← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 158

Sashe 72

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nayi masifar nayi bala’in amma ko kallo ban ishi Bashir ba qarshe na fashe da kuka haka na kwana ina tunanin mafita a raina, idan nace zan jira naga abinda zeyi bana tunanin samun mafita daga gareshi dan ko an samu gidan nasan bashi da kudin da ze biya dan chanjin da za’a bashi ba isa zeyi ba qarshe dai ni din ni zanyi fafutukar yanda za’ayi.

Kafin safiya na yanke zuwa gurin Baffa na, shi kadai nake dashi da ze share mun hawaye masan kuma baze kasa sama mun mafita ba dan ko kusa ban hasaso rabuwa da Bashir ba akan wannan dalilin, gari na waye wa kuwa na shirya yara muka tafi gidan mu saboda haushi ko Bashir ma ban gayawa inda zani ba shima be tambayeni ba.

Kuka na fashewa Baffa daya zuba mun ido yana kallon yanda na lalace na fita hayyacine kamar wata matar qauye. Seda na gama lissafa masa matsalolina yana ji, murmushi yayi kafin yace

“Ko wanne aure da kalar qalubalensa Ma’u ayi ta haquri zan duba naga yanda za’ayi kafin lokacin da suka dibar mukun, tashi ko shiga cikin gida ku karya kin debo yara ga Sheik Jafar nan da gani bacci be ishe shi ba”.

Haka na wuni a gida ranar ina jin kamar kar na tafi duk yanda Na ringa shan zagi a gurin yan uwana kowa na fadar ni na jawa kaina.

“Ba kalar mutanen arziqin da basu zo kanki ba Ma’u amma kika nace se wannan Bashir din da ba mutunchi ne dashi ba. Ki ajiye maganar bashi da shi a gefe dan mu ba itace matsalar mu ba Aa girman kansa da yake hana shi fita ya nema shi ya jefa ku a duk halin da kuke ciki shi se aikin office zeyi ko ke ce yar wahala yana zaune ki fita ki nemo masa.
Se kije kiyi tayi, ina dai jiye miki ranar da dadi ze zo ya dakko miki yar tayin cin arziqi ta hanaki zaman lafiya idan ma be yar dake a sannan ba tunda kin gama masa aiki” Anty Zubaida Yayar mu ta biyu a Mata dana tarar a gidan ta gayamun.

Haka suka ringa gayamun maganganu kala kala wanda ko dar banji a raina akan Bashir ba, abinda na yarda na kuma amincewa zuciyata Bashir yana so na ba kuma ze taba juya mun baya ba dan haka zan taimakeshi da iya qarfina in har ni ina dashi.

Da zan tafi Goggo ta sake yi mun nasiha akan nayi haquri na zauna lafiya da mijina kar na yarda da abinda yan uwana suke gayamun. Allah sarki ita kadai ce take qaunar Bashir a gidan mu se ko Baffa da bazance ga bangaren da yake ba. Haka na koma gida ba tareda na cewa Bashir komai ba.

Kwana biyu a tsakani Baffa yace naje gida, a gaban Yayyena dukda suke gari da Iyayen mu ya mallaka mun takardun gida wanda aka siya da sunana sannan ya bani kudi naira miliyan biyu a sannan yace naja jari.

“Ku zama shaida nayiwa Asma’u kyautar wannan gidan sannan ga kudi nan taje suja jari ita da mijinta su riqe kansu”.

Haka na tattaro na dawo gida cikin dimbin farin ciki bayan Yah Abubakar ya karbe kudin daga hannuna yace naje nayi tunanin abinda zanyi dasu. Godiya sosai na ringa zuba wa na kuma qudurce a raina in sha Allahu bazan sake komawa gida da niyyar neman wani taimako ba.

Zanyi tunanin abinda zanyi da kudin ba kuma zan gayawa Bashir batun su ba gida dai gashi nan muje mu zauna a ciki.
Da na nuna masa takardun gidan ma kada ran kada han fuskarsa, washe gari mukaje muka ga gidan.

Sabon gida ne me kyau ginin zamani a cikin GRA Flat me dauke da Qaton palour da Dining se dakuna bibbiyu a cikin corridor hagu da dama ko wanne da bandakinsa a ciki ga qaton kitchen da store tsakar gidan kansa a qalla zeci mota uku zuwa hudu sannan ga dakin me gadi.

Ni kadai na ringa tsalle ina murnata Allah sarki Baffana Allah ya biyashi da Aljanna, tun a ranar muka fara kwashe kaya, a kwana na uku muka tare bayan da yan uwana da Abokanan Arziqi suka rakani kowa se yaba guri yakeyi yanda yayi kyau dan har kujeru da labulaye na sake.

Satin mu daya a unguwar na fahimci matsalar masu kantina da take damun gurin duk abinda kake nema seka fita can babban titi ko kaje kasuwa.

Ni da nake neman abinyi se na yanke shawarar bude provision store kawai dana gayawa Yah Abubakar shima yayi na’am da maganar nan da nan yasa aka fashe dakin me gadi aka sake ciyo filin cikin gidan aka yi babban shago a gurin.

Lokacin da nakeyiwa Bashir zancen muna zaune se yake cemun “ai kuwa hakan yayi dan kinga ko ni ma se na ringa zama a gurin kafin na samu wani abinyin”.

A lokacin ba qaramin dadi naji ba, dan daman tunanina kenan amma ina tsoron na gaya masa ya fassara maganar da wata manufa ko yace na rainashi shi yasa na yanke kawai zan sa a nemo min yaro da ze ringa zama tunda ga qofa anyi ta cikin gida na ringa leqawa naga yanda abubuwan suke tafiya.

Cikin dan lokaci aka hada shago sosai aka shaqe shi da kayan masarufi harda su ruwa da Lemo duk muka zuba cikin ikon Allah kuma ya samu karbuwa dan sosai ake ciniki kafin cikar wata biyu seda ya zamana har buhun huna muke siyarwa na kayan abinci da muka ga ana yawan tambaya.

Bashir ne yake zama se wani yaro Shafi’u dayazo yace ze ringa taya shi. A dan qasan mu yake maraya ne ake ruqonsa a gidan qanin Babansa sedai beyi sa’ar mariqiya ba ai kuwa na riqe shi sosai gashi da amana.

Shekarar mu daya a gidan na sake haihuwa yar mace da se naga kamar Bashir yafi yin murna akan ta sama da sauran haihuwar da nayi har na ringa tsokanar sa wai saboda an samu Dada ne yasa yake murna amma yace Aa shi ba sunanta ze saka ba.

A raina har na dauka ko ni zeyiwa kara ya saka Goggona se ji nayi ya mata huduba wai da Aisha Farida.

“Ni na zata Dada ko Goggo zaka saka ai” na fada bayan daya gaya mun sunan, se ya kalleni yace

“Bani da ra’ayin yiwa wani takwara, ko Aliyu da kuke zaton sunan marigayi Aliyu ne kawai ra’ayin kainane”.
Haka naci gaba da rainon Faridata dan tuni an saka Aliyu da Jafar Makarantar Boko da Islamiyya.

Nisan da mukayi dasu Addah be sa Amirah ta dena zuwa ba dan yawanci duk Juma’a se sunzo musamman tunda na haifi Farida wani lokacin ta kwana daya ko biyu wani sa’in ma ni zan kira Addah nace ta turo mun ita tayi mana kwana biyu dan yanzu ta fara zama yammata ta rage fitsara da rashin kunya abu daya yake hadani da ita qazanta da rashin son aiki dan in tazo se nayi da gaske take kama mun ayyuka ga bata guri haka zasu ci abinci su bata ko ina idan bani nace a kwashe ba sedai su zauna a cikin dattin.

Daman batayi mun raino qarqari ta in zanyi wani abun na ajiye mata Faridar ta kula da ita amma fa ko zata kwana tana kuka Amirah bazata goya mun ita ba bare naci arziqin tayi mun wankin yara ko yi musu wanka ba tayi to kanta ma se nayi dagaske take wankan bare tayiwa wani.

Watannin Farida Shida Allah ya karbi rayuwar Baffan mu sanadiyyar ciwon ciki da yayi na kwana daya har seda aka kaishi Asibiti inda acan ya rasu. Fadar irin tashin hankalin da muka shiga ma bata lokaci ne, munyi kukan rashin Baffa babban bango ya fadi se dai mu bishi da fatan Alkahiransa da halinsa na gari su bishi. Rasuwar Baffa da kwana Arba’in aka yi mana rabon gado kamar yanda ya bar wasiyya bayan an gama tattara komai kowa aka bashi kason sa.

Wannan karon ma ba’a bani komai nawa a hannuna ba dan ana gama rabon Yah Muslim ya danqawa Alhaji qarami nawa dana Amna. Bansan dalilin da yasa sukeyi mun haka ba, amma koma menene banyi magana tunda nasan baza su cutar dani ba.

Seda Alhaji qarami ya gama tsara duk yanda yake ganin yayi sannan ya sameni har gida wata rana yake gaya mun, mota biyu ya kawo mun cikin rabona yace gashi nan se na dauki daya na bawa Mijina daya. Na samu gonaki manya har biyu yace za’a ci gaba da noma su kamar yanda akeyi dabbobi na suma ze zuba mun su a gidan gonarsa.

Akwai fili manya guda biyu dana samu se ya bani shawarar tunda mun samu wani gida me flat takwas a Abuja aka raba mana ni biyu, Junaidiyya biyu se nasa guda hudu idan na yarda ayiwa kowanne kudi muyi musanye ya karbi filayen ya bani gida itama idan tana so ayi haka mu ringa karbar kudin hayar duk shekara dan a cikin gari suke nan take na amince na kuma bar masa duk sauran abubuwa a hannunsa yaci gaba da kular mana dasu kafin ya tafi ya turamun zunzurutun miliyoyin kudade na a account da seda jikina yayi sanyi da ganinsu.

Rayuwa kenan, shi wanda ya tara su yanzu tasa ta qare muma da muka samu wata rana haka zamu tafi mu barsu, shawara muka yanke akan gidan mu kar a tabashi, abar shi a yanda yake tunda kowa sun san kason su kowa mahaifiyarsu tana ciki sannan muka samu Qaton fili muka siya akayi Babbar Makarantar Islamiyya da masallaci Muka kuma bude foundation ta tallafawa Marayu da mabuqata me sunan ABDULLAHI TUKUR KUMO FOUNDATION ladan Allah ya kaiwa Baffan mu.
Chapter 72 · 0% Book details