← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 158

Sashe 42

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru yai yana kallona harna dasa aya ina sake turo dankwalina gaban goshi, ajiyar zuciya yayi kafin yace “yanzu dai bazaki karba ba kenan?”

“Allah me iko, da Hausa fa nayi maka jawabi dalla dallah amma kake sake tambaya ta kuma?”

“Eh saboda kinsan ni bana son dogon surutu, amsa daya nake buqata Eh ko Aa kawai” ya fada a dan hasale alamar ya fara barin cool site dinsa ze koma Bashir dinsa na gaskiya, se kuwa na tura baki gaba nace “Toh a taqaice dai bazan karba ba”.

“Shikenan, amma ina da ikon da zan kawota cikin gidan nan ko tunda gida nane” ya fada yana miqewa, nima sena miqe tsaye jin wani qundumemen rainin wayo,

“Tabbas gidanka ne ka isa ka dakko kowa nene ka kawo shi ciki, zaka iya kawo ta tunda itama gidan ubanta ne ai se ka hado dame kular maka da ita, ko kuma kai zaka aje aikin ka ka zauna rainon duk ba matsala ta bace ni” na fada ina dauke kai gefe, ina jin yanda yake qare mun kallo kafin yaja tsaki tareda sakin kwafa ya shige daki na rakashi da harara ina cewa a fili

“Wallahi ba tsaki ba kome zakayi sedai kayi, bazan karbi raino ba, rainon ma yar Amirah yarinyar da duk zamana da ita idan dana ze tsaga guri saboda kuka bazata dauke shi ba balle aje ga tsarkin kashi ko wanka shine ni ga jaka yanzu ta haifa za’a dakko a kawo mun in riqe mata toh ko daga turu aka kuntota qarewar rashin nutsuwa sedai duk handa za’ayi ayi”. Tsaf nasan yaji ni dan da qarfi nayi saboda yajin, na koma kan kujera na zauna, se kuma na miqe na dakko wayata na dokawa Dadar su kira dan fa karma inji wata magana daga baya.

Ringing biyu ta dauki wayar, a taqaice na gaisheta ta amsa kafin na shiga koro mata jawabin yanda mukayi da Bashir, na rufe da cewa “Iya gaskiya ta na fada ko bana aiki bazan riqe mata ya ba kowa ya kula da nasa Allah ya taya masa, idan kuma Ya dage akan hakan to sedai na bar masa nawa nima ya nemo wadda zata riqe masa su ni intafi”. Shiru Dada tayi har na kai qarshe sannan ta numfasa tace

“Ya kirani ya gayamun kuma na gaya masa wannan ba me yuwa bane, todai yanzu duk se hankalin ku ya kwanta tunda Allah ma ya raba muku gardamar ya karbi abarsa, se kowa yayi haquri ya maida wuqar” Dadan ta fada cikin sanyin murya,

“Hasbunallahu wani’imal wakeel, ta rasu jikin ne ya sake tashi?” Na tambayeta a rude dan maganar ta dake ni dagaske, “ta rasu yanzu Likitan ya kira Naziru yake gaya masa lafiya lau dan yau sukayi niyyar sallamarta ma har an yi mata wanka ma sun bata madara tayi bacci to daga baccin ne kuma bata farka ba”.

“Allah yasa me ceto ce, ya musanya mana da wadda tafi ta Alkahiri” Na fada a sanyaya tareda sauke wayar daga kunne na, ina dagowa muka hada ido da Bashir daya fito kamar wanda aka koro.

“Se ki zuba ruwa a qasa kisha, da baki karbeta ba ta mutu” ya fada yana jifana da wani irin kallo kamar ni na kashe masa ita. Sena miqe na nufe shi ina cewa “karbarta ko akasin haka be isa ya chanza hukuncin Allah akanta ba tunda babu dayan mu daya halicceta ko kuma ranta yake hannunsa dan haka ko tana gidan nan tunda wa’adinta yayi dole ta mutu, in zuba ruwa a qasa nasha kuma bani zaka gayawa ba Uwarta da tai sanadinta can zakaje ka gayawa dan ita ta nuna a fili bata damu da ita ba” na wuce shi na shige dakina tareda banko qofa, in banda ma rainin hankali ji abinda fa yake cewa fa.

Ina ciki naji tashin motarsa alamar fita yayi a raina nace a sauka Lafiya Allah ya gani qilan zamanta ze iya zama fitina shiyasa Allah ya karbi abarsa, Har qarfe biyar ina dakin fito ba, gaba daya zuciyata a jagule take ga alhinin rasuwar Iman ga soki burutsun Bashir na sake kiran Dada nayi musu ta’aziyya ta cikin wayar ina iya jiyo kururuwar Amirah da muryoyin mutane wasu na tausarta wasu kuma suna mata fada akan kukan da takeyi.

Na tausaya mata harga Allah Kuka kam dole tayi shi wannan duka wani kan wani amma yata iya haka Allah ya tsara abinsa masu samari da yammata ma ake dauka bare ita jaririyar da ba dadewa tayi ba.

Har na miqe da niyyar zuwana dora abinci wani tunani yazo mun, ta yuwu fa Bashir ya tafi Gombe be gayamun ba ga yara a makaranta lokacin tashin su tuni ya wuce, Hijabi na na dauka da wayata na fita, bari naje na ari motar Anty na dakko su dan tawa tana gurin Service ba’a dawo da ita ba, ina kulle qofar gidan motar sa na tsayawa da yaran ya dakko su se na bude na koma ciki ina jiransu.

“Mami ina zakije” Abdallah ya fada bayan daya rungume ni, “Da zuwa zanyi na dakko ku na zata Abbi ya tafi Gombe” na fada ina kallon Bashir daya shigo a sanyaye kaman wanda aka sheqawa ruwan sanyi.

“Abbi yace Baby Iman ta rasu wai Mami” Farida ta fada fuskarta kaman zatayi kuka, sena riqo hannunta ina cewa “ta rasu Farida” kaman tana jira kuwa ta saka kuka tanacewa “kenan banida sister mace yanzu har fa na fadawa friends dina yau a school step mum din mu ta haifo mun baby sis”

“Dallah malama yi mana shiru, kina kallon yarinya kamar mage dama ai kinsan mutuwa zatayi kuma ai ma...”

“Shut up You are very stupid Aliyu” Bashir da yake shan ruwa a dispenser ya katse Aliyu cikin tsawar da harni seda na tsorata amma ko gezau yaron nan beyi ba sema ido daya zubawa uban suna kallon kallo kamar wasu zakaru.

“Zaka wuce daga nan ko sena zo na same ka wawan yaro har fada kake daman mutuwa zatayi kenan so kake ta mutu koh” Bashir din ya sake fada cikin bacin rai, se na saki hannun Farida da Abdallah na miqe da niyyar yin magana Aliyu ya rigani yana cewa

“Toh ni Abbi me nace kawai dan na fadi gaskiya wayace su jagwalgwalata sannan su sakata a sanyi ai dole ta mutu....” be rufe bakinsa ba Bashir ya dauke shi da mari da har seda gefen bakin sa ya fashe kafin ya fizgo shi ya hau dukansa.

Kuka yaran suka saka gaba daya ganin abinda be taba faruwa ba a gidan yau Bashir ne yake dukan Aliyu kamar wanda ya samu jaki, tsakiyar su na shiga ina qoqarin kwatar Aliyu da ko gezau sema cewa da yake yi

“Ai daman seda nace miki ki koreta daga gidan mu muguwa ce kika qi seda ta aure shi, gashi nan yanzu yafi son su akan mu tunda ta haifi yarinyar nan kina kallo yanda hankalinsa ya koma kanta komai ita har comapany da ze bude da sunan Farida ma ya chanza na gani sunanta ya saka, shi yasa kullum nayi sallah sena yi Addu’a Allah yasa ta mutu dan akan Abbi ze iya yin komai gashinan kuma kina gani”.

Bige bakinsa nayi ina fashewa da kukan nima dan na kasa tare dukan da Bashir yake masa shi kuma yaqiyin shiru nasan kalaman sa ne suke qara tunzurashi seda ya gaji dan kansa kafin ya kyale shi ya shige dakinsa ya banko qofar ya barmu muna rusa kuka kamar nan ne gidan mutuwar.

Wannan wane irin bala’ine, ni na kashe yarinyar ko Yara na da ze huce akan mu? Ai kuwa wallahi da sake zan dauki komai amma banda irin wannan dukan da kalaman da basu dace ba akan yarana.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 25

Ina kuka ina gasawa Aliyu fuskarsa da ta kumbura sosai saboda marin daya sha a hannun Bashir, tausayin sa ya cikani tabbas be kyauta ba amma ai dukan yayi yawa, Yanda ya zage ya ringa dukansa kamar wanda yake dambe da sa’ansa.

Gaba daya yaran suna tsaye sunyi cirko cirko kowa fuska da hawaye kana kallonsu kasan a tsorace suke, bude qofar da Bashir yayi da qarfi yasa suka zabura kafin kace meye wannan sun maqalqaleni wani kan wani Jafar yana cewa “kice masa yayi haquri Mami dan Allah karya doke mu”.

Tausayinsu da matuqar takaicin Bashir ya sake qume ni, na daga idanuwana da har sun qanqance saboda kuka na kalleshi yana tsaye shima mu yake kallo, fuskarsa a daure tam haka idanunsa sun kada sunyi jajir har wata jiniyace ta fito a goshinsa. Daga tsayen yace mun “Ina kika saka mun folder dana ajiye akan Gado”.

Ayanda nake jina Banyi niyyar tanka masa ba amma saboda yaran da suke gurin bana so na bada qofar da zamu ringa raba hali a gabansu dan hakan ze shafi tarbiyyar su, “Ina zuwa” nace masa kafin na miqe na kama Aliyun da zuwa sannan jikinsa ya rufe da zazzabi me zafi amma saboda dakiya da taurin kai har sannan ko digon kwalla babu a idonsa.

Dakinsu na rakashi, ina tsaye ya shiga ya watsa ruwa a jikinsa ya fito dakyar ya kwanta akan gadonsa. A cikin first Aid box dinsu na ciro masa Paracetamol na bashi yasha, ina zaune a gefen kansa nace

“Aliyu kana babba kai kake so ka raba kan qannenka ko, irin abinda na koya muku kenan ka tsaya mahaifinka yana fada kana fada Aliyu?”

Se a lokacin ya saka kuka yana cewa “Mami Abbi ya canza wallahi ya dena son mu, da bakwayin fada amma yanzu kullum se sukunyi kuma duk akan Anty Amirah ne. Mami yanzu fa da muna tahowa yana waya da Abokinsa Uncle Bala yana ce masa daman bakya son yarinyar yace ze kawo miki ita kinqi yanzu gashi ta mutu hankalinki seya kwanta ai”.
Chapter 42 · 0% Book details