Sashe 39
Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Ya zama kuskure na qarshe da zakiyi tunaninyi ki sake dora hannunki a kan yarinyar nan, da kina sonta kika jawo mata ciwo sannan tunda aka fita da ita daga gidan kin tambayi yanda take bare kije ki ganta? Idan ke bakya qaunarta ni inasonta dan haka nayi miki iyaka da ita kota warke bazan dawo miki da ita ba tunda bake kadai bace zan kaiwa wadda zata kular mun da ita” yana gamawa yasa kai ya fice ya barta tana rusa kuka.
Abinda baze ma yiwu ba kenan taya ze raba ta da yarta ce masa akayi bata sonta? Ai tasan tana Asibiti kuma a kwanakin in ma tace zataje ba bari ta zeyi ba shi yasa amma wallahi bazata yarda ba dole ma ya barta ta fita kai ita bama zata iya zama a gidannan ba sedai ta tafi gidansu, ta yarda acan din bazata fita ko ina din ba amma badai a nan ba.
Tana son magana da Addah amma babu hali, ita ba waya Addah ma haka dukda da tana da wayar samun Addah bazeyi wahala ba ko a wayar Ummi ne. Tunda suka rabu a gidan Dada basu sake magana ba bata san yaya Addah ta qare a nata gidan ba tilas kuwa tana buqatar magana da ita, ya dai tafin ko Nazirun in yazo anjima ta roqeshi ya siyo mata ko Key pad ce a cikin kudin da Bashir din ya bar mata.
GIDAN ADDAH
Ranar bayan Addah ta bar gidan su Bashir Napep ta hau ya kaita gidanta. Alhaji Murtala na tsaye a qofar gidan da wasu mutane su biyu Addah ta sallami me Napep zata shige ya dakatar da ita.
“Yawwa ga Hajia Fatun ma ta dawo” ya fada yana nuna musu ita. Se Addah taci burki ta bisu da kallo daya da daya amma bata ga fuskar data sani ba dan haka se ta saka kai ciki kamar bataji maganar da Alhajin yayi ba harta tura get ya dakatar da ita dacewa
“Wallahi kika shiga gidannan se ranki yayi mummunan baci Fatu” Alhajin ya fada cikin kakkausar murya. Se Addah taja da baya jiki a sanyaye, to su waye wadannan kuma? Wane jafa’in ne ya sameta.
Takadda daya daga cikinsu ya miqo mata yana cewa “Hajia gashi sammacine daga kotu ana qararki akan laifin damfara”.
“Damfara?” Addah ta fada da qarfi tana dafe qirji tareda zaro idanu waje
“Ni Fatu wana damfara?” Ta sake tambayarsu hankalinta in yayi dubu ya tashi.
“Akwai bayanin komai a ciki idan kunje kotu zakiji cikakken bayani kafin sannan kina iya neman lauya da ze tsaya miki” dayan mutumin ya fada, sallama sukayiwa Alhaji kafin suka hau mashin din da suka zo suka bar Gurin.
Addah data gama jiqewa da zufar tashin hankali ce ta kalli Alhaji Murtala da yake jifanta da wani irin kallo data fassara dana tsana da takaici yace “Daman na fada miki Fatu tun kina dauko magana kina cin riba wata rana se kin dakko ta wanda yafi qarfin ki.
Se kije ki san yanda zaki kare kanki ko kuma ki fara shirye shiryen tafiya gidan prison tunda halinki yaja miki” yana gama fada ya shige cikin gida Addah ta rufa masa baya tana kuka kamar yarinya.
Bata tsaya ba har cikin uwar dakinsa inda ya shiga, Hajia Binta yar tsakiyarsu na cikin Toilet tana wankewa taji shigowarsu da kukan Addah seta leqo tana cewa “Aa Alhaji lafiya waye yake kuka... Au Addah kece lafiya dai waye ya mutu?”
“Kiga mutuwa akanki munafuka kuma duk sharrin da kuka kitsa masa sedai ya koma kanku” Addah ta fada cikin hargagi, dariya Hajia Binta tayi harda tafawa tana cewa “Ikon Allah se kallo, da alama dai bana an kwaso me zafi”
“Fita ki bamu wuri” Alhaji ya katseta, seta hade fuska tana cewa “kamar yaya Alhaji in baku guri bayan ni nake da aiki ko Alfarma za’a nema ai ba ta haka za a zomun ba” kafin yayi Magana Addah ta tareshi da cewa
“Alhaji muje gurina Dan girman Allah”. Shiru yayi kamar baze amsa ba se kuma ya miqe yayi waje ta bishi a baya yana jin Hajia Binta na fadar maganganun an shiga haqqinta dan ba haka taso ba, dayace ta fita zata fitan in yaso ta labe inda zata ji kan zancen tas gashi yanzu ta jashi dakinta.
Addah kuwa tiryan tiryan ta labartawa Alhajin duk abinda ya faru da basussukan jama’ar data ci da yanda sarqar Hajia me Gwal ta salwanta dama yanda suka rabu yanzu ga zancen sammaci”.
Takaici ya gama qume shi, shidai Fatu qaddarar sa ce amma ba komai lokaci yayi daya kamata yayi maganinta ko yaya me taji a jikinta amma yanzu bari a gama wannan case din tukunna.
“Wanda yaja ruwa ai shi ruwa ze doka, takaddun gidan original suna hannuna gobe se muje gidan matar aje da Dillalai suyi masa kudi a siyar a biya kowa kudinsa, Allah ya tsare gaba idan zaki gyaru” ya tashi ya fice ya barta tana ajiyar zuciya dan bata zaci abubuwan zasu zo da sauqi haka ba. Ita yanzu koma menen ai a siyar a biya wannan jarababbiyar matar, ita da tunda Allah ya halicceta ko Police station bata taba zuwa bare a ganta a gaban Alqali gara komeye a siyar a bata kudin su rabu lafiya. Da wannan ta samu sa’idah har ta iya kwantawa tayi baccin gajiyar da batayi ba.
ASMA’U
Gaba daya sukuku mukayi tafiyar babu wani kuzari har muka sauka Ikko, a Airpot din muka rabu Drivern Bashir ya kwashe mu shi kuma ya dauki Shatar Taxi ya wuce office daga nan. Yanda nayi tsammani gida na nan ya hada kari, bamu ko zauna ba na rabawa ko wa aikin da zeyi, Ahmad da Muhammad da suka fara mun rigimar wai Yunwa dukda munsha Tea kafin mu taho ga Cake da sukaci a jirgi se na turasu gidan Anty suna fita kuwa se gasu sun dawo wai Aliyu da Jafar suje inji Anty, Breakfast ne data shirya mana ta basu wanda ya zamar mata kamar dole duk sanda mukayi tafiya irin haka bata gajiya seta kawo mana.
Nan da nan kafin wani lokaci mun qalqale ko ina har kayan da muka dawo dasu kowa ya jere nasa na amfani kuma an adana su a inda ya kamata.
Bayan Azahar Muna zaune muna huce Gajiya Anty ta shigo su Ahmad na binta a baya da kulolin Abinci, bata gaji ba wai abincin rana ta kuma kawo mana, matar dai tana da kirki kwarai nayi sa’ar maqociya.
Kan Dining suka koma Amna ta zubo nawa ta kawo mun cikin palour ina ci muna hira da Anty suna gamawa kuwa duk suka shige daki wai bacci se Anty ta miqe tana cewa bari ta barni nima na huta. Tsarabar Kindirmo me kyau da Dambun fura se Kuka da kayan qamshi na dakko mata daman na ware su daban na hada mata da wani turaren wuta da Alawiyya yayata take hadawa ta bani yana da kyau sosai mukayi sallama ta wuce gida.
Na raka ta kenan David yaron da Bashir yake aikowa wani lokacin ya kawo saqo ya tsaya a qofar gidan, kayan amfani ya kawo su kayan miya, veggies, Nama, kifi, dankali, doya plantain duka dai kayan amfani da za’a nema ya siyo, qofar kitchen ta baya na bude masa suka shiga da kayan shida me Uber daya kawo shi.
Dole na fasa kwanciyar na shiga ware komai ina saka shi gurinsa kafin na gama har uku tayi dan ban nemo yan tayi ba ganin sun gaji yasa na barsu su huta. Bayan na gama na shiga dakina, zama nayi akan gadon ina miqa Kafin na dan kishingida ina duba waya ganin da sauran kusan 30 mins kafin ayi la’asar yasa na kwanta wai in dan matse ban tashi farkawa ba kuwa se qarfe biyar harda rabi na yamma na miqe ina salati ganin irin baccin da nayi, anyi la’asar tun tuni ga Bashir nasan yana dab da gida yanzu kuma Azumi yake.
Alwala na farayi nayi sallar bayan na idar na shiga wanka. Ban wani jima ba ina fitowa na shafa mai sama sama na goga yar hoda da kwalli se lip balm kafin na fesa turare, doguwar riga na saka ta wani plain material Silk Dark green an masa dinkin kamar Jallabiyar qirar Turkey babu adon komai a jiki se maballai da aka jera a jikin wuta zuwa qirji guda uku da kuma bakin hannu. Mayafin ta na yafa a kaina wanda be kai kalar rigar duhu ba na zura flat shoe baqi na fito da wayata a hannu ina tunanin me zan dora masa mara wahala da zan gama da wuri.
“Mamina” Ahmad ya fada yana rungumeni, se na janye shi gefe ina cewa “Ina zuwa Ahmad Abbi ya kusa dawowa gashi ban masa abin buda baki ba” ai ban qarasa rufe bakina ba naji tsayuwar motar da nake da tabbacin tasa ce a qofar gida. Kitchen din na fada da sauri a rainaina cewa “shikenan yau an bani”dan Bashir baya wasa da abinci. Idan yayi azumi yafison kafin asha ruwa an gama jere masa komai a gabansa yanda bama ze jira komai ba.
Da niyyar dafa masa tea in soya kwai na shiga in yaso kafin yaje sallah ya dawo ko couscous ne na turara masa, nasan dakyar idan yaran nan sun ci farfesun kayan cikin da Anty ta kawo dazun ba tunda ba son shi suke ba se in hada masa ya qarata, mita ce dai nasan sena sha ta yau dan babu ruwansa baze duba irin aikin da muka sha a gidan ko gajia ba tunda kawai nasan yana azumi dole na tanadar masa abincin.
Amna da Farida na tarar Amna na kwashe dankali daga mai Ita kuma Faridan na yanka Fruits a bowl, suka kalleni a tare suna murmushi “Mami kinsha bacci, naga yamma tayi nace bari mu hadawa Abbi kayan shan ruwa” Amna ta fada tana kashe Gas din bayan ta qarasa kwashe dankalin.
“Allah dai yayi muku albarka, na manta shaf ma kuna gida ai” na fada ina qarasawa kan Island inda suka ajiye kwanukan da aka zuzzuba abincin na bude na farkon.