← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 158

Sashe 123

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abubakar ne ya fado masa a rai, shi kuwa be yi wannan riqar da ze iya tunkarar Abubakar a yanzu ba bayan duk abubuwan dasuka faru tundaga auransa da Amirah zuwa yanzu daya sakar masa qanwa ya tabbatar ma baze saurare shi ba idan kuwa ya saurare shi to tabbas maganganu ze yayyaba masa da se yayi dana sanin kiransa.

Haka ya ringa saqa da warwara, shi da kansa ya tsinewa hali irin nasa yafi sau dubu ganin cikin lambobin sama da dari biyar da suke cikin wayarsa ya rasa shaqiqi daya da ze kira ya gaya masa damuwarsa ya bashi shawara akai.

Duk wadanda zasu bashi shawarar arziqi yayi fada dasu a lokuta mabanbanta lokuta amfabin zama da mutane lafiya kenan a rayuwa yanzu gashi yana cikin damuwa amma ko cikin yan uwansa da suke ciki daya ya rasa wanda ze tunkara dan ba saurarar sa zasuyi ba.

Wayar sa ce tayi qara, da sauri ya daga ganin Naziru ne me kiran a ransa yana Addu'ar Allah yasa ya sakko ne ya neme shi suyi magana dan yana da yaqinin ko iya Naziru idan ya shiga maganar ze iya shawo masa kan Ma'u saboda dab dakinta ne akwai kyakykyawar alaqa sosai a tsakaninsu.

A cunkushe kamar an wa Naziru dole ya gaida Bashir, ya amsa masa kafin yayi shiru yana jiran yaji abinyze fada

"Jirgin qarfe bakwai da rabi zata biyo idan sun sauka zata kirawoka" Naziru ya fada a taqaice.

Be damu da sanin wacece me zuwan ba yace masa
"Zan tura maka da Lambar samuel yanzu idan sun sauka kawai ta neme shi ze kawota gida, yawwa Naziru dan Allah...." qarar da wayar tayi alamar an kashe ce ta katse masa magana Wato Naziru ya gama jin abinda yake da buqata ya kashe masa waya.

Tagumi ya buga a gurin, ga damuwa, ga Yunwa ga ga kai abubuwan ma sun masa yawa. Tunawa yayi da ko sallar Isha beyi ba yasa ya miqe dakyar ya wuce dakinsa.

Gaba daya ko ina a hargitse yake komai yana nan zaune da kafafunsa daidai da takalman sa duk inda ya cire ya ajiye anan suke basu matsa ba yo daman waye ze gyara masa?

Badan ya tsawatar bama da har dakin nasa zata ringa sauke kwandon hauka da rashin hankalinta a ciki ai.
Haka ya dauro Alwala ya fara jera salloli yana ta kaiwa Allah kukansa har seda gabbansa suka gaji kafin ya zauna yana jin yanda cikinsa yake karta.

Dole ya tafi Kitchen ya hada shayi ya sha da burodi dan babu komai idan basu din ba sannan ya sake dawowa ya zauna a palour se sannan ma ya tuna da beji motsin yaran ba se ya miqe ya leqa dakinsu Aliyu.

Gaba dayansu suna ciki sun kwanta bacci, dakin Amirah ya koma bega Farida A ciki ba seya sake komawa kai tsaye ya kunna filita ya qarasa kusada kan Aliyu ya tsaya yana kiran sunansa.

"Ina Faridah?"
"Tana gidan Mami" Aliyun ya fada a cuskule kamar ma daman ba bacci yake yi ba se ya juya yana ce masa

"Kayi muku Addua seda safe" ya kashe fitilar yaja musu qofa.

Ranar dai kwanan zaune yayi idan yayi sallah ya gaji se ya zauan ya hau jan charbi har aka kira Sallar Asuba suka fita masallaci suna dawowa ya kwanta saboda wani bacci daya ji yana neman fin qarfin sa.

Can kamar a mafarki ya ringa jiyo karadi da hauragiya kamar ta Addah, qofar dakinsa dayaji ana duka tasa yayi juyi yana jan tsaki saboda katse masa daddadan mafarkin da yakeyi ya bude ido dakyar yana tambayar waye

"Nice nan Bashir gamu mun iso" ta fada daga waje. Dakyar ya iya tashi ya bude qofar a ransa yana mamakin wanene ya turo masa wannan matar? Kaf dangi a rasa wa za'a turo musu se Addah ai ba taimaka musu zatayi ba sedai ta qara masa yawan damuwar dayake ciki.

"Fisabilillah saboda wulaqanci irin naka Bashir seka turamun wani qedari da ko zo na kashe ka be sani ba duk ka gama kadamun hanta kasan da yanda na iya gano inda ma yake a cikin iyafot din ina zuwa kuma naganshi wani basamusen Arne. Nidai badan sunyi turanci da Naziru ba kuma Nazirun ya gaya mun na bishi babu komai Alqur'an da sedai nayi ta yawo a iyafot din idan suka gaji da ganina na nuna musu hotonka ai nasan dai baza'a rasa wanda yasan inda kake ba" Addah ta shiga jera masa bayani tana riqe da wata qatuwar Akwati kamar wadda tayo hijira.

"Ya akayi suka barki kika taho da wannan jakar" ya fada yana kallon Akwatin tata.

Seta gyara tsayuwa tace
"Kaidai bari ai Allah ya tsinewa mutanen nan seda sukawa jakata tsirara kamar wadanda na sako uwarsu a ciki, dakyar fa seda Yaron nan Naziru ya biya wani kudi wai nayi lodi da yawa kafin suka barni na wuto da ita dukda haka seda suka kwashe mun wasu abubuwan wallahi nidai nayi Allah ya isa".

Juyawa yayi ze koma ciki dan kansa harya fara masa ciwo da wannan surun nata se kuwa ta tareshi tana cewa

"Ina kuma zaka? Ita Amirar tana ina ko bata ji shogowata bane? Sannan ina zan ajiye kayan nan ga Yunwa ni ina jin ai se a bani abin kari".

"Ina zuwa" ya fada yana shigewa ciki tareda murzawa qofar key. Wayar Dada ya shiga kira yana shafa goshinta ko tsayawa gaisuwa beyi ba yace mata

"Dada me yasa zaki turo mana Addah kin manta matsala ce matar nan nida nake neman sauqi ya zaki qara mun damuwa?"

"Toh Bashir idan ba ita ba wa kake so tazo karka manta fa ita ta haifi Amirah kuma ko ba haka ba yar uwata ce kaga tana iya zuwa gidan ka ta zauna ai. Nidai Koma mene ne dai se kayi haquri ka dauke kai kwana nawane da Amirah ta warware ai zata dawo ne ta barku ko" Dadan ta fada.

Sallama sukayi dan bashida abinda ze kuma fada toh mema zece bayan aikin gama ya gama ai tun kamin ta taho ya kamata a gaya masa da se ya dauki mataki yanzu kuwa ya zeyi ma da ita.

Wanka ya shiga yana jiyo yanda take ta mita tana buga masa qofa harya shirya tsaf kafin ya bude qofar ya fito.

"Wannan wane kalar wulaqanci ne haka, ka barni a gantale ko masauki baka bani ba idan Nafi ce tazo haka zaka barta a tsaye ka shige daki ka rufo qofa koda yake mantawa nayi ai ba mutunchi ne dakai ba daman to ina ita Amirah tunda uwarta ce ni ai bazata wulaqantani ba".

"Nifa bance a turo ki bama kawai ki jira yanzu za'a zo a mayar dake Airpoki wuce gida" Bashir ya fada cikin hade rai.

"Ai wallahi ko ubanka Amadu be isa ba dan naga guri nan zama me nawuda ta samu katifa duk baqin cikinka se naci arziqin da kuka tare a nan bakwa tunawa da mu se abinda kuka ga dama kuka yafa mana ina ita daya shegiyar nace maka tunda ita na haifa ai bazata koreni ba" Ta fada tana riqe qugu kamar wata qaramar yarinya.

"Tana Asibiti se gobe za'a sallamota" ya fada a cuskule yana qoqarin wuceta.

"Yau naga abinda ya ishe ni, to ka kaini Asibitin mana kana jan qafafu kamar na zalbe zaka wuceni zamane daram ba inda zani sedai baqar zuciyarka ta kashe ka shege me baqin halin tsiya@ ta fada tana gyara mayafinta. Ba tareda ya kalleta ba kuwa yace mata

"Ba'a zaman jinya ki jira da Yamma wanda ya kawo ki ze zo seya kaiki ki dubata ku dawo" yana gama fada yayi ficewarsa dan gara yayita yawo a gari yana qona mai daya zauna a gidan nan wannan birkitacciyar tsohuwar ta chaza masa kai.

Rasa abinyi Addah tayi, ta shiga Kitchen ta duba gadai kayan abinci amma bata san ya zata yi amfani da kayan wutar ba dan Gas cooker dinsu ma soft touch ne. Palourta dawo ta tsaya tayi sa'a sega Aliyu ya fito daga daki da Kofin shayi da farantin daya soya dankali da kwai ga ragowar nan be cinye ba seta nufeshi tana washe baki tace

"Yawwa Dan Albarka taimaka nima ko shayi da kwan ne ka bani wallahi Yunwa nake ji ban karya ba na fito, bani wannan na fara dashi kafin ka hadomun wani" ta fada tana qoqarin riqe farantin hannunsa.

Kallon daga ina ya mata kafin yayi kwana ya fasa shiga Kitchen din da yayi niyya, akan idon Addah ba tareda ya kalata ba ya fita qofar gida ya zazzage abincin a inda suke zubawa karnukan da suke gadi abinci ya sake dawowa ya wuceta ba tareda ya kulata ba.

Haka ta ringa masifa kamar zata ari baki amma dan gaske yayi banza da ita qarshema Tv ya kunna ya hada Game dinsa ya fara bugawa daidai Nan Jafar ya shigo, shine me farat farat nan da nan ya gaishe ta. Shi ya rakata har qofar gidan Ma'u be shiga ba dan yasan qila tayi masa fada se ya koma gidansu yana shiga kuwa Aliyu yayi kansa da fada kamar ze dakeshi shi dai yayi shiru be amsa masa ba.

ASMA'U
Cikin filo na cusa kaina dana dafe da hannaye bibbiyu, na kasa yarda Bashir ne ya durqusa a gabana yana bani haquri sannan waini Asma'u na iya gaya masa maganganu haka ba tareda wani dar ba.

"Kar fa ace na dena son Bashir da gaske" na fada a fili ina tashi zaune. Tagumi na rafka hannu biyu gaba daya na rasa me ma yake damuna. Ina jin wayata dake gefen gado tana ta qara amma naqi dubawa dan nasan dayan uku ne ko dai Bashir ko Yusuf ko kuma dayan Mayen Hayatuddeen.

Gaba daya daren haka na qarar dashi ina juyi da tunane tunanen da ni kaina bansan me nake tunawa ba. Saboda rashin samun wadatacce bacci da ciwon kai na tashi idona yayi ja kamar wadda tayi kuka.

Da yake Asabar cema abin yazo mun da sauqi nayi wanka na saka riga mara nauyi kafin na fito palour na tarar da Amnah da Farida suna cin abinci.
Chapter 123 · 0% Book details