← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 158

Sashe 43

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru nayi ina shafa kansa, wato a gabansu ma ya fadi haka kenan, tabbas shi ya bada qofar da yaran zasu ga baqin sa ko bayan haka yana sane Aliyu ai photocopy dinsa ne daman, duk wani hali daya ke taqama dashi Aliyun ya kwasa harda qari dan badan ma Irinta Allah ya bawa Aliyun a matsayin uwa ba da ba qaramin wuyarsa za’a sha ba.

Numfashi naja kafin nace “koma menene karna sake gani, Abbinku yana sonku ka sani irin son da yakeyiwa Iman, ba fata ba yau ko daya daga cikin mu ya rasa irin damuwar da ze shiga kenan kasan halinsa kuma idan yana cikin damuwa Fada yakeyi da kowa. Dan haka ka kiyaye Aliyu karna sake jin wata magana irin haka kaine babba komai kayi qannenka suna koyi da kai ko so kake Allah yayi fushi daku kuna sabawa mahaifinku?”

Girgiza kai yayi a sanyaye, na ci gaba da cewa “yawwa Haidar dina kar a sake, gobe kuma ka same ahi ka bashi haquri kaji ko dan yanzu dai be huce ba”

“Insha Allah Mami bazan sake ba” ya fada.

“Yauwa Allah yayi muku albarka ya kulamun da rayuwarku”
“Amin Mami, I kove you”
“I love you more” na fada tareda kissing goshinsa kafin na ja masa bargo na fita.

Seda na lallaba sauran suka cire uniform na dora farar shinkafa dan ina da miya na barwa Amna ta duba sannan na tafi dakin nasa.

Ina tura qofar yana sako kai ze fito, ya watsamun kallon banza na mayar masa da martani na shige se ya biyo ni yana cewa “Wato daman abinda kike gayawa yaran nan kenan kina koya musu mugun hali har Aliyu yana fadar na fi son Amirah akan su ko?”

Banza na bawa ajiyarsa, na jawo drawer dana saka folder na dire masa akan gadon kafin na miqe na nufi qofa.

“Ma’u” ya kira suna na kafin yaci gaba da cewa

“Wato Ma’u kin rainani, saboda wulaqanci da rashin mutunchi ina miki magana shine kika sa kai zaki tafi bayan tara yayana da kike yi kina cusa musu tsana ta a zuciyar su ko?”

Tsabar mamaki daskarewa nayi a guri daya na kasa gaba na kasa baya, wace kalar kwaya Bashir yasha ne? Ko kuma rasa Ÿa hauka ne ko a kansa aka fara, kai da alama dai kawai Bashir ya shirya ci mun mutunchi ne idan ba haka ba ya gama jibgar mun Da sannan ya kalleni yace wai ina masa wulaqanci da rashin mutunchi, waiwayawa nayi na gyara tsayuwata sosai ina kallonsa

“Wulaqanci ko rashin mutunchi ba tarbiyyata bane dan da ace na iya da bamu kai shekara goma sha shida tare da kai ba, batun in tara yaran ka kuma in cusa musu tsanarka..” na dan dakata tareda qara taku biyu na dawo gabansa sosai, murmushi nayi me kama da yaqe kafin na ci gaba da cewa

“Base na zugasu akan ka ba, yanda kyakykyawar mu’amalarka gare su ta sa suke sonka haka sababbin halayen daka tsiro dasu zasu bi su goge duk wannan so da shaquwar da kake gani a tsakanin ku, sannan kayi a hankali duk abinda yaro ya gani a gurin iyayensa tarbiyyar da ze tashi da ita kenan musamman kai me Ÿaya maza zasu tashi su zata abin kirki kake aikatawa kaga haka zasu tafi da matan da.....”

“Ya isheki Asma’u” Bashir ya katse ni cikin hargagi tareda daga hannunsa ya nufoni da niyyar mari, sedai ko me ya tuna ya janye tareda kaiwa Bangon dayake bayan mu naushi sannan ya juya ya dafe kansa yana huci kamar wanda ya hadiyi kunama.

Tabbas na tsorata, na kuma saddaqar sheya shararamun mari a yanda ya nufo ni amma taurin zuciya da dakiyar dana dorawa zuciya ta bata sa baki na ya mutu ba,

kallonsa nayi da kallon da ni kaina bazan iya fassara shi ba, na tsana ne ko na takaici da baqin cikin abinda Bashir yakeyi mun nace

“Nima dukana zakayi kamar yanda ka kusa illata danka gashi can kwance, to ka tabbata hakan shine abu na qarshe da kwakwalwarka zata raya maka akaina dan wallahi Bashir sekayi dana sanin dora hannunka a jikina da sunan duka, har Mahaifina ya koma ga Allah ban taba ganin ya dagawa daya daga cikin matansa murya ba ballantana har ya dake su se kai kake tunanin zaka daki yar sa? Toh bismillah” na fada ina zare masa ido kamar wani dana.

Naga alamar se nayi masa haukan gaske sanann ze shiga hankalin sa, wata irin tsanar Amirah ce tayi mun dirar mikiya dan itace sila, ita ta janyo komai da yake faruwa da be aure ta ba da haryanzu muna cikin zaman lafiyar mu da qaunar juna amma tunda ta shigo rayuwar mu abubuwa suke rinchabe mana bamu taba rufa sati ba tareda munyi tashin hankali da Bashir ba.

Shiru mukayi gaba daya, ni ina jiran ya sake wata magana ko yunqurin marin nawa dan wallahi sena gwada masa nima yar buyagi ce yau amma se yai shiru, kiran Sallar Magriba ya sakashi shigewa Toilet ya bugu qofar da qarfin gaske se na bishi da harara kafin na ja dogon tsaki na fice daga dakin.

Seda na tashi Aliyu na sake bashi awa paracetamol bayan yaci abinci yayi sallah kafin bacci ya sake dauke shi, gaba dayan su basu da walwala haka na daure na ringa tausarsu har sukaci abinci sunayin sallar isha kuwa kowa ya nemi makwanci sa har yan biyu da suke qanana sun shiga nutsuwarsu dan Muhammad dayaga Bashir ya fito daga dakinsa ze shiga Kitchen ma kuka ya saka ya rirriqe Jafar.

Ina kallon yanda yai turus yana kallon yaron, duk da fuskarsa bata nuna ba amma jikinsa yayi la’asar daga gani cike yake da nadamar abinda ya aikata amma izza irin tasa bazata barshi aga gazawarsa ba.

Palour na dawo na zauna bayan duk sun shiga daki ina jiran kota kwana, jira nake naji ko Bashir zece na bashi abinci ko ya sake gayamun wata maganar banza a daren nannayi masa wankin babban bargo amma shiru har sha daya ina zaune ban sake jin motsinsa ba.

Dakina na shige nayi wanka, Idona sun soye bana jin bacci dan haka nayi Alwala nayita jera salloli ina kaiwa Allah kukana har seda gabbaina suka gaji kafin na kwanta ina ci gaba da jan carbi.

Nayi niyyar washe garin na kira Amirah da Addah nayi musu gaisuwa amma wallahi na fasa, na kuma shirya duk wanda ya sake bude baki ya gayamun zancen banza a gidan nan bazan daga qafa ba sena gaya masa na wofi.

Da safe ban jira shi ba na shirya yara na kaisu Makaranta a motarsa daya bar Key akan Dining be dauke ba. Tare muka fita da Aliyu bayan na bada excuse din bashida lafiya na wuce dashi Asibiti aka sake duba shi suka rubuta masa magani muka dawo gida.

Ina Kitchen ina dama masa wa Aliyu custard naji fitowar Bashir daga daki, sena dawo bakin qofar na leqa tareda kasa kunne ina jin Aliyun yana gaishe shi, se ya amsa harda tambayarsa yaya jikinsa yace da sauqi.

“Abbi kayi haquri bazan sake ba” naji Aliyun yana fada, se Bashir yace

“Ya wuce Aliyu kaima kayi haquri ina cikin fushi ne na dake ka gashi har naja maka ciwo, kaci abinci muje na kaika Asibiti a duba ka” Bashir ya fada, se Aliyun ya nuna masa ledar magungunan da muka siyo yace

“Mami ta kaini yanzu ga magani ma an bani”

“Ok Allah ya qara sauqi, ka huta sosai kaji bari naje office nakai papers din nan.

“Yawwa yaron kirki ga shi tashi kasha” na fada ina ajiye masa.

Nida Aliyu muka wuni a gidan ya warware har yana tayani aiki munata hirar mu, qarfe hudu har na kira Uber zan tafi dakko yara se gasu sun shigo wai Driver Office dinsu Abbi ne ya dakko su.

Bashir ne dawo gidan ba se 9 na dare, muna zaune muna kallo ya shigo da sallama hannunsa dukka biyu da ledoji, Kallon cikin ido mukayiwa juna kafin na janye nawa ina tabe baki yara suka tashi suna masa sannu da zuwa ya amsa ya basu ledojin hannunsa manya guda biyu ya wuce da qaramar dakinsa.

Be dade da shiga ba ya kwalawa Aliyu kira ya tashi ya tafi sauran suka bude ledojin, tarkace ne kowa Abinda yafi so ya siyo masa, indai yaudara ce ya kware daman, ya zuga rashin mutunchi sannan ya siye ka da abinda yasan kana so. Ina jinsu suna tsallen murna banbi takansu ba.

Aliyu ne ya fito ya debi abinci a plate ya hada da ruwa da cup akan Try yaje ya kai masa ina kallonsa ban ce masa komai ba ya sake dawowa ya debi zobon dana hada ya kai masa.

Da gudu ya fito daga dakin yana tsalle da ihun murna na waiwaya ina cewa “kai meye haka zaka zo kana mana ihu akai”

“Kukalla ku kalla” ya fada yana daga kwalin wayoyi iphone X guda biyu, Amna ya jefawa daya kafin ya zauna cikin zumudi ya shiga bude ta hannunsa.

“Yaya waya aka siya muku” Jafar ya fada yana komawa kusa dashi,

“Wallahi Mamai waya ce, yeee munzama yan gayu muma Faree mun samu tayim snap” Amna ta fada tana daga wayar tata Fara ta Aliyu Baqa. Duk su biyun suka dawo kusa dani suna nuna mun, na karba ina cewa “iye yan gatan Abbi gaskiya kun gode Allah ya sanya Alkahiri ya sa lafiya ta kashe”.

Gaba daya sun cika gurin da ihun murna, sun dade suna nacin a siya musu waya amma yaqi yace se sun gama secondary school idan zasu kira abokansu sedai su karbi tawa ko tasa kowannensu dai yana da Laptop itama dan dokar makarantar suce amma yanzu da yake neman shiri yake da yaran shine ya siyo musu da kansa, Bashir kenan.

Ana tsaka da murnar ya fito da plate din abincin, Jafar ya tashi da gudu ya karbo yana cewa “Abbi mufa, se yaushe za’a siya mana?”
Chapter 43 · 0% Book details