← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 158

Sashe 6

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

LAGOS
Malam Bashir kuwa dakyar ya iya farkawa da Asuba kansa kaman an dora masa Dala tsabar ciwon da yake masa, basu iya fita masallaci ba a gida sukayi sallah suka hau shirin makaranta dan zasu fara biyawa Asibiti su duba Mami.
Tea suka dafa suka soya kwai suka karya, basu daukar mata komai ba se kaya kala daya wanda zata saka idan An sallameta tunda Asibitin nada uniform na marasa lafiya baa buqatar kaya haka abinci ma a can ake basu..

A hankali ya tura qofar hadi da sallama, a nutse ta dago ta kalleshi tareda amsa sallmar, fuskarta dauke da wani kyakykyawan murmushi. Magana take yi da yaranta kowa na gaya mata yanda yayi missing nata.

Qara shigowa yayi idanunsa akanta yana qarewa kyakykyawar fuskarta me cike da kalama kallo ganin yanda Omo blue din Uniform din Asibitin ya amshi fatar ta matuqa kamar wasu kayan kwalliya. Aliyu ne ya bashi kujerar da yake zaune akai still idanunsa akan ta yaja ya zauna dukda daqi sake dagowa ballantana ma su hada idanu da ita.

Shigowar Nurse da taje kawo mata breakfast yasa ta daga kanta Yaran suka shiga gaida Nurse din tana amsa musu da kulawa, Dan gyaran murya yayi tareda kallon yaran yace “kuje mota ku jirani kar mu makara idan mun taso se mu sake biyowa aga Mami ko? Basu musa ba da daddaya suka fice bayan sun mata Addu’ar samun sauqi itama Nurse aje kayan tayi ta gaishe shi kafin tayi waje abunta.

Cikin sanyi jiki ya miqe zuwa gefenta da tun kafin ya qaraso ta dauke fuskarta zuwa dayan side din, be haqura ba ya bita, can qasan maqoshinya furta “How are you feeling now? Ina ne yake miki ciwo?”

“Oh really ka damu ne daman da lafiyata toh Alhamdulillah Yanda kaso be samu ba jinina ya sauka ya dawo dadai”. Be kula maganar taba ya sake matsarta yana cewa “Why? Me yasa baki gayamun that you are pregnant ba??”

Ita se a yanzu ma ta gane dalilin wannan fake concern din wato saboda cikin da ya zube, murmushi tayi me kama da yaqe tana tashi zaune sosai tace
“Baban Ai kenan, to ina ruwanka da ina da ciki ko bani da shi naga yanzu ai baka damu dani da yaya nane bako? Ko da yake dama ai bazaka damu ba tunda qaddarace tasaka kuka hada Zuri’a dani
Yanzu ai gashi za’a haifar maka jininka yayan dangi na meye zaka damu akan wanda Allah ya taqaita samuwarsa bare yazo shima a barshi a titi a bula masa qura ko yaje makaranta ko kar yaje duk ba matsalar ka bace.

Wallahi Baban Ali kayi nasarar doramun Hawan jini amma ina tabbatar maka bazan bari ka nakastamun rayuwa ba idan kuwa haka ta faru sedai muyi mutuwar Kasko”.

Kaman wanda aka dasa haka ya bude ido da baki yana Kallon ta, kai wannan Mata wai ita bata yafiya ne a ko yaushe burinta ta ringa hukuntaka da kuskuren da ka aikata? To in ba haka ba meye na dawo da wadannan maganganun marasa dadi? Yana shirin maida mata da martani wayarsa ta dauki qara, hadiye bisashshan yawu yayi kafij ya zaro wayar yana tattara kalaman da ze bata amsa dasuba zuciyarsa.

Sunan “DADA da ya gani ya saka shi saurin daga wayar ya kai kunnensa. Cikin harshen fulatanci ya shiga gaisheta ta Amsa tana tambayarsa Asma’u da yara.

“Bashir Meya sami wayarka Amirah tace tun jiya tana kira baka dagawa” ta fada bayan sun gama gaisuwar.

“Qarata ta kai kenan, ai kuwa seta gane bata da wayo” ya ayyana a ransa a fili kuwa se yace
“Dada Ma’una ce bata da lafiya tayi Bari muna Asibiti tun jiyan”
“Subhanallahi a garin yaya” ta tambaya muryarta na nuna Alhini se ya sake narkewa abin tausayi yace

“Nima ban sani ba ina office aka kirani wai ta yanke jiki ta fadi ina zuwa muka hato Asibiti” ya yanko maganar da shi besan gaskiya ya fada ba ko qarya. Asma’u dai kallonsa kawai takeyi tana qara mamakin Bashir a ranta, miqo mata wayar yayi seta tsaya kamar bazata karba ba kome ta tuna kuma ta karba.

Sama sama ta gaida Dadan tareda amsa ya jikin da take mata dan itakam ai sun shata ta warke abinda mutanen nan suka mata ta yaya zata manta dashi?

Kallonta Bashir yake a ransa baya jin dadin yanda alaqar Dada da Ma’u ta lalace be kuma san ta yanda ze gyarata ba, yasan sun mata laifi amma Ma’u ma akwai ruqo da kafiya ai.
Miqo masa wayar tayi ya karba sukayi sallama da Dadan sannan ya kashe. Hannu yaki ze riqe nata tayi saurin janyewa se ya girgiza kai kawai yace “Ki kwanta ki huta bari naje mun makara ma idan mun taso zan ga Dr ance be shigo ba yanzu naji yaushe zeyi discharging naki”

Bata amsa ba shima be saka rai ba dan haka yaja qafafunsa ya fice yana sake kallon Wayarsa dan ganin da gaskw sun makara din.
Asma’u kuwa da harara ta raka shi kafin ta zumburi baki tana qunquni tace “wato in dawo kaci gaba da Gallazamin ko toh ba inda zani se na tatike Aljihun ka qat na huta wallahi”
Ita kadai tayi ta sababi har bacci ya dauketa sannan tayi shiru.

Bashir kuwa sauri sauri ya kai yaran har an rufe get dakyar suka karbe su suna ta masa qorafin in suka sake makara bazasu karbe su ba shida ya ajiye su ya wuce nasa aikin da baya zaton ze amfani komai yau. Gaba daya shima ji yake kamar bashi da lafiya ga wani mugun bacci dayake jin idon sa yayi fici fici har wani yaji suke masa,haka ya lallaba ya qara sa office din.

GOMBE
Bayan da Dada ta ajiye wayar se ta maida hankalinta kan yayartata Adda fatu datayi kamar bata gane me Dada da Bashir din suka tattauna ba.
“Ashe Ma’u ce bata da lafiya tayi bari suna Asibiti” Dadan ta fada.
“Allah sarki Allah ya bada na aike” Adda Fatu ta amsata a ranta kuwa murna tayi gara ma da cikin ya zube ita duk wadannan yayan data zuba bazata haqura ta barwa Amirah itama ta samu rabonta ba ita dai fatan ta Allah yasa ba ita Amiran ta gado ba dan ta fara ganin sare sarin hakan, seta gyara zamanta tana cewa

“Kinga daman maganar shirye shiryen tafiyarta lagos din nan ce lokaci nata tafiya yace ze turo mata kudi tayi siyya anan kafin ta tafi yanda kinga in lokacin haihuwa yayi ta howa kawai zatayi komai na jiranta a nan to kuma naga yana nema ya shiriran tar da maganar ga yarinya kuma ko baccin kirki wallahi bata iya yi to Allah ya hada ta da jarababben ciki gara dai yazo ya tattarata su tafi dan nikam na fara gajia gaskiya”.

Kallonta kawai Dada tayi ita kam Adda Na bata mamaki da kunya wallahi in ba haka ba ina ita ina irin wannan magana ai tsakaninsu ne can ko amma ita babu ruwanta tana manta cewa Matsayin Suruka take a gurin Amira ba kowacce magana ya kamata ta ringa yi da ita b, dakyar ta bude baki tace

“To Adda nake ga siyayya ai bawata matsala tunda in kayane ai can Lagos sun fimu in taje din se su siya acan su turo kuma ni da zaki ji ta tawa ma da tayi haquri ta yi zamanta a nan tunda yana zuwa sati biyu dan gaskiya abinda ake shirin yi ba Adalci bane. Yarinyar nan Asma’u mun mata abubuwa da yawa ni wallahi har kunyarta nake ji to yanzu kuma akace wannan gaskiya ya zama da daukar Alhaki kuma.https://chat.whatsapp.com/GBC9U1ddKHO94q4CSL2jZ8

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(Alkhairi CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar Qaddarah)

Page 5

“Ban gane ba Nafi me kike nufi da ta haqura da binsa ko baki gane halin da yarinyar nan take ciki bane, yarinya na buqatar mijinta a kusa idan kuma ba halaka ake so ta fada ba se naji, nifa dama na gane take takenki kina so ki fifita bare akan yar uwarki ko Nafi. Kuma da kike zancen za’a shiga haqqin Asma’u ita Amirar daba uwace ta haifeta ba ai ba’a shiga nata haqqin bako” Adda Fatu ta fada cike da jin haushin Dada, se Dadar ta gyara zama tareda cewa

“Ni ba haka nake nufi ba amma gani nayi ai tun farko tare suke a can, yanzu ko cewa akayi suringa yi idan wannan ta je ta kwana biyu se wannan taje kinga bame yiwuwa bane tunda Asma’u tana aiki a garin bakuma ze yuwu muce tabar aikin ta ba tunda idan Amira ce a matsayinta muma bazamu bari a mata ba ko?

Ni dai a nawa ganin Adda ayi haqurin shi yafi a zauna lafiya tunda har komai ya daidaita tsakaninsu bana son wata rigima ta sake tasowa kindai san sharadin da Malam ya kafa mun dan Allah bana so ya sake ganin laifina akan lamarin gidan Bashir”.

Se Adda Fatu ta miqe nan da nan ta fara sababi da fadan maganganu ta inda take shiga bata nan take fita ba, ga baqin cikin rashin samun biyan buqata a gurin Bashir gashi da Alamu wannan Karon Nafi na nema ta bata matsala amma ina bazata sabu ba wallahi dole tasan abinyi. Miqewa tayi still tana masifar ta nifi qofa,

“Wato Nafi kina ganin yanzu kinkai matsayin da zaki qalubalance ni ko? Kin manta duk halaccin da nayi miki a rayuwa saboda qasa ta dade da cinye Naman Baffa da Inna dole ki watsar da maganar su tunda kina ganin yanzu kema Kin kawo qarfi. Na gode zan kuma tafi amma daga yau kisa a ranki baki da sauran wata yar uwa data rage miki a duniya tunda kin zabi Matar danki akaina da Yata shikenan Nafi na yafewa Duniya ke” ta qarasa tana rushewa Kukan munafunci wanda dashi take cin galaba akan Nafin.
Chapter 6 · 0% Book details