← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 158

Sashe 56

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Shi yasa fa na rubuta maka komai dalla dalla da kudinsa karma kace qari nayi maka ko wani abu” na fada ba tareda na kalle shi ba, seda yaja wata qwafa kafin naji yace

“Yanzu kudin zan baki kenan?”
“Ka siyo da kanka ma duk daya ne ai” nayi saurin katse shi. Beyi magana ba mintina kadan naji wayata tayi qara alamar shigowar message na jawo na duba Alert ne na dubu dari da Hamsin daga Bashir nayi murmushi nace
“Sun shigo harda qari ma muka samu toh mungode Allah ya qara budi”.
Washe gari ya tafi Gombe.

Weekend din a daddafe nayi shi dan gaba daya bana jin dadi, zazzabin dare ne yake damuna safiya nayi kuma naji garau na bari akan Monday idan be dena ba zanje Asibiti.

GOMBE

Wato wata Irin ladabi da biyyaya Amirah ta ara ta yafawa kanta wanda duk hudubar Sa’ada ce. Jikinta na bari Daman yanzu da yace zezo zataje ta qalqale gida a gyara ko ina dukda dai da taimakon Ummi harda Sa’adan ma suke zuwa wani lokacin sannan idan yazo tana iya qoqari tayi tsafta harya tafi a bangaren girki ne dai har yanzu da saura yana ci yana qorafi dan baya masa kamar na Ma’u.

Wannan zuwan da yayi sosai yaji dadinsa ga tarairaya yana samu da kula kamar wani jariri babu aikin office babu hayaniyar yara.

Butulci irin na dan Adam a yanzu se yake ganin Yafi samun yanda yake so a gurin Amirah musamman da yanzu ta dena masa qorafin da tambaye tambayen kudin da takeyi gashi a karan kanta ta canza sosai komai tana yi yanda yake so.

Suna zauna ana gobe ze tafi tana bare masa Ayaba yana ci ya kalleta yace “kina son zuwa Lagos?”

Sam Amirah bata kawo da ita yake ba dan a bazata maganar tazo mata har seda ya sake maimaitawa kafin tace “Meze hana mana Yaya ai kowacce mace zata so ta zauna kusada mijinta daman, wani gidan zaka samar min kenan”ta fada tana danne zumudin ta, lallai ta yarda kissa tafi Asiri tunda gashi yanzu hankali kwance tana samun abubuwan da suka wahala suka kashe kudinsu a banza akansu.

“Aa ina ganin zaku ringa karba karba ne dan baze yuwu na ajiye ku gaba daya acan ba”.

“Toh Anty fa ya zatayi da aikinta” ta fada tana gyara zama a ranta tana Addu’ar Allah yasa matsala suka samu daman ta lura tunda yazo bata ga sunyi waya ba.

Seda Bashir yasha ruwa kafin yace “Ina ganin zata ajiye aikin ne kawai idan yaso ta cigaba da kasuwancinta kema ya kamata ki samu wani abinyi zaman haka ya isa”.

Tamkar Amirah ta taka rawa haka taji amma ta dake, cikin kisisina tace “Toh yaran kuma fa su acan za’a barsu ko suma nan zasu dawo?”

“No su zasu zauna can saboda School”

“Amma Yaya indai makaranta ce anan ma fa akwai ko wacce iri kake so, ni ba wannan ba ma abinda yafi damuna Tarbiyyar su kasan fa yaran da suka tashi a Kudun nan duk zaka gansu se a hankali ko a gida ana musu tarbiyya tunda kullum suna fita su cakudu da yara kala kala se kaga anayi tana warwarewa. Ni da zakaji shawarata ka dawo dasu nan ga makarantu nan na kudi masu kyau a saka su”.

Shiru Bashir yayi yana tunani, baza’a hadama karantun boko nacan da na nan ba amma maganar tarbiyya tabbas tayi gaskiya abinda yasa ya hana Amna yin Jamb wannan shekarar kenan yace ta bari se next year saboda kafin nan ta dan qara girma da wayo yana tsoron turata Jami’a cikin Yayan Arnan nan.

Su kansu su Aliyun yasan badan Ma’un ma Jajirtacciya bace irin yaran da suke cakude dasu a makaranta da sun debi dabi’un da ba nasu ba.

“Haka ne kuma, shikenan zanyi magana da Ma’un se muga yanda za’ayi”.

Litinin ya koma Lagos da wannan qudurin a ransa. A daren ranar suna cin abinci bayan ya gama ya kalli Asma’u da tunda suka zauna ta kasa cin komai yace “Inason magana dake idan kun gama” ya wuce dakin sa.

ASMA’U

Yana tashi nima nabi bayansa gaba daya jikina baya mun dadi dan haka ina shiga na kwanta akan gado ina jiransa ya fito daga yin Brush.

“Daga Next month Amirah zata fara zuwa nan”.

“Wata sabuwa” na fada a raina, sena miqe zaune ina kallonsa nace “toh ni mene ne nawa a ciki idan Amirah zata zo ko a nan gidan zata sauka ne?”

“Ina nufin ke zaki tafi Gombe idan zata zo, then se ku tsara yanda kuke ganin lokacin da kowacce zata ringayi a nan din”. Ya fada yana zama a gefena.

Yanzu kam na gane inda ya nufa, wato tsohuwar magana ce ta taso kenan yaje ta sake masa fanfo akan tanaso ta dawo nan. Zaune na tashi na jingina bayana da Allon gadon nace “Toh Baban Ali ya zanyi da aiki na kuma? Sannan Yara suma ya za’ayi dasu?”

“Maganar aiki na gaya miki zaki ajiye daman yara kuma dasu zaku tafi duk wadda take Gombe se su zauna a gurinta”.

“Kan uban nan lallai ma” na fada ina kallonsa kafin naci gaba da cewa
“Yanzu saboda matarka tana so ta dawo nan shine zakace na ajiye aiki na amma kasan sam wannan ba adalci bane ko?”

“Ke zaki koyamun yanda zanyi adalci kenan, toh ki dauka duk yanda yayi miki amma na gama magana dole ki ajiye aikin ki Ma’u ki koma Gombe tunda haka na tsara” ya fada yana kallona.

Seda na qare masa kallo dan na tabbatar da gaskiyar abinda yake fada kafin na sassauta muryata ganin dagaske neman rigima yake nace

“Haba Baban Ali, ka manta wuyar dana sha kafin na samu aiki nan, mutum nawa ne suke nema Allah ya zabe ni akan su ya bani amma yanzu lokaci daya kace na ajiye. Da ace muna da Branch a Gombe da babu musu zan nemi transfer in koma can amma yanzu kawai dan kana so ka kawo wata ni kuma seka tauyeni kace na bar aiki na ai bakayi mun daidai ba.

Ni bani da matsala zaka iya dawo da ita ko a cikin gidan nan ne ka bata daki amma dan Allah kabar maganar aikina ina son sa ban kuma shirya barinsa a yanzu ba”.

“Shikenan tunda kina son aiki ki, seki zaba ko shi aikin ko kuma umarnina” yana fadar haka yaja bargo ya rufe har kansa nima sena fice nabar masa dakin.
Sam abin ma dariya ya bani lallai akwai match me zafi a gidan nan to Allah ya bawa me rabo sa’a.

Washe gari tsaf na shirya zan fita aiki, ina tsaye ina barwa Amna sallahun abinda zata girka ya fito muka kalli juna se cewa yayi

“Kiyi mun tuwo da miyar Kubewa da rana za’a zo a karba”

“Naman rago zaki sakawa Miyar Akwai soyayye ma a Freezer seki diba” na fada ina zuge jaka ta dan duk a zatona da Amna yake seda naji yace

“Dake nake ba ita ba, daga yau ma karta sake yimun girki kuma kullum za’a ringa kaimun lunch office” yana gama fada yasa kai ya fita na bishi da saurin. Sanda na fito yana tsaye a jikin motarsa.

“Ban fahimci abinda kake nufi da nayi maka lunch ba ka manta zanje aiki ne” na fada ina kallonsa, idan ya amsa ni to motar sa ma tayi magana, ya kunna mota ya bata wuta, harya taka ya leqo ta window yace
“Banyarda ki dara qofar gidan nan ba” ya qarawa motarsa wuta ya barni a tsaye.

Kamar mara laka haka naja qafafuna na koma cikin gidan, akan kujera na zube ina sauke numfashi, dagaske dai Bashir yake ya na so ya rabani da aikina kenan. Badan ina tsoron Allah da fita zanyi sedai duk abinda ze faru ya faru amma yau zan haqura idan yaso ya dawo naji me yake nufi dani tukunna.

Anty Suhaima na kira ina kuka na shaida mata komai tunda daman da ita muka fara maganar ai, haquri ta bani tace yanzu zata kira Alhaji qarami ta gaya masa duk yanda mukayi zanji ba’a rufa awa guda ba kuwa sega kiran Alhaji Qaramin.

Shima din nasiha yayi mun akan na kwantar da hankali na shedan ne kar mu bashi qofar da ze farraqamu ya tabbatar mun kuma ze kira Bashir din yayi masa magana.

Ban san yaya sukayi ba dan daya dawo be kulani ba fuskar nan dai kamar ta shanu haka muka kwana kamar abokan gaba. Washe gari dan na gwada Sa’a ta na shirya kuma akayi dace tafi kuma mutu be ce dani ba hakan yayi mun dadi alamu sun nuna sunyi magana da Alhaji Qarami kenan kuma ya barni naci gaba da zuwa aiki.

Haka muka cinye sati biyu cir ana wannan yanayin duk iyakar qoqari inayi gurin kyautata masa dayi masa duk abinda nasan yana so amma kallon banza ban ishi Bashir ba bare na arziqi haka idan zan kwana ina masa magana baze daga kai ya kalleni ba ko wani abin yake so sedai ya kira daya daga cikin yaran yayi masa.

Abinda na lura dashi shine harda zugar mutane a cikin abun nasa kuma daman na san Bashir halinsa ne daukar shawarar wasu indai ka gaya masa abinda yayi daidai da ra’ayinsa tofa shikenan.

Haka dai nake lallabawa ina taka tsantsan da duk abinda ze qara mun laifi a gurinsa ga zazzabin da yake damuna kullum qaruwa yake ga kuma sabuwar damuwar Bashir gaba daya na susuce har wata rama nayi,

A bakin Aliyu naji cewar Monday zuwa Laraba su Bashir bazasu yi aiki ba an basu hutu, nan da nan nima na rubuta letter akan bani da lafiya naci sa’a akayi mun approving da wuri dan daman duk wanda ya ganni yaga mara lafiya.

Nan da nan na shiga shirye shiryen yanda zamu gyarota da Bashir dan wannan zaman doya da manjan da mukeyi bayamun dadi kuma a zahiri na fishi cutuwa sedai nima qudurce a raina indai yana tunanin abinda yakeyi ne zesa na sakko na bi ra’ayin sa na ajiye aiki na na koma Gombe ya dakko wata Mata ya kawo nan to kuwa bazan chanza ba.
Chapter 56 · 0% Book details