← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 158

Sashe 54

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bansan ya suka qare da Amirah ba nasan dai ta tafi, dukda abinda ya aikata ai ba laifi bane ko babu komai ai matarsa ce daman ai yana da ikon kaita ko ina amma yanda ya biyo da abun ne babu tsari a ciki. Dan haka fushin kwana biyu na qara kafin na ware muka koma daidai kamar bamu samu wani saba ni ba.

Amirah
Da baqin ciki da takaicin Ma’u da Bashir ta koma Gombe, har kuka tayi sanda take labartawa Addah abinda ya faru.

“Se kinga yanda ya rikice Addah harda durqusawa yana bata haquri a gaba na ita kuma se yankwana shi takeyi saboda ta nunamun ta isa dashi. Saboda wulaqnaci fa gidan Ghali ya turani na qarasa kwana sannan da zan taho ma Taxi yasa ta kaini Airport se a waya mukayi sallama”.

“Tab lallai Asma’u ta gawurta yanzu Bashir din ne ya duqa mata, lallai dole mu sake tashi tsaye. Ni ina ganin komai yayi lafiya yanda kwana biyun nan aketa abin arziqi ashe da sauran rina a kaba” Addah ta fada tana kama baki.

“Ai wallahi bata ci bulus ba, yanda ta rusa mun tsarina nima sena rama” Amirah ta fada, daga nan suka shiga qulle qullen yanda zasuyi su rama abinda Ma’u tayi mata.

Lagos
Ranar Juma’a data kama litinin a koma makaranta Amna da Farida suka dawo, ban gayawa Bashir ba na saka Naziru ya siya musu Tickets dan daga Yola Gombe aka kaisu se ganinsu kawai yayi ai kuwa ya ringa masifa akan me zan doro masa yara a jirgi su kadai me yasa ba’a gaya masa yau zasu dawo ba yaje ya taho dasu ko shi Nazirun ya rako su nidai nayi banza dashi tunda sun dawo ai magana ta qare.

Monday qalau muka rabu kowa ya tafi aikinsa ranar na dan jima a office saboda shirin Tafiya Abuja da mukeyi wani conferees se bayan Magriba na shigo gida. Seda mukaje kwanciya sannan nake gayawa Bashir dan saura sati daya tafiyar.

“Lallai Big woman anya nima bazan zo a dan sama mun guri ba naga fa kuna kwasa da yawa a office din nan naku” ya fada da dan murmushi yana danne danne a wayarsa, sena gyara zama ina cewa

“Kaidai bari wallahi yanzu ma fa package din tafiyar nan naji Accountant yana cewa kusan 700 huns za’a bamu each kudin TP da accommodation ni daman gidan Alhaji Qarami zan sauka kaga sena soke kudina, Goggo nake so ma na biyawa Umarar Azumin su tafi tareda Maman Ayman”.

“Hakan yayi kyau, nima idan na samu yanda nake so se mu tafi da ke ita kuma Amirah se taje Hajji”.

“Allah ya yarda toh” na fada sannan muka ci gaba da hira har bacci ya dauke mu.

Weekend din daya kama satin da za’a shiga zanyi tafiyar ranar Asabar da daddare na sake gaya masa zancen tafiyar base ranar Monday ya ganni da jaka ba.

Yana zaune na kawo masa coffees da yace yana so nake masa zancen ina cewa “Allah ma ya taimake ni Amna na gida yanzu da bansan yanda zanyi tafiya harta sati guda ba”.

Shiru ya mun yaci gaba da shan coffee dinsa nima se na mayar da hankali na kan Tv seda ya mula dan kansa se cewa yayi “wai dole ne se kinyi tafiyar nan?”

Ban waiwayo ba na bashi amsa “Kaji Baban Ali da wata magana, tun fa last week na gaya maka, me ze kaini toh idan ba dole ba”.

Tsakin daya ja ne ya saka ni waiwayawa na kalle shi, fuskar nan a mugun hade seda gaba na ya fadi dan rabon da nagan shi a irin haka an kwana biyu.

“Lafiya” na fada ina gyara zama na fuskan ce shi da kyau, se ya miqe kawai ya shige dakinsa nima na rufa masa baya.

“Kibar tafiyar nan kawai dan bazan iya zama har sati guda ni kadai ba” ya fada yana cire rigar jikinsa da alama wanka ze shiga. Sena marairaice cikin lumana ina cewa

“Haba Engineer satin fa kamar yaune qilan ma baza mu kai haka ba, kayi haquri ka daure In Sha Allah gaba idan haka ta taso zan nemi a chanza wani dani amma yanzu lokaci ya qure kaga jibi ne fa tafiyar”

A maimakon ya sakko se nagama kamat fetur na qarawa wutar dan hargagi ya shiga yi mun yana cewa “nidai na gaya miki kawai, ke ni aikin nan ma gaba daya bana sonsa daman idan mace taga tana samun kudi gani takeyi kanku daya tunda babu abinda zata nema a gurinka, kai ta yaya ma za’ayi mutum yana da mata amma ta tafi wani guri tayi har sati daya meye marabar sa da gwauro” bam ya shige Bandaki ya bugo qofar sena rakashi da ido kawai ina karanta Hasbunallahu wani’imal wakeel a zuciyata.

Abin ya motsa kenan, haka naja jiki a sabule na fice na koma dakina. Rasa wanda zan kira na gayawa wannan abu nayi ina zaune sega kiran Babbar yayar mu a dakin mu Anty Suhaima da take America ta kirani.

Bayan mun gaisa mukayi shiru dan babu sabo sosai tsakanin mu saboda ita da wuri tayi aure ta auri dan Abokin Baffan mu yan Kano ne a lokacin Baban sa shine Ambassador na Nigeria a America dan haka tunda tayi aure can aka kaita kusan shekara Ashirin da biyar yanzu.

Jin shirun naw yayi yawa ya sakata cewa “Ma’u lafiya kuwa kamar akwai abinda yake damun ki” haka kawai naji kuka ya taho mun ba kuwa ta hanani ba ta barni na yi abuna seda nayi shiru dan kaina kafin na gaya mata yanda mukayi da Bashir.

“Daman baya son aikin naki tun farko ne ko yaya” ta tambaye ni,
“Wallahi Anty be taba nuna baya so ba, tun ma ba yanzu ba kinsani kafin wannan nayi wau qananun ayyukan kuma be taba hanawa ba a koda yaushe yana bani goyon baya, yanzun mafa ya yarda yau ne kawai dana sake gaya masa zancen tafiyar shine kuma ya bullo da wannan maganar”.

“Shikenan, ki rabu dashi ki ci gaba da Addu’a zuwa goben ku sake maganar idan be yarda ba ki haqura karki tafi ba tareda izinin sa ba idan yaso ki gayawa Alhaji qarami se aji me yake nufi da aikin naki daman ai zaman aure dole akwai qalubale Ma’u Allah dai ya sa mu dace kawai” nasiha taci gaba da yi mun kafin mu ka gaisa da yaranta dukka su hudu sannan mukayi sallama bayan na tura musu da Number Aliyu da Amna da suka ce.

Ban koma dakin Bashir ba a zato na kuma ze biyo sahu amma har dare ya tsala naji shiru.

Da safe na sake tun kararsa da maganar se kuwa cewa yayi “In dai izinina kike nema toh ban yarda ba” ya sa kai ya fice daga gidan.

Yana fita na dannawa Dadan su kira dan kuwa bazata sabu ba, tas na gaya mata yanda mukayi tace na kwantar da hankali na zata masa magana, ilai kuwa da daddare ina zaune se gashi fuskarsa nan kamar Hadari yace

“Wato qarata kika kai Gurin Dada ko? Shikenan kije amma ki tabbata sena dauki hukunci akan hakan”.

“Tunda dai ka barni ai zance ya qare” na fada bayan daya fice daga dakin, washe gari na cale zuwa Abuja bayan na barwa yara komai da zasu buqata karma ya huce haushi na akansu.

Amirah
Sosai ta kunnowa Bashir wuta tunda ta fuskanci shi mutum ne me son a girmama shi ba kuma yason raini se tayi amfani da wannan damar gurin nuna masa ai Asma’u ta raina shi kuma abinda take nuna wa mutane kenan cewa tafi qarfinsa.

Da Samirah qanwar sa suka shirya komai dukda ita Samiran bata san amfani da ita Amirah tayi ba. Tana zaune ta kirata take bata labarin abinda ya faru ai Bashir ya durqusaw Ma’u, Smairah kuma irin masu dan banzan surutun nan ne idan taji abu kamar dukka dangi kowa yaji ne dan haka kafin kace me wannan Labari ya karade kowa kamar wutar Daji cikin haka maganar ta koma kunnen Bashir.

Amma saboda rashin Adalci irin nasa a maimakon ya ji haushin Amirah data fada tunda a gabanta akayi se laifin ya koma kan Ma’u a cewarsa da batayi masa boren da tayi ba ai da be durqusa matan ba har Amiran ta samu abin yayatawa ba wannan fushin ya qudure a ransa.

Kwana biyu tsakani har ya huce tayi masa zancen biyawa Goggonsu Umarah se akayi dace washe gari Bala ya kirashi, suna cikin waya yake ce masa

“Mutumina ashe Ma’u ta siyi gida nan kusa damu, jiya mun zagaya ta gurin naga gidan hadadde nake tambayar na waye akace na matar ka ne kamar ma guda biyu ne fa ko Su Aliyu ta siyawa ne”.

“Anya kuwa Ma’u ta siyi gida ba tare da na sani ba me zatayi dashi, ina ga dai ba nata bane sedai wata daga cikin yan gidan su ko” Bashir ya fada.

“Lallai Bashir baka san mata ba, ka manta lokacin baya kenan yanda yan uwanta suka tinga zugata akan karta doraka akan dukiyarta. Yanda take karbar kudin Hayar gidajenta ga Albashi me tsoka ai dole ta ringa siyan kadarori tana boyewa baka sani ba,

nifa wallahi nama ga baikenka kana zaune na tabbatar yanzu ta ninkaka sau uku a arziqi wallahi in bakayi wasa ba kwanan nan zaka zama mijin Hajia se yanda tayi dakai tunda tafi qarfin komai babu abinda zata nema a gurinka.

Da zaka ji ta tawa ma kasa ta ajiye aikin nan wallahi dan tana dab da finka Albashi bashi ne taqamarka ba”.

Wadannan maganganun na Bala dana Amirah su suka yi tasiri a ransa dan yana ganin abinda Balan ya fada gaskiya ne.

Tunani ya shigayi Rabon da ya dauki kudi ya bata ma shi harya manta daidai da kudin sati na man mota da yake bata yafi wata shida be bayar ba kuma bata tambaye shi ba.
Chapter 54 · 0% Book details