‍♀️🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(Alkhairi CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 9

Gombe
Ana kiran magriba Bashir ya shiga gidan sa na Gombe, tun qarfe hudu da rabi suka sauka tazarar tafiyar daga Akko zuwa Gombe ta kaishi Magriba.
A qofar gidansa Me Taxi din daya dauko shata daga Airport ya sauke shi ya fito dakyar yana jan qafa ga yunwa ga gajia tiqis saboda yau yasha aiki a office ga kuma tafiya dukda a jirgine.

Yana qoqarin bude get din a ransa yana ayya Allah yasa ma ta dawo gidan dan yana daga ciki rashin sanin ya kamatan Amirah a duk sanda zezo hankalin ta be taba gaya mata tazo ta gyara gida tayi girki dan tarbarsa ba se in ya tuna mata. Dama can tun tana yarinya yasan qazama ce ta gaske daga baya ne zama da Asma’u ya sa tadan chanza tareda koyar wasu abubuwan amma dukda haka tsaftar biri gareta. Zata yi wanka ta gyara jiki amma fa duk dattin guri haka zatayi zamanta.

Yana jefa qafa busassun ganyayen bishiyar da suka zube ne suka masa Maraba. Compound din ya hada uwar qura dama ga shi an fara Sanyi da Hazo a garin. Takaici ya qume shi danya tabbata bata dawo ba kenan.

Bangaren Asma’u ya nufa dan yasan yace zeje dakinsa na part din Amiran ma ransa ne ze qara baci. Seda ya kunna wutar bangaren sannan ya bude palour ya shiga da Bismillah. Komai na nan a kintse yanda ta barshi, cike da gajiya yake daga qafafunsa ya haye benen da ze kaishi dakinsa. Nan dinma fes dashi ya saka hannu ya yaye ledar da take shimfidawa akan Katifa bayan ta cire bedsheets din saboda qura sannan ya zube kayan daya shigo dasu.

Toilet ya fada ya dan daurayeshi yayi wanka tareda dauro Alwala ya fito. Harya idar da sallah beji alamar waniya shigo gidan ba ransa ya qara baci amma seya danne kawai ya janyo wayarsa ya kira Qaninsa Naziru ya kawo masa motarsa dayake amfani da ita anan. Bayan ya kashe se yayi dialing number Asma’u, deep down yanajin kaman dazu da safe be kyauta mata ba.

Har wayar ta qaraci ringing dinta bata daga ba, ya sake kira nan ma shiru se ya maida akalar kiran zuwa ga Amirah dan yaga alamar hankalinta ragaggene. Ai a qalla yaci ta kira taji yazo ko kuwa tunda tasan da zuwan nasa yau amma still itama bata dauki wayar ba.

Ajiye wayar yayi a kan gado cikinsa na cigaba da qugin yunwa shikadai se sakin qwafa yakeyi da ayyana hukuncin da ze dauka akan Amirah. Kusan minti 20 Naziru ya kirashi ya iso, se ya dauki wallet dinsa da keys ya saka a Aljihu ya fita. Naziru na ganin sa ya fito daga motar da niyyar bude get ya shigar masa da ita Bashir din ya dakatar dashi da cewa
Chapter 13 · 0% Book details