← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 158

Sashe 100

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zugudi Amirah tayi da waya a hannu cikin tashin hankali, ciki dai cikin shege Ummi ta yi to yaushe hakan ta faru? Zama tayi akan gado ta rafka tagumi radadin da takeji a kunnen ma ya tafi saboda jin sabon tashin hankali yanzu me Alhajin su zece idan yaji wannan maganar ta tabbatar da sedai Allah ya tsare amma da wuya auran Addah be mutu ba a dalilin wannan abun amma.

Ummi ta cuce su koda yake ba Ummi ba Addah zatace ta cuci Ummi tunda babu yanda batayi akan ta barta ta auri wanda take so ba amma ta kafe cewar bazata aureshi ba saboda bashida komai, shegun da take yawan ambatarsu dashi gashi yanzu ya tabbata ai seta shirya goya shegen jika.

Wanann maganar ce ta kashe wutar abinda ya faru da safe, haka ta wuni jiki a sabule batayi musu girki ba daman yaran suna dawowa gidan Ma'u suka wuce shima Bashir daya dawo yaganta a yanda ya fita ya barta kwafa kawai yayi ya sake wanka ya fice be kuma dawo gidan ba se bayan data kwanta.

ASMA'U
Da safe ganin harna shirya yara basu shigo yasa nayi tunanin sun koma cin abinci a gidan su kenan, toh itama Amna ta huta, a tsatstsaye na karya dan ina sauri mukayi sallama da Amnah ina fitowa na gansu cirko cirko a qofar gidansu fuskar Aliyu dana kalla ta tabbatar mun wani abu ya faru.

A gabansu na tsaya da mota na sauke glass, dukkan su suka gaishe ni na tambaye su lafiya Jafar na shirin magana Aliyu ya galla masa harara yace mun babu komai. Sena tabe baki nace "toh yayi, ina Abbin naku kuke tsaye anan kun kusa makara fa" ina rufe baki na hango an bude qofar, nasan Bashir ne dan haka nayi musu sallama kawai na wuce haka nan bana son haduwa dashi kuma.

Gurin qarfe goma ina zaune a office wayata tayi qara, ta true caller naga sunan me kiran YUSUF IBRAHIM WUNTI ina gani na gane Yusuf ne dan haka na daga wayar na kara a kunnena tareda yin sallama.

"Barka da rana Hajia" Yusuf ya fada daga daya bangaren sena amsa da cewa

"Barka dai Excellency"
"Ashe baki manta sunan ba" ya fada yana dariya sena mayar masa da amsa da cewa
"Haba dai ya za'ayi na manta, waya sani ma ko sunan ya tabbata yanzu dan Majalissar Jaha ne kai ko na taraiyya?"

"Haba Hajjaju ai tuni muka tsallake nan, sanata nake meci a yanzu kuma Gomna me jiran gado in Allah ya yarda" Yusuf ya fada, sena bude ido da mamaki kamar yana kallona nace

"Dagaske amma babu labari ko a gurin Alaqiyya ban taba jiba ita da take yar garinku, toh Allah ya tabbatar da Alkahiri kace na kusa zama qanwar Gomna".

"Toh ai baki taba neman koda labari na kinga bazaki sani ba, duk kuma sanda zanje gida se muyi sabani ace kinso kin tafi shiyasa amma yanzu da Allah yayi zamu sake haduwa kinga a arha na ganki a hanya, ya gida ya yarana na shigo Lagos ya kamata nazo na gansu ki sanarwa da Oga kar nazo yayi mun rotse"

Yanda ya fadi rotsen seda nayi dariya nace "ba abinda zeyi maka ai yasan kai Yayana ne ko, ba damuwa toh yaushe zaka shigo?"

"Injiwa ta ya za'ayi ya yarda da wannan nima bazan fara shigar masa gida ba a waje zan tsaya ki turo mun yarana na gansu kar naje mun sha haduwa ma ban san su bane ko da yake bayanda za'ayi naga jininki na kasa ganewa, ina jin ko a taron Arfa naga wanda ya shafeki sena gane shi wallahi

Zan zo gobe da yamma, idan babu damuwa zan sa a kawo takwarar ki anjima kafin nazo kin san an kawota gurin Hajia to ban samu na shiga Bauchi ba ita kuma ta saka rigima se an kawota gurina, inaga na saka a kawota nan din dan idan aka kaita Abuja ma bani da lokaci acan saboda aiki"

"Ok ba damuwa a kawota, ba tare zasu zo da mamanta ba?" Na tambayeshi, a maimakon ya amsa mun se yace

"Shikenan se goben In Allah ya kaimu kiyi saving Number ta nasan yanzu ma qila sa'a naci kika daga tunda baki da ita"

"Ai naga sunan a true caller na gane kaine, Allah ya kaimu goben a gaida Madam" daga haka mukayi sallama.

Dana tashi a hanya naga wani boutique da suke siyarda rigunan yara masu kyau, na tuna gobe ne fa Graduation partyn su Amna jibi kuma suyi prom kuma Faridah bata da kayan da zata saka goben dan haka na tsaya a gurin na siya mata riga me kyau, har na gama na tuno da za'a kawo mun wata yarinyar dukda bani da tabbacin ze bar mana ita ne ta kwana a nan nace bari na siya mata.

A hoto dana ganta dai nasan bazata wuce tsahon Abdallah ba amma dan na tabbatar sena kira wayar Yusuf amma line busy

Text yayi mun cewar yana busy akwai wani abune?
Sena mayar masa da cewa menene tsahon Takwara da size din takalminta ba'a dauki lokaci ba ya turomun kuwa na siya mata kalar ta Faridan da takalmi harda su Ribbon dan naga tana da gashi kafin na wuce gida.

Ina zuwa na tarar dasu sunyi kaca kaca da gidan na kuwa hausu da Fada akan su gyara na wuce dakina ina shiga Jafar ya biyo ni a baya tas ya kwashe abinda ya faru dazu ya gaya mun.

Sosai raina ya baci akan abin, wane irin rashin hankali ne ze saka Aliyu ya daki Matar Babansa da ko bata aure shi ba matsayin uwa take a gurinsa cikin bacin rai nace ya kiramin shi na hadasu su biyun tunda sune manya nayi musu tatas nace kuma idan ya koma ya bata haquri sannan na kira sauran na tara su gaba daya na sake ja musu kunne akan duk wanda na sake jin ya mata ko kallon Banza ne se ransa yayi bala'in baci, haka na wuce daki na barsu Aliyu ya cika kamar ze fashe har na tafi na koma na sake masa warning akan karya kuskura ya taba Jafar dan nasan qarshe se ya huce haushin gayamun da yayi akansa.

Ina Wanka najiyo wayata na qara, da yaje na kammala sena dauro towel na fito kafin na daga ta katse sega wani kiran ya sake shigowa.

Yusuf ne, ina dagawa muka gaisa yace
"Gata can a waje sunzo amma taqi fitowa daga mota, dan Allah ko zakije ki lallaba ta idan kuma taqi su wuto da ita kawai nan bansan ya zanyi da ita bane meeting mukeyi nasan zan iya kai qarfe biyu ma kafin na gama".

"Zama ta yarda in sha Allah bari naje na gani" na fada kafin na kashe wayar. Dogon Hijab har qasa na zura na saka takalmi na fito har sannan yaran suna zaune suna kallo, Abdallah na ganin na fita ya biyoni, a qofar gida naga motoci guda biyu masu numfashi da wasu qarti su biyu a gaban daya daga cikin motar.

Number Yusuf na sake dialing tana shiga ya katse se naga wayar daya daga cikin qattin tayi qara ya daga da sauri kafin ya juyo inda muke se gashi da dan gudunsa ya taho gurin.

Cikin girmamawa kamar ze durqusamun ya gaisheni cikin harshen turanci kafin ya nunamun motar da take a rufe yace tana ciki.

Gaban motar na qarasa na kwankwasa super tint windown motar, kusan minti daya aka sauke shi wani ni'imtaccen qamshin yan gayu ya daki hancina har seda na lumshe ido kafin na bude fuskata dauke da murmushi na kalli cikin motar mukayi arba da wata farar mata irin fara fat din nan dan duk farina se na ganni na zama wata kala a gabanta siririya me dogon gashi da ta barshi a bude, a yanayinta ma zan iya kiranta da bauturiya ko kuma dai ruwa biyu amma ba hausa ko Fulani bace wannan.

Qara fadada fara'ata nayi, dan naga yanayin yarinyar Yusuf a fuskar ta dan haka na tsammaci itace matarsa, cikin harshen turanci na miqa mata gaisuwa dan bana tunanin wanann zataji hausa, ta amsamun a wani yatsine har seda abin ya sosamun rai nan da nan kuwa nima na datse fara'ar dan ban son wulaqanci a rayuwata.

Cikin yauqi da iyayi tace mun "kece Asma'u?"
Sena daga mata kai kawai ina kallonta ta waiwaya daya bangaren da bana hango wanda yake zaune tace
"Sweetheart kije ga Namesake dinki nan zaki zauna a gurinta, ki zama yarinyar kirki kinji"

Cikin muryar yara da kanaji kasan yaron ma sangartacce ne Yarinyar ta fara mana tana cewa
"Ni bazan je ba gurin Dady na zanje"

"Dadynki bashi da lokacin ki na gaya miki kece kike ganin yana sonki amma baya sonki sam, idan ba haka ba ya za'ayi ki taho tundaga United State amma ya kasa zuwa ya tare ki sema yace a kaiki gurin wata stranger ki zauna hmm" Matar ta fadawa yarinyar seka rantse da wata babba Sa'arta takeyi ni kuwa ina daga gefe ina kallon ikon Allah.

Wannan wace irin uwa ce me qoqarin turawa yarta wata aqida da zata sa ta tsani mahaifinta?
Ganin dramar bazat qare ba ya saka na zagaya daya barin da take, badan kar Yusuf yaga rashin kirki na bama qyale ta zanyi su tafi amma bansan dalilin sa na cewa a kawota ba tunda ga uwarta amma yanzun ma sau daya zan lallabata idan bata yarda ba su sauka lafiya.

Qofar na bude da murmushi na na miqa mata hannu seta dakata daga bubbuga qafar da takeyi ta zuba mun ido

"Muje ko kinga dare yayi Momy tana so ta tafi gobe da safe se na kaiki gurin Dady da kaina" na fada cikin lallashi, seta kalleni ta kalli uwarta data wani tabe baki ta dauke kai gefe, kai na gyada mata alamar tabbatar wa se kuwa gashi ta zuri qafafunta sena dagata na fito da ita daga motar ashe ma afili batafi girman Yan biyu ba.
Chapter 100 · 0% Book details