← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 158

Sashe 66

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka na tashi washe gari babu walwala, nayi duk abinda na saba na koma daki na kwanta, ina kallonsa se zarya yakeyi yana kallona amma dan baqin hali ya gagara bude baki yayi mun magana haka muka wani har dare dadai yaga abin nawa bana qare bane se jinsa nayi a cunkushe yana cewa

"Dan bamu shiga gida jiya bane wai kike ta wannan Fushin to shikenan wani satin se kije" nayi masa banza kuwa tunda shi baze iya bani haquri ya rarrashe ni ba ai shikenan. Dakyar ya samu na sakko shima seda ya yarda randa na cika sati biyu ze kai ni nan da kwana uku kenan sannan na haqura, washe garin ranar da yamma yace na shirya zamu je gidan Addah ashe ma unguwar mu daya suna ta bayan layin mu ne.

Sam Addah ta kasa zaune ta kasa tsaye sanda mukaje, haka ta ringa kawo mun Abubuwa se sannu da zuwa take mun kamar wadda tazo daga China ina kallon Bashir se hada fuska yake da gani abin be masa ba yaran Abokanan zamanta da yaransu suka ringa shigowa muna gaisawa da yake akwai yammata da yawa Sa'annina a cikinsu dama wadanda suka girme ni nan da nan muka saba.

A nan Bashir ya tafi ya barni yace ze dawo da magriba, Amirah na naniqe dani qaramar Ummi ce me dan qyuya bata sakewa da mutane  Addah kuwa ta ringa bani labarai kala kala anan nake jin ashe su kadai ita da Dada iyayensu suka haifa anyiwa Addah aure ba dadewa suka rasu dan haka Nafi(Dada ta koma gurinta har tayi mata aure).

Na zata tana da wasu yayan bayan su Amirah a cikin hirar da muke  naji su kadai ne yayanta tace dai ta haihu duk basu tsaya ba dan Babban Danta ma ya girmi Amina yayar Bashir.

Da zamu tafi haka ta hada mun kayan yaji su citta da kanumfari da daddawa dasu kuka harda Barkono se kuma tace bari abarshi a daka se a kawo mun daga baya, Amirah harda kukanta da zan tafi wai seta bimu seda Bashir yayi mata jan ido sannan ta koma muka rabu da alqawarin zasu zo daman sun barmu mu dan huta ne tukunna.

Kwana biyu naje gidan mu, wannan tun safe na tafi ai kuwa nasha Fada gurin Goggo kamar tayi me wai tunda nake wa na taba gani tazo gida sati biyu da aure sena tattara na tafi bazan zauna ba aikuwa na ringa kuka dakyar Baffa ya bata baki ta haqura na kuwa bar mata dakin ta na koma gurin Hajia Babba har dare seda zan tafi naje mukayi sallama tana sake buga mun warning din karta sake ganin qafata idan ba wani abu ake a gidan ba, a hanya Bashir yayi ta tsokana ta wai gashinan, da yace bazan zo ba ai harda daukar fushi dashi yanzu gashi naje din an koroni.

Haka rayuwa taci gaba da mirginawa. Su Addah da kishiyoyinta uku masu kirki suma duk sunzo haka yaran gidan suna zuwar mun musamman da yanzu Bashir ya koma aiki in ya fita se gidan duk kadaici ya isheni in suka zo musha hirar mu kafin ya dawo sun tafi.

Tunda Amirah taga hanya kullum seta zo, abinda na lura shekara shida amma ba'a sakata a makaranta ba kuma duk sauran sa'anninta na gidansu suna zuwa. Dana tambayi Addah dalili tana dariya take cemun

"An kaita fa in gaya miki se tayi ta kuka wai bata son makaranta, ni kuma nace ina dalili tunda bata so yanzu a barta, in ta qara wayo dakanta ma zata ce a sakata".

Mamaki ya kashe ni, wai shekara shida se wani lokaci zatayi wayo ta zauna a makaranta? Abinda na lura dashi daman sam Addah ta sangarta yarinyar nan yanda kasan goyon gwarawa babu kwaba gata da shegiyar rashin kunya ga barna duk abinda ta gani seta lalata abinda yake hadani da ita kenan ma na fara gajiya da zuwan naya dan kullum tazo seta bata mun wani abun.

Akwai randa tazo inada wata yar Aku ta roba me magana, ina son Akun nan tun banfi shekara goma Hajjin su Anty Suhaima ta siyomun ita. A lokacin tace a kantin ita kadai ce tayi saura har Goggo tace baza'a siya ba dan rigima kawai zata zo ta hada a gida idan sauran suka gani amma Baffa yace se an siyowa Mamansa suka kuma yita nema ba'a samu wasu ba.

Tun sannan nake ta boyonta ko wasa bana fitowa da ita ayi kai in kana so kayi wasa da ita sedai mu shiga daki kuma ka biya ni kudi shekararta Tara yanzu na qudure har Yayana se sunyi wasa da ita.

Da yake babu wuta lokacin ni kuma ina Kitchen ina girki sena dakko mata na saka mata batir wai ta samu abin wasa.

Ina Kitchen ina jinta tana magana Akun na maimaitawa, se ji nayi tana qundumawa Akun zagi ita kuwa Aku ta maimaita.

"Yada wasan zagi Amirah ki dena babu kyau" na fada daga cikin Kitchen, se tace "Anty ita ce komai na fada se ita ma ta fadi irinsa" tana gamawa Akuma Ta maimaita.

"Bazaki dena kwaikwayata ba ko" Amiran ta fada caraf Aku ta sake fada itama, se abin ma ya bani dariya, ina shirin in leqo na gaya mata rikodin Akun takeyi duk abinda mutum ya fada itama seta maimaita se ji nayi Amiran nacewa

"Shegiya mahaukaciya wallahi kika sake kwaikwayona sena cire miki kai" ba kuwa ta rufe baki ba Aku ta dauka sena leqo ina cewa

"Ke Amirah bana hana ki zagi ba in banda shirmenki batiri ne da ita tana rikodin...." maganata ta maqale daidai sanda tayi wurgi da Akun nan da qarfin gaske ta daki bango take ta tarwatse komai ya kama gabansa.

Tsabar takaici kasa ko motsi nayi, yanzu Akun da har nagama tawa yarinyar ko kwarzane be sameta ba shine yanzu zata rada mun ita da qasa? A fusace na qarasa inda take na miqar da ita tsaye ina zare mata ido nace

"Amirah bakida hankali me yasa zaki fasa?"
Se kuwa ta wani murguda baki cike da fitsara tace "Na fasa din, ai seda na gaya mata ta dena kwaikwayona harda fa zagina take yi yanzu dana fasa se naga yanda zatayi".

Saboda haushi ban san sanda na kai mata ranqwashi ba, kamar zanyi haqaye nace "kin san shekarun Akun nan kuwa ta ma girmeki amma saboda shegen rashin jinki shine zaki fasa mun ai kuwa sena zane ki yau a gidan gobe ma ki sake yimun barna".
Fincikewa tayi ta nufi gurin Akun, injinta da shima ya cire ta hau tattakewa tana cewa "kika ranqwashe ni  toh na fasa na fasa din ayi koma menene".

Lallai rashin kunyar yarinyar nan ta isa dole na koya mata tarbiyya tunda bata da ita ai kuwa na jata Kitchen na zari tsintiya na shiga tsula mata a jiki daman rigar ta me kamar Bea ce bata da hannu ai kuwa dukan ya shigeta tana tsalle tana ihu ina tsula mata ina cewa

"Gobe ki sake yiwa wani rashin kunya tunda ke fitsararriya ce". Seda na mata lilis kafin na saketa, ta kwasa da gudu tana kuka ko ta kan Takalminta da Hijab bata bi ba ta bar gidan ni kuwa ko a jikina na tattare fasashshiyar Akuna idona ya ciko da kwallar takaici ganin babu ta yanda za'ayi ta hadu, a kan Centre table na ajiye jin abincina na kamawa a Kitchen.

Ina kwashe abincin Bashir ya dawo, yasan yanda nake son Akun nan da mamaki ya kalli pisis din da suke ajiye ya kwalo mun kira na fito ina masa sannu da zuwa.

"Meya samu Akun taki? waya fasa ta haka?" ya tambayeni yana kallona, se ji nayi hawaye ya silalomin na bude baki da niyyar magana hargagin Addah ya katse ni.

A sukwane ta fado dakin tareda Amirah a bayanta da har sannan bata dena kuka ba tayi tumu tumu da ita qasa har cikin gashinta da naci wuya jiya na gyara mata shi tsaf da niyyar yau zamuyi kitso da gani birgima tayi a qasa.
Ke Asma'u me Amirah tayi miki zaki kama ta kiyi mata wannan dukan kamar kin samu jaka" Ta fada tana hura hanci.

"Ni ba abinda nayi mata Addah kawai dan na fasa waccen shegiyar Akun shine ta kama ta dokeni da zabori" Amirah ta fada cikin kuka kafin Addah tayi wani abu se ji mukayi
"Fuu" Bashir daya fi kusa da Amiran ya dauketa da mari ta kuwa kwala ihu dan marin ya shigeta da gaske.

"Zaki wuce daga nan ko sena tattakaki fitsararriyar banza da wofi, wato ke kika fasa har kina sake fada kuma an hukuntaki shine zakije ki kai qara toh zuwa kukayi a rama miki ko me" ya hayayyaqo mata kamar ze sake rufe ta da duka tayi bayan Addah tana hadiyar zuciya dan tuni kukan nata ya tsaya.

"Idan ita ba'a rama bata ba ai kai seka zo ka dakeni dan ubanka se insan ka isa ka tarewa matar ka fada" Addah ta fada kafin ta juyo kaina tace

"Ke kuma wannan ya zama na qarshe da zaki sake dukar mun Yarinyar idan ma ba cin zali ba akan ta fasa abin wasa kawai ki hau dukan ta to wallahi karki sake" ta juya fuu suka fice ni kuwa na rakata da ido.

"Maganin ki kenan ai da kike jawo yarinyar kece baki san halin ta ba amma Yanzu gashi ta fara nuna miki, mtsw" ya ja tsaki ya shige dakinsa ya barni a tsaye.

Daga wannan abu naja baya gaba daya da Addah dan ba'a fi kwana uku ba se gata da Amiran ta kawo su harda Ummi wai zataje unguwa akayi sa'a Bashir yana nan yace mata muma fita zamuyi ta ringa mita kuwa nidai suna fita na sakawa qofa muqulli to ina dalili yaro yayi maka ba daidai ba in ka hukuntashi a zo har gida a gabansa a ci maka mutunchi to ni banga ana haka a gidan mu ba.
Chapter 66 · 0% Book details