← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 158

Sashe 77

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dana takurashi daga qashe yace dubu dari yayi niyar bada gudummawa nace sunyi kadan gadon nan fa dole shi ze siya mata haka dai ya haqura daga qarshe ya yarda yace na ranta masa kudin muka siya mata gado me kyau dan dubai a sannan ma dubu dari hudu muka siye shi irin nawa dana siya na chanza na dakina na mayar da na ciki dakin su Amna.

Hidimar da nayi ta kayan auran Amirah ko bikin Farida nake yi se haka dan wallahi bazan iya lissafa nawa na kashe mata ba a kayan Kitchen Anty Halima har fada ta ringa yi mun tace dangin miji nakeyiwa wannan hidimar a maimakon nayi musu gwaninta qarshe baki zan janyowa kaina suce da kudin dan uwansu nake wadaqa amma na toshe kunnena nayi mata.

Haka na tattara kaya rankatakaf aka kwasa a mota aka kai Gombe sannan muka ci gaba da gyaran Amarya kuma da shirin biki dan har dinkunan ta duk nan aka kawo na bawa sabon tailor da nayi ya yi mata dinkuna na daukar magana biki kawai muke jira.

Randa aka kai azumi na Ashirin da biyu Bashir yazo mun da Albishir din ya biya mana Umarah nida Yara Gaba daya kuma wai a gobe zamu tashi abin ne da kamar baze yuwu ba shiyasa be gayamun ba se yau da safe sannan komai ya kammala.

Nayi murna kuma banyi ba. Murnar da nayi ta tafiya Umarar ce da kuma yarana dukka gaba daya abinda na dade ina mafarkin yi inda naji rashin dadi kuma ba tare da Bashir zamu tafi ba dukda sati biyu zamuyi dakyar idan tarar da bikin Amirah qila ranar da aka gama zamu dawo amma.

Haka muka tashi hada kaya a daren dan ma tashin namu bana safe bane, ta waya na kira gida mukayi musu sallama washe gari tun safe Amirah ta fara tafiya Gombe, harda kukanta wai bana nan za'ayi biki gaskiya zataje ta cewa su Addah a qara sati se na dawo haka na rarrasheta ta tafi, mun samu delay najirgi dan haka se qarfe 7 na Magriba muma muka tashi zuwa qasa me tsarki muka bar Bashir shi kadai yana ta daga mana hannu.

Mun sauka qasar madina lafiya, sosai na kama ibadah ta dan ko kusa ban bari hidimar yara ta hanani ribatar goman qarshe da muka shiga ba. Kwanan mu biyar muka tafi Makka muka dauki Haramin umarar mu, bayan mun sauke nan ma a kullum ina Masallaci ina ibaduna, kwanan mu biyu aka sallace banyi sanya ba na duqufa sosai ina ta kaiwa Allah kokena. Adduata duk akan Iyayena, Yarana da Mijina tareda sauran Al'umar musulmi baki daya.

Ranar Juma'a data kama Lahadi zamu dawo Nigeria da yamma mun fita kasuwa da yara wayata dake cikin jaka ta ringa qara, seda muka shiga shagon nacewa Amna zu zagaya su dauki abubuwan da suke so kafin na dakko wayar na duba,

Rahma ce Amaryar Amiru da mamaki nake kallon tarin missed calls dinta gida shida se na fara qoqarin kiran ta dan tabbas nasan ba lafiya ba irin wannan kiran nayi sa'a kuwa ringing biyu ta amsa wayar.

"Maman Aliyu wane labari naji dan Allah kice mun ba gaskiya bane" ta fada ba tareda ta bari ko gaisawa munyi ba. Se naji gaba na ya fadi, daman dauriya nakeyi, a kwanakin kullum cikin faduwar gaba nake da quncin zuciya na rasa me yake damuna shiyasa ko da yaushe ina cikin Harami ina sallah ko karatun qur'ani su kadai suke sanyayamun zuciya na kuma fawwalawa Allah ya iya mun koma menene yake tun karo ni dan a duk sanda naji irin wannan yanayin to tabbas wani mummunan abu ne yake shirin samuna.

"Maman Aliyu bakya jina ne kin yi shiru k baki samu labarin abinda yake faruwa bane" Rahma ta sake fada abinda ya fito dani daga duniyar tunanin dana luluqa.
"Wani abun ne ya faru Rahma ban sani ba wallahi Allah dai yasa lafiya" na fada a sanyaye, se tayi shiru kafin cikin wani yanayi tace

"Tunda baki sani ba bazakiji a bakina ba Maman Aliyu amma ki kira Yaya Bashir yanzu base anjimaba kiji komai" kafin nace wani abu ta yanke wayar.

Seda na kira Bashir sau uku amma be daga ba, ganin magriba ta kusa sena haqura muka qarasa siyayyar mu muka koma masauki akan zuwa bayan Isha se na sake kiransa idan na dawo daga masallaci amma sam na kasa samun nutsuwar zuciya.

Kira na ringa doka masa abinda ya bani mamaki ko ince ya fara bani tsoro ganin na kira yafi sau Ashirin wayar tana qara amma ba'a daga ba sena mayar da akalar kiran nawa kan Amiru dan na sake kiran Rahman itama bata amsa ba.

Kira biyu ana ukun Amiru ya daga. Cikin sanyinsa muka gaisa se mukayi shiru gaba daya ni ina jira naji yace wani abu ne ya samu Bashir shima yana jiran jin dalilin kiran, ni na katse shirun da cewa

"Baba Amiru Bashir kunyi waya da Bashir kuwa yau"

"Eh mun yi waya bamu dade da rabuwa bama na barshi a gida yanzu na fita"

"Oh yana Gombe ashe, nayita kiran wayarsa ne amma ban samu ba shine nace bari na kiraka naji ko kunyi magana yau shikenan se an jima" na kashe wayar. Daga yanayin sa sam banji cewa wani abu ya faru ba to me yasa Rahma zata kira ta daga mun hankali??

Qoqari nayi na yakice tunanin daga zuciyata muka shirya muka tafi masallaci, ina cikin yin shafa'i da wutri wayata da sam na manta ban saka ta a Silet ba ta dauki qara lokaci daya gaba ya yanke ya fadi da har seda na dafe qirji na shiga nanata Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un a zuciyata.

Ina sallamewa na jawo wayar na duba, Alawiyya ce ta kirani, sena miqe kawai ina shirin bin bayanta wani kiran ya shigo sena yi saurin daga wa na saka wayar a kunnena.

"Ma'u bansan daga ke har mijinki yan kutumar uba bane se yau, anya ba asirce ki yayi ba kike zaune dashi ya kulle miki baki? yanzu ace za'ayi miki kishiya duk duniya ki kasa gayawa kowa sema ki tsallake kibar qasar wai kin tafi Umara sedai kawai muji a gari, shikenan ai Bashir ko gaki gashi nan tun ba'aje ko ina ba kin fara karbar saka makon ki a hannunsa".

A duk maganganun Alawiyya babu abinda na tsinta banda kalmar kishiya data fada, seda na da dage piller masallaci jin jiri yana neman kadani.

"Lallai wato ga mahaukaciya tana magana kin yi mun shiru ko Ma'u, shikenan amma ki tabbata kin nemi wata yar uwar da zaki raba baqin cikin Bashir da ita dan wallahi bazaki dora mun hawan jini da takaicin mijinki ba, mtsw" taja tsaki.

Seda nayi da gaske na iya bude baki nace
"Alawa ni duk ban gane abinda kike nifi bane waya gaya miki Bashir yayi aure?"

"Kina nufin baki sani ba to maza shiga whatsapp yanzu na tura  miki hotuna kigani se ki tabbatar wa idon ki" tafada kafin ta kashe wayar.

Wata wawuyar Ajiyar zuciya na sauke lokacin da naga hotunan da Alawiyya ta tura mun. Hotunan Bashir ne da Amirah tareda sauran yan uwan su wanda na tabbatar na daurin auran Amiran ne amma ai na zata se gobe Asabar aka saka a katin data tura mun kuwa.

Da daddaya na ringa binsu da kallo Bashir yaci uwar Babbar riga fara gasu Addah nan baki ya gonar Auduga an washe shi ina shirin bude na qarshe da naga kamar kati ne kiranta ya sake shigowa.

"Yanzu kin yarda ko kuwa dai kina tantama" ta fada".

"Haba Alawa haka kawai kin saka hawan jinin dare daya ya nemi kamani a marrar nan kike mun zancen kishiya. Amirah cefa kin manta da bikinta akeyi hotunan daurin auren nefa duk kika bi kika kidima kanki".

"Allah ya yafe miki Asma'u ya nuna miki hanyar daidai, shikenan tunda ni na kidima kaina ba lefi idan kika dawo hayyacin ki se muyi magana dan naga alamar kwakwalwarki ta juye Ma'u kina buqatar saiti amma ki nutsu ki sake kallon hotunan dakyau ga wasu can ma na qara tura miki" Alawiyya ta fada sannan ta yanke waya.

Hotunan na sake bi da sababbin Videos din data turo mun na Amirah data sha kwalliya tayi kyau suna ta shaqiyanci, akan katin dazu na sake tsayawa na bude shi na fara karanta abinda aka rubuta.

"DAURIN AURAN ENGINEER BASHIR AHMAD DA AMIRAH MURTALA" Abinda na gani an rubuta kenan, daga Bashir din har Amirah ko daga bacci na farka naga sunansu na san sune ballantana wannan ga gurin daura auran nan masallacin dake layin gidan Addah ne hakan ya sake tabbatar mun da gaske dai Nawa Bashir din ake nufi bawai wani na daban ba.

Wayar hannuna ce ta dauki qara, ban san ya akayi na daga kiran ba nidai naji muryar Anty Halima tana cewa

"Asma'u dagaske ne ko wasa yanzu a duniya Bashir ya rasa irin cin Amanar da ze yi miki se ya tura ki wata qasa sannan ya daura da yarinyar da kika riqe?"

Iya abinda naji kenan lokaci daya tsikar jina suka zuba  kaina yayi mun dum kamar wadda aka kwadawa guduma daga nan ban sake sanin inda nake ba se farkawa nayi na ganni a gadon Asibiti.

Waya ta da nagani a gefena na jawo na sake budo hutunan dazu dan in tabbatar gaskiya ne ko qarya. Ina kunna Data kuwa kamar ana jira messages rututu suka fara shigo mun alamar dai magana ta baza gari ga status din yan gidan su   Se a sannan ma naga status din Jama'a ashe an yi posting hotunan sosai hankali na nae bekai kai ba.

Tun yaushe aka shirya hakan? Daman Bahsir da Amirah suna soyayya ina zaune dasu ban taba ganin wata alama ba?

Wai ma me nayi wa Bashir a rayuwa dana cancanci irin wannan sakayyar bayan tarin dumbin sadaukarwa da Alkhairan da ni da yan uwana muka yi masa.

Wane irin mugun hali ne dani da har ya kasa gayamun zeyi aure sedai naji a duniya bayan daya rigada ya daura me nayi masa dan Allah?
Chapter 77 · 0% Book details