Sashe 95
Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Allah karka jarabce ni da wannan, Allah ka sani bazan iya dauka ba, nayi kuskure Allah dan darajar Annabinka Muhammad SAW kayi mun sassauci karkasa wannan ya zamo mun qaddadar da bazan iya dauka ba Allah karka rabani da Asma'u" sambatun da ya ringayi kenan shikadai kamar zararre, wayarsa ya zaro faga aljihu ya fara laluban numbobi, waze kira ya gayawa damuwarsa? Waye ze bashi sharar yabda ze gyara wannan kuskuren tun kafin dare yayi masa.
"Bala" hannunsa ya tsaya akai, ba bata lokaci kuwa ya dannan masa kira cikin Sa'a bugu biyu Balan ya daga yana cewa
"Engineer Mijin Asma'u, na Amirah ko dubu ta taru"
"Bala akwai matsala, ina cikin masifa ina cikin tashin hankali ka taimaka mun ka gaya mun yaya zanyi na fita wallahi zan iya rasa raina Bala akan wannan tashin hankalin" Bashir din ya katse Bala kamar ze fashe da kuka ko da yake tuni ma ya fara na zuciya kawai dai hawayen ne suka qi fitowa a fili".
"Subhanallahi Bashir meya faru badai korar ka akayi daga gurin aiki ba?"Bala ya fada
"Wallahi gara na rasa aikina Bala, gara na bayar da komai dana mallaka a rayuwa ta da abinda nake shirin rasawa"
"To menene meyake faruwa kayi mun bayani yanda zan fuskanta se musan ya zamu kamo bakin zare wane abune haka daya fi dukiya muhimmanci a gurinka Bashir?" Bala ya sake tambayarsa a tsorace dan gaba daya kalaman Bashir din firgita shi sukayi.
"Asma'u, itace Bala, Ma'u tafi mun komai zan kuma iya bada duk abinda na mallaka akan fansar ta, Zan iya bada raina akan Ma'u ka sani Bala" Bashir ya fada dakyar dan qirjinsa ya fara yi masa nauyi, wani irin zafi zuciyarsa take masa kamar wadda ake watsawa ruwan zafi, Tsakin da Bala yayi ne ya katse masa tunani kafin Balan ya ci gaba da cewa
"To me Ma'un tayi maka yau kuma yanzu? Kai wai kullum baka da aiki sena kawo qarar Ma'u ne haba ni wallahi na gaji da jin Ma'u tayi Ma'u tace idan ka gaji ka saketa kawai kowa ma ya huta mana".
"Bala na saki Ma'u shine Bala'in da nake ciki a yanzu ta gama iddah kafin na mayar da ita kuma tace bazat sake komawa gida na ba ta gama aure na" Bashir ya fada kamar ze fashe da kuka.
"Kace ka saki Ma'u harta gama Iddah Bashir" Bala ya tambaye shi da son tabbatar da daidai yaji ko kuwa kunnensa ne yajiyo masa abinda ya dade yana fatan faruwarsa.
"Dagaske nake Bala na saki Ma'u saki biyu kuma tayi bari a washe garin ranar dana saketa kaga kenan iddarta ta ciki ka gayamun ya zanyi na shawo kanta ta haqura mu koma auran mu wallahi ina son matata idan na rasata zan iya mutuwa ka sani Bala" Bashir ya sake fada a matuqar raunane.
Bala kuwa seda yayi matuqar qoqari gurin danne farin cikinsa kafin ya aro damuwar qarya ya saka a muryarsa yace
"Ashsha Mutumina ya akayi haka a garin yaya? Amma dai koma yayane aikin gama ya gama yanzu sedai nemi mafita kuma ayi fatan Allah ya kiyaye na gaba.
Kana ji ko ni nasan Ma'u duk fushin da zatayi ba wani me yawa bane kasan irin son da takeyi maka, dan lokaci kawai zaka bata dakanta idan ta sakko zata nemeka ku daidaita kaima kasan duk abinda zata fada buyagine kawai amma Ma'u bazata iya rayuwa babu kaiba kowa ya shaida hakan"haka Bala ya cigaba da dorashi a keken bera har seda ya yarda kafij sukayi sallama.
Suna kashewa kuwa Bala ya daka tsalle yana cewa
"Allah na gode maka, badai kai wawa bane ka raina ni'imar da Allah yayi maka zaka gabe kurenka wallahi muje zuwa yanzu aka fara wasan Ma'u kuwa nasan bazan same ta ba amma tunda kaima ka rasa ko haka aka tashi wasa nayi nasara kuma in sha Allahu bazat taba dawo maka ba".
Allah sarki Bashir shi kuwa Sosai kalaman Balan suka kwantar masa da hankali dukda wani bangare na zuciyarsa yana so yaqi karban hakan dan a yanayin da Ma'u ta nuna tabbas yaga chanje chanje da yawa a gareta yana kuma jin gaskiya ta fada a maganganunta amma yasan so ba qarya ba, ba kuma ya zaton Ma'u zata taba tsanar sa a rayuwa ta bakin Balan zafin abinda ya mata ne ya sakata fadar duk wasu maganganu amma idan ya bata lokaci ta huce yasan zasu daidaita.
Da wannan ya lallashi kansa ya koma kan gado ya qudundune yana so ya manta maganganunta amma ya kasa ga wani irin tsoro da tashin hankali dayake shigarsa a duk sanda ya tuna kalaman ta na dazu har wani zazzabi yaji yana neman kama shi.
Anya ze iya bin shawarar Bala na ya bata lokaci harta huce dan kanta? Ya lura idan mafa fushin tayi ba kadan bane dazu fa har mari yasha, kai ina baze tsaya ya zuba ido yana kallo kwado ya masa qafa ba, a wannan gabar dole ya ajiye girman kai ya kwato Ma'u tun kafin yan iskan mazan Lagos su hure mata kunne.
Haka yaringa hada lissafi yana warwarewa, a ranar dai yanda Bashir yaga rana haka yaga dare sabanin Ma'u da ta shaqi bacci me cike da mafarkai masu dadi.
Washe gari haka ya farka kamar bugagge, ga damuwa ga rashin bacci lokaci daya gaba daya suka nuna a jikinsa seka zata yayi sati yana jinya idan ka ganshi. Amirah ma dai yau ta kama kanta, danfa jiya da daddare jijara yayi mata ta gaske akan taliyar da har daddawa ta saka mata gashi taji kifi amma loma daya Bashir yayi ya ture ya ringa surfa mata cin mutunchi wai bata iya komai ba haka yaran ko dandane basu ci ba suka gudu gidan uwarsu acan suka kwaso abinci tana kallo suka ci suka bata guri kuma haka ta share gudun sake yin wani laifin a gurinsa.
Da safiyar ma harda hawaye seda tayi da tana hada musu abin kari, doya da kwai ta soya sannan ta dafa zallar ruwa ta jefa Lipton ko arziqin kanimfari da citta be samu ba alhalin gasunan tunda ya siyo bata ko kwashe su daga kan inda ta ajiye ba bare ta zuba komai a ma'adanar sa.
Haka ta gama hada abincin nan kafin dukan su su fito, tana tsaye yaran suka fara fitowa tacewa yan biyu suzo suci, harta fara hada musu shayi Aliyu yana fitowa ya kada kansu suka tafi gidan Maminsu suka bar Amirah tsaye tana binsu da kallo tama rasa abin cewa.
Fitowar da Bashir yayi ta sakata waiwaya wa ta kalleshi, a kallo daya ta hango damuwa qarara a fuskarsa amma ina ba wanann ne a gabanta ba, yana zama a Dining din ta dira masa qorafin sunqi cin abinci Aliyu ya jasu sun fita ita dai ya kirasu dan bazata hana kanta bacci tasha wahalar banza ba sannan suqi ci in kuwa ba haka ba zata ajiye musu daga yau har gobe se sun cinye sannan zata sake yin wani girkin.
Bashir daya gaji da jinta, ga damuwar da take kansa ga ta surutun data tsaya masa akai tanayi ya ture plate din data saka masa doyar ya tashi dan daman sam cin yunwa kawai zeyibawai dab ta masa irin yanda Ma'u takeyi ba, jiya beci abincin dare ba, ya fita ya nema ya ga babu motar Ma'u a waje abinda ya kaishi gidan kenan yana tsaye se gata ta dawo yayi wannan mummunan ganin haka ya kwana da yunwarsa gashi yanzu kuma tasa abincin ya fita daga ransa saboda qorafi.
"Yanzu Yaya ina maka magana shine kaima zaka ture ka tashi ni me aka mayar dani a gidan nan ne a tilastani nayi girki sannan aqi ci wallahi bazata sabu ba ba kuma zan iya ba" Amirah ta fada tana shan gabansa.
"Amirah ki rabu dani, ki kuma kama kanki a cikin gidan nan idan ba haka ba zaki ja nayi miki abinda zaki zo kina dana sani tunda duk ke kika jefani a masifar danake ciki, matsa mun daga hanya na wuce" ya fada a hankali amma sautin maganar ya sakata shiga hankalin ta.
Da gani akwai abinda yake damunsa idan kuma ta matsa tasan tabbas zeyi abinda ya furta din dan haka ta matsa masa tana qunquni qasa qasa shidai ya fice ya barta a tsaye.
Yana saka qafarsa a waje idonsa suka sakeyin mummunan gani a karo na biyu, Asma'u ysaye da wani basamuden Beyerabe suna dariya ga jakarta a hannunsa ya riqe mata yana mata alamar da tayi gaba ta shiga motarsa kamar wani saurayi yazo daukar budurwarsa zasu fita ita kuma se washe baki takeyi ta shiga motar yana tsaye mutumin da besan ko waye ba yaja suka wuce Bashir daya dafe motar sa jin jiri yana neman watsar dashi a gurin.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Ma'una ce nake gani a gaban motar wasu mazan daban bayan ni Allah me na tuba ka yafe mun kuskuren da nayi ban butulcewa Ni'imar ka ba wallahi sharrin zuciya da shedan ne suka ingizani" ya fada yana jin ina ma ya samu hawaye ya zubo masa ko ya samu sauqin radadin da zuciyarsa takeyi masa daga jiya zuwa yau, yana tsaye har besan sanda yara suka fito daga gidanta suka shiga mota ba seda Jafar yace masa
"Abbi mu tafi mana karmu makara" sannan ya shiga ya tafa motar, tuqi kawai yake amma ikon Allah ke tafe dasu a haka ya samu ya sauke su ya wuce aikinsa da bashi da tabbacin ze iya tsinana komai yau idan yaje
To Bashir tsautsayi da Asara Allah ya kiyaye 😂😂
Assalamualaikum Barkanmu da wannan lokacin AUNTY ZEE TAKU CE ,Ina uwar gida Amarya da yanmata albishir gareku
BONONZA; BONONZA;BONONZA;
Nazo maku da SAHIHIN MAGANIN CIRE TUMBI CIKIN SATI DAYA ZAKI BAN LABARI,KINCI GAYU ANA TAMBAYARKI YAUSHE ZAKI HAIHU TUMBI YA HANAKI ADO DA KWALLIYA SHA KURUMINKI NAZO MAKI DA MAGANI CIKIN SATI DAYA ZAKI BAN LABARI ZAN DANDANA MAKU SHI AKAN RABIN KUDINSHI DAGA NAN ZUWA SATI DAYA 7K DUK ROBA DAYA KI BIYA 3500 KI MALLAKI NAKI NAN DA SATI DAYA ZAI KOMA 7K