← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 158

Sashe 106

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Dada ta daga kai ta kalleshi, ya akayi yasan da maganar cikin Ummi bayan Addah ta tabbatar mata babu wanda ya sani shiyasa suke neman hanyar da Asirinsu ze rufu kafin abu ya fashe kowa ya sani in har kuwa Alhaji yasan zancen to babu shakka labari ya rigada ya gana gari sune suke shirmen su da tunanin babu wanda ya sani kenan.

Muryar mutumin daya kira a waya ce ta katse mata tunani, tana ji suka gaisa kafin Alhajin ya ke ce masa

"Yanzu Me dakina take samuna da maganar cewa Unaru ya janye maganar aure ko? Shine nace bari na kiraka na tabbatar daga bakinka tukunna"

"Wallahi Alhaji nima da safiyar yau dinnan ya same ni yake gaya mun na kuma yi masa fada na gaya masa be isa ya mayar damu qananan mutane ba, yanzu haka ka ganni shiri nake zanje na samu uwarsa na gaya mata halin da ake ciki shiyasa ma ban kiraka ba na bari se mun gama yanke sa rana tukunna sedai kawai ka gammu"  mutumin ya fada daga daya bagaren

"Aa Alhaji baza'ayi haka ba, babu wanda fa yayi masa dole akanta shi ya gani yace yana so dan haka yanzu ma bamu san dalilinsa na cew aya janye ba. Ka barshi kawai Allah yasa hakan ne yafi Alkahiri amma batun a tilasta yaro ma be taso ba shine ma'auri ba kuma auran fari ba bare ace za'a bashi shawara rajin kansa yasaka shi tunanin qarawa tunda kuma ya janye a qyale shi kawai" Alhaji Amadu ya fada kai bazakace yar sa ake cewa an fasa aure ba.

Haka sukayi sallama wancan yana ta faman bada haquri da alqawarin idan komai ya daidaita zasu zo, yana kashe wayar ya kalli Dada data saki baki tana kallonsa yace

"To kinji dai abinda ya fada. Idan aure take so anjima zan bada sanarwa a masallaci duk wanda yake sonta yazo zan bashi sadaka har sadakin ma ni zan biya masa idan kuma taqi ai kinji abinda na fada a farko seta zabi abinda ya mata a ciki.

Ni yanzu kin cinye mun ma lokacin baccina bari na tashi nayi ta hailala da istigfari maganin masifa kafin a kira sallar" ya qarasa yana janyo carbinsa.

Haka Dada ta kwashi qaqafunta ta fice, a bakin qofa taci karo da Fainusa da ashe tana labe tana jin komai bata kulata ba ta wuce dakinta can qurya ta shiga kiran Addah a waya.

GIDAN ADDAH

Addah na tsaye akan Ummi dake kwarara amai a bandaki tana zazzage mata ruwan masifa da bala'i kiran wayar Dada ya shiga. Bata daga ba ta ci gaba da sababinta, magani ne ta karbowa Ummin na zubar da ciki tana shi shine ta amayoshi tas kuma wannan shine karo na uku data kashe kudi aka karbo mata magani amma ciki na nan daram ko girgiza beyi ba.

Kiran wayarta da ake tayi babu qaqqautawa ya saka ta fito cikin bala'i ta daga tana cewa
"Wai Nafi wannan wace kalar lukutar masifa ce da zaki ringa kirana kamar naci miki bashi ki barni naji da abu daya mana haba"

"Addah dole na kiraki ai, kika cemun babu wanda yasan da zancen cikin Ummi amma ya akayi har Alhaji ya samu labari anya kuwa magana bata fasu ba Addah?"

"To idan ma magana ta fasu Nafi se akayi wace kutumar uba eye nace se akayi me? Da zaki ce mun Amadu yasan zancen waya sani ko a munafuncinki kika gaya masa tunda kema ai ba sanin zuciyarki nayi ba waya sani ko kina cikin masu farin ciki da abinda ya same ni in ba haka ba shi mijin naki yana kanannade a kujera ta ina ze jiyo wani labari?

Ni karki sake kirana indai ba mafita kika samo mun ba, kuma abin kunya ai ba kanta farau ba kumaba ita zata rufe ba wasu da yawa Allah kadai yasan shegu nawa suka haifa aikin banza kawai" ta kashe wayarta kafin ma Dadan ta sake magana.

Kan Ummi data fito daga bandakin da kyar ta koma tana cewa
"Dan uwar ubanki ba kwanciya zakiyi ba tashi zakiyi mu tafi gidan Balaraba yanzu ai Qanwarta sarai ta taba yin ciki sukaje aka cire muje ta raka ni gurin dan dole se abin nan ya fita ko bangon duniya zancen yaje qarewarta se an cire idan yaso senaga shedar da za'a bayar idanan tashi gulmar".

Kuka Ummi ta saka tana cewa ki qyale ni Addah in dai ba so kike na mutu ba dan Allah ki rabu dani. Qaddarata ce tazo a haka kuma kece sila dan haka ki barni na haife abinda yake cikina ban sani ba ko shine silar kaffarata a gurin ubangiji"

"Wallahi sedai ki mutu dan ubanki dama amfanin me zakiyi mun idan kin rayu bayan abin kunyar da kika janyo mana, ki tashi tun wuri mu tafi kafin nazo na haye kanki na murqusheki daga ke har shegen dan cikin naki ku mutu kowa ya huta".

Haka Ummi tana ji tana gani Addah ta tasata a gaba tana kuka suka tafi. Matan gidan da sukayi cirko cirko suna kallonsu dan duk abinda ta ke fada sunji saboda ba a hankali take magana ba.

Daman sun san da qishin qishin din maganar yanzu gashi sun tabbatar suna fita kuwa Binta da tafi kowa tsugudidi ta shige daki ta dauki wayarta ta kira Alhaji Murtala.

Yana zaune a kasuwa a daidai lokacin wani Amininsa Alhaji Yero ya same shi da maganar cikin Ummi daya ji a bakin Matansa.

Hankalin Alhaji Murtala yayi qololuwar tashi da jij maganar wata irin tsanar Addah yaji tana saukar masa shidai tunda ya auri Fatu bazece ga wani abun Alkahiri daya same shi ta dalilin ta ba a kullum cikin jefa shi a masifu kala kala take.

Kiran wayar Binta na shiga ya daga, ba maganar gaisuwa ta shiga rattaba masa cewa
"Alhaji ka kira Addah duk inda take ta dauki Ummi tana kuka da komai sun tafi tackaita a zubar da ciki kar yarinyar nan ta mutu mu shiga uku ka kirata ka dakatar da ita".

Wata zufa yaji tana sakko masa, kiran wayar Addah ya shigayi tana ringing amma bata dagawa seda ya kirata sau goma a na sha daya ta kashe wayar. Babbar rigarsa ya cire saboda yanda yaji tana neman shaqeshi ya ringa safa da marwa a cikin shagonsa yana ayya na irin wulaqancin da zeyiwa Fattu a wannan karon, tabbas yakai bango kuma dole ya dauki matakin da ze shigar da ita hankalinta.

Wayar Amirah ya shiga kira ringing biyu ta daga tana gaishe shi, be amsa mata ba cikin kakkausar murya yace mata

"Ki kira uwarku ki gaya mata wallahi idan wani abu ya samu Ummi a sanadiyyar zubar da cikin data tafi kaita se na daureta dauri har qarshen rayuwarta sannan ki gaya mata daga inda ta tafi karta dawo mun gidana na saketa saki biyu" yana gama fada matan ya kashe wayar sa.

Sosai zuciyarsa take tafarfasa, Addu'arsa Allah yasa kar wani abu ya samu Ummin dan wallahi bega wanda ze hana shi shari'a da Fattu ba.

Hajia Addah kuwa Napep suka haye se gidan Hajia Balaraba suna tafe a hanya tana surfawa Ummi zagi har suka isa.

Ta tarar da Hajia Balaraba tana wanka dan haka suka zauna a palour suna jiranta ba adauki lokaci ba kuwa se gata ta fito daga dakinta a kallo daya Addah ta hango irin yanda tayi sanyi laqwas kamar ba Balaraban data sani ba mace me izza da taqama.

"Aa Fattu kece yau a gidan namu yaushe rabo" Balaraba ta fada tana zama akan kujera, se Addah ta tabe baki kafin tace

"Zaki fadi haka mana tunda kin samu yanda kike so kij watsar dani bayan da kika kaini gidan dan damfara ya cinye mun kudi ai dole kice yaushe rabo, ni ba wannan ta kawo ni ba ma.

Likitan da ya cirewa Sarai qanwar ki ciki zaki hadani dashi wannan tsinanniyar yarinyar taje ta kwaso mun abun kunya dama yana qare da maqiya ballantana yanzu ta janyo mun abun magana a ringa nunani a gari"

"Kai kai Fattu ki bari dan Allah, irin wadannan mugayen kalaman da muke jifan yaran mu dasu su suke tasiri akan su suke lalatasu.
Ummi a garin yaya me ya kaiki irin wannan abu ke da nake yiwa kallon nutsatstsiya ko yar uwarki da take da rawar kai ta gama yammatancinta lafiya Me ya sa Ummi" Hajia Balaraba ta fada cikin Jimami.

Ummi ta qarawa kukan ta volume tana cewa "Wallai Hajia sharrin shaidan ne kuma da laifi Addah, seda na gaya mata ga wanda nake so tace ko zan mutu bazan aure shi ba"

Duka Addah ta kai mata tana cewa "Na fada din yanzu ma na maimaita ko zaki mutu bazaki aure shi ba shegiya da bata san ciwon kanta ba.

Ke kuma ni ba mayar da zance ne ya kawo ni ba ki bani lambar waya ko Adireshi na tafi dan a yau nake so ayita ta qare kafin maganar taje kunnen ubanta".

"Cikin wata nawa ne?" Balaraba ta fada tana janye tagumin da tayi, se Addah tayi caraf ta ce

"Ko wata tara ne se an cire shi babu ruwanki kawai nidai ki hadani da me aiki badai maganar kudi bace zan bayar ba matsala"

"Dan Allah Hajia karki barta ta kaini cikin fa wata hudu ne wallahi mutuwa zanyi Nasan gara ta barni ko a gurin haihuwarsa na mutu nasan nayi shahada Allah yasa haka ya zamar mun kaffara" Ummi ta fada tana sake rushewa da kuka, se Addah tayi kanta da duka Hajia Balaraba ta shiga tsakani tana bata haquri

"Fattu Yarinyar nan tafiki gaskiya, ko sarai da kikaga a lokacin munje an cire wata biyu ba'a ko busa masa raiba magani kawai ya bata tasha cikin ya fita amma wannan wata hudu fa, kisan rai zakiyi qarshe idan ba'a dace ba itama a rasata gaskiya kiyi haquri ki dauki qaddarar data zo miki a haka tunda ke kika jawowa kanki. Yarinya ta kawo mijin aure kinqi ai dole ki karbi duk sakamakoj daya biyo baya kuwa".
Chapter 106 · 0% Book details