← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 158

Sashe 33

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Wato ni za’ayiwa wasan kwaikwayo kuna tsaye kuma Naga alamar bazakuyi abinda ya dace ba ni bari na shiga dakaina na fito da ita dan wallahi wannan karon Mariya bata isa ba, ta saba salwantar mun da qananan abubuwa ko nata tace an sace to wannan karon bazan dauka ba ina gani ta sabautamun miliyan Ashirin a sama ba taci bulus seta biyani ko mota ta ko kudina fita kuma ba izinina da takeyi taje ita da Allah dan na gaji”. Ya tattare riga ya doshi Gate inspecta na tsayar dashi amma yaqi.

Yana zura qafarsa Amiru na faka mota Suka fito da sauri ganin yan sanda, da sauri Naziru ya qaraso yana tambayarsu lafiya se Alhaji Kabiru ya dakata ya yo baya yana cewa
“Yawwa Samari gidan kune ko? To shiga ka fitomun da Mariya qawar Fatu data zo suna gidannan ka gayamata wallahi idan bata fito ba tunda wadannan dana zo dasu basu da amfani mopol zanje na dakko ai tasan halina”.

Amiru ne ya qaraso gurin shima Ummi daman wucewarta tayi bata ko kallesu ba tayi cikin gida. A taqaice Naziru yayiwa Amiru bayanin abinda ya fahimta cikeda takaici Amirun yacewa Alhaji Kabiru da Inpectta su biyo shi dan abin nasu Addah ya kaishi maqura.

Yanzu haka Iman nacan a NICU sun barota wanda dakyar likitan ya karbeta yace tunda uwarta bata san ciwon kanta ba subarta kawai su koma gida idan ta mutu Allah yasa qarshen wahalar da zata sha kenan dan shidai be taba haduwa da Uwa da Ya marasa tunani irin Addah da Amirah ba, dakyar suka roqeshi suka karbeta yanzu dai sun baro an jona mata oxygen da sauran tarkacen wayoyi sedai su bita da Addu’ar samun lafiya dan su da kansu sun cire rai da yarinyar.

Dirar mikiya sukayiwa Palour Amirah, Hajia Mariya da farfadowarta kenan tayi arangama da Alhaji Kabiru ai take qirjinta ya bada daram dam.

“Gasunan ku duba wadda kuke nema ku tafi dare yayi ya kamata a rufe gida” Amiru ya fada yana qara hade rai. Ba bata lokaci Matan yan sanda sukayi ram da Mariya suka tisa qeyarta akayi waje Alhaji Kabiru na zuba tijara se muce Allah ya bada yanda za’ayi a biya Kabiru kudin motarsa 😂😂😂

suma basu tsaya ba suka fita, a qofar Asma’u ya tsaya ya kira Rahma da harta fara bacci ta fito suka tafi lokacin sha biyu harta gota, a gidan suka bar Naziru ya kwana saboda gudun abunda ka iya faruwa kuma, seda ya duba ko ina kafin ya kulle gidan ya kwanta a dakin Aliyu.

Su Hajia Addah dai kamar masu kwanan keso haka suga safiya ido biyu kowa da abinda ya dameta Asubar fari kuwa wadanda suka kwana suka dade akabar Addah da Amirah se Ummi da itama tace gida zata tafi anjima bazata iya wannan masifa ba kafin takwas na safe kuwa se su biyu kawai ga uban barnar da akayi a dakin sun ma rasa ta ina zasu fara.

Dakin Bashir Amirah ta nufa da niyyar tayi wanka saboda bala’in tsamin da jikinta yai mata kafin su san abinyi sedai ta tarar da qofar a rufe se a sannan ta tuna da Anty Aisha ta bawa key jiya kuma ita bata ma sake ganinta ba gashi babu waya bare ta kirata dole haka ta shiga dakinta ta binciko inda ta boye key din toilet data rufe dan kar a bata cikin Sa’a sega na Dakin Bashir a gurin da alama anan ta boye mata.

Da murnarta ta dauki key din ta fita, Addah na zaune akan kujera ta rafka uban tagumi abin duniya ya taru ya mata yawa dare daya harta zabge tsabar Tashin Hankali yanzun ma tayi zurfi a tunanin yanda zasuyi su gyara gurin kafin azo tunanin neman kudin da za’a biya bashin da suka karbo bata maji fitowar Amirah ba se ihun salatinta data jiyo a dakin Bashir ba shiri ta miqe ta bita.

“Na shiga uku Addah shikenan sun kashe ni wallahi Yaya Inaga yanka ni ne kuma kawai bazeyi ba” Amirah ta fada hannu aka tuni idonta ya fara tsiyayar da hawaye lokacin data ci karo da murfin Wardrobe din Bashir da aka fashe ga kan Mirrow dinsa wayam babu ko kwalli suma an kwashe wai iya abunda idonta ya gani kenan Allah kadai yasan dame dame aka dauka kuma.

Ita kanta Addah seda hankali ta ya qara tashi dan duk a zatonsu tunda qofar na kulle bala’in be taba can ba basusan ta nan Al’amuran suka fara sauka bama 😂

“Dallah can ki mana shiru aikin gama dai ya riga ya gama duk ma abinda za’ayi daga baya ne me afkuwa ta afku ni dai yanzu ciro sarqar nan ki gani mu Adana su kafin suma bala’in ya dirar musu nidai wannan Ya dakika haifa kamar yar Allah bani ta jefa mu a masifa (babu ruwan Iman ku dai kuka jefa kanku uku ah to 😚😚).

Wata sabuwa inji yan caca ai seda Amirah ta shafa wuyanta taji wayam sannan ta ankare babu wannan sarqa dama babu batun awarwaro tun tuni su ta ankare da sun zube amma a sannan bata su takeyi ba, yanda take rarraba ido ne yasa Addah a fusace cewa “bazaki ciro bane kike tsareni da ido ko kuma daman ta kice” ta wara idonta akan Amiran.

“Shikenan ashe ba Mariya kadai ce take da rabon zuwa Birsin ba harda ni wayyo Allah na na shiga uku na lalace wannan wane irin bala’i ne suke bibiyata sahu sahu ni fatu?” Kuka riris Addah takeyi, sarqar da hayota tayi dakyar Hajiya Inna Qawarta tayi mata hanyarta a gurin wata qawarta.

Seda ta bada dubu dari kudin Haya sannan ta bata takaddun gidanta dashi kadaine kadarar datayi mata saura a yanzu akan idan wani abu ya samu sarqarta sedai a siyar ta cire kudinta ta bata chanji to a qalla da sarqar da abin hannu sun kai na kusan miliyan biyu gashi babu ko daya se warin dan kunne daya ne a kunnen Amiran to ita kuwa yau ta shiga ina taga haske wannan Asara kan asara babu biyan buqata?

Rasa me bawa wani haquri akayi cikinsu ita Amirah tana kukan haduwarsu da Bashir ita Addah tana na sarqa seda suka gaji dan kansu sannan sukayi shiru kowa tayi wanka suka shiga gyaran guri kafin kuma su san abinyi a gaba. Tsakar gida suka watso sharar Addah ta fita ta samo yara suka shiga sharar tsakar gida aka tattare kujeru masu lafiya aka ware karyayyu gefe suma kafin masu su suzo ayi lissafi haka suka tattaro kwanuka da kulolin abinci suka bayar yaran suka wanke komai bayan yaran sun gama ta biyasu suka koma ciki sukayi zugun zugun.

Babu wanda yayi tunanin zuwa duba halin da Iman take ciki a cikinsu tunda dai Ummi ta gaya musu tana Asibiti shikenan daman ko wancan kwanciyar da tayi bayan an sallamota ba kullum take zuwa ba, da aka fara bata abincine taje zuwa tayi pumping Nonon da za’a bata daga baya ma a gida takeyi ta zuba a Container da suke bata akai shikenan. Seda sukaji Yunwa na neman hallaka su suka nemi abinci suka ci suka ci gaba da zaman jiran tsammani kuma.

A bangaren Bashir kuwa Tun a daren Dr Ishaq ya kira yana zuba masa ruwan masifa kamar shine Amiran, bayan sun gama ya kira Naziru ya gaya masa yanda akayi harda qarin maggi da gishiri abinda ya qara tunzura zuciyar Bashir din kenan ya shiga kiran wayar Amirah amma Allah ya taimaketa wandaya sace ya kashe dan kuwa daya sameta a waya Allah kadai yasan yanda zasu kwashe a daren, Ganin be sameta seya maida akalar kiran kan Asma’u.

Tana nade akan gadonta bayan ta gama shirin bacci har sannan Bata bar mamakin abubuwan da suka faru ba yau a gidan nasu kiransa ya shigo. Daga yanda ya amsa sallamarta tasan ba qalau ba se tayi shiru tana jin yanda yake magana ta inda yake shiga bata nan yake fita ba masifa yake mata akan me yasa tun farko bata gaya masa zasuyi taron sunan ba.

Galala ta saki baki tana sauraronsa ganin fa ba shiru zeyi ba yasa ta katse shi da cewa “Dakata Malam wai ko baka san wa kakira bane To Asma’u ce ba Amirah ba”.

Cike da masifa yace “oh maganar banza zaki gayamun kenan ce miki nayi bansan wanda na kira ba ai koma mene laifinki ne tunda kina gaba da ita ya kamata ki nuna mata abinda yake daidai da ba daidai ba data tace zatayi taron seki hanata tunda kinsan bana so”.

“Ashema ni ce gaba da ita, meye darin gami na da ita da zatayi abu na hanata ko an saka ni a ciki ballantana kuma nima gani nayi anayi. Kuma da kake maganar daidai ko rashin sa qarewarta naga da sa hannun yan uwanku tayi komai danginku kaf babu wanda bezo gurin ba su a cikinsu babu wanda yasan daidai kenan, kuma naga ai ita da uwarta suka shirya kamai se kuma kazo kana gayamun wani qabali da ba’adi dan Allah in baka da abin fada ni bacci zanyi kabarni inji da hayaniyar da suka jazamana a gida har sha biyu sannan muka samu salama Allah yasa kar cikin dare kuma wata sabuwa ta taso”.

Jin da yayi ta fitittike masa yasan halin Ma’u sarai itama ba baya bace seya sassauta muryarsa yana cewa

“Kina nufin dangina ne basu san daidai ba kenan, kuma da kikaga za’ayi ai seki kirani ko a wayane tun da safen ki gayamun ni na tsaqatar amma fa kalli duk abinda akayi se a gari naji ke baki kirani da kanki kin gaya mun ba”.

“Nidai ai kasan ban iya sa ido da munafunci ba bare kace duk abinda wata takeyi sena kwasa na gaya maka, bayan haka tsakanin ku can nasan koda yardar ka suke abunsu? Yanzu dai aikin gama yarigada ya gama mudai ka tiro azo a chanza mana keys din gidan nan kar muje wani ya sata shima muna zaman mu a ringa diro mana da daddare tunda yau gungun barayi aka hada a gidan”.
Chapter 33 · 0% Book details