← Book details Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 158

Sashe 104

Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya sosai Yusuf yayi harda dukan sutiyari kafin ya kalli Bashir daya shaqa iya wuce ya nuna shi yace
"Oh wai akan Asmy kake magana daman ai cemin zakayi tsohuwar matarka se nafi ganewa.

Toh tunda anyi haka yanzu bari nayi amfani da wannan damar nayi maka jajen wautar daka tafka ka rabu da Mace kamar Asmy bayan ka manta akwai irin mu a waje da duk sallah biyar ta duniya da zamuyi a rana se mun roqi Allah ya bamu mace kamarta.

Nagode maka kwarai daka sako min ita a daidai lokacin da nake tsananin buqatar ta, na kuma yi maka alqawarin zan riqe Asma'u na bata kulawa da soyayyar daka gaza bata, kai amma ka tafka Asara yallabai se in ce maka Allah ya mayar da Alkahiri ko da yake naga ka samo wata me fada akan Abinci a gurin taro ko?

Irin matan nan in gaya maka ba'a zuwa gurin kunya dasu dan se sun zubar maka da mutunchi a ringa kallonka kamar baka yi musu komai Alhalin tsabar rashin godiyar Allah ne kawai. Kayi haquri fa amma dai dole in gaya maka kayi wauta Allah dai ya mayar da Alkahiri" yana gama fada ya dage gilashin motarsa yayi gaba yana cigaba da yiwa Bashir dariya.

Bashir kuwa tsabar yanda ya tafi wata duniya na wucin gadi besan sanda Yusuf ya bar gurin ba se qugin motarsa yaji. Ya juya ya kalli motar ya waiwaya ya kalli Gidan Ma'u wai ma takamaimai laifin wa ze gani anan.

Yanzu har Ma'u ta bawa wani dama ya maye gurbinsa a rayuwarta Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.

YUSUF
Wato rai fes sunan wata Atamfa haka ya ringa tuqinsa yana murmushi shi kadai idan ya tuna yana yin fuskar Bashir sanda yake gaya masa magana.

Tun ranar daya hadu da Ma'u da daddare yana sauketa ya kira Alhaji Tukur ya gaya masa yau ya hadu da Ma'u babu bata lokaci kuma ya sanar masa da zancen mutuwar
Wanda yayi bala'in yi masa dadi ya kuma jin jinawa wauta da hauka irin na Bashir amma daya tuna cewa Allah shi yake qulla aure ya kuma rabashi a sanda yaso se ya gode masa ya kuma tabbatar da Allah ne yake son sa shiyasa be sake hadasu shi da ita ba se a yanzu da take babu igiyar kowa akanta.

Yana sane yake nuna mata kamar besan komai ba dan yafi so ita da kanta ta gaya masa bata da aure a sannan ne ze dakko tsohon littafin soyayyarta ya karkade shi ya fara biya mata shafi shafi dan yayi alqawarin a wannan karon babu gudu babu ja da baya se inda qarfin sa ya qare amma se ya mallaki Asma'u kuma in sha Allahu rabonsa ce.

M&Z FASHION DESINGNERS
INA MATA YAN KWALISA
KU GARZAYO M&Z
FASHION DESNGNERS DAN SAMUN IN GANTATTUN KAYA MASU AMINCI.
IRINSU
ZANNIWAN GADO
TROW PILLOWS NA ZAMANI
TUM TUM
BABY SET
TOILET SET
KITCHEN SET
LABULAYE DA SAURAN KAYAN KWALLIYAR GIDA.
HARMA DA ATAMFOFI DA KAYAN KITCHEN AKAN FARASHII ME RAHUSA
KU NEMEMU AKAN LAMBAR WAYA 07064870087.08127423783.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 49

ASMA'U
Kai tsaye dakina na wuce sanda na shiga gidan ban ko tsaya jin Anty data tareni da tsokana ba na wuce. Seda na cire kayan jikina da naji kamar harda su gurin tare mun numfashi kafin na watsa ruwa na saka doguwar riga mara nauyi na fito har sannan tunanin Yusuf da kalamansa suna mun yawo a qwaqwalwa.

Anya kuwa Yusuf be san aurena ya mutu ba amma idan ya sani me yasa ze tsaya beyi mun maganar ba? Da wannan tunanin na dawo palour na tarar da Anty Hadiza ita kadai tace mun Anty taje gida ta dawo.

Hira muka shigayi da Anty Hadiza, itama ba baya bace wurin zance nan da nan ta shiga kwashewa Bashir Albarka.

"Ni wallahi naga qarfin halinsa irin yanda ya iya tsayawa a gaban mu bayan duk rashin mutunchin daya tatawa mutane, kinsan da Alhaji ya kirashi akan maganar ya bar miki yara me yace masa? Cewa fa yayi shi baze bar Yaransa a hannun Mace ba yana buqatar ya basu tarbiyya kiji dan abu ta kazan uba ko ina tarbiyyar take a gurinsu da yake iqirarin baiwa wasu oho.

Allah ne yaso ki ya rabaki da Shi tun yanzu dan wannan mutumin tantirin mara mutunchi ne wallahi qila da se kin kai shekarun da baki da yanda zakiyi ko yaka ki zeyi dole ki haqura ki zauna sannan zece ze sakeki.

Ni wallahi ma sena raina ajinsa dana ga ita matar so din, me mace kamar ki, da se ya bari idan ya auro wadda ta fiki sannan se yayi duk kadifirin rashin mutunchinsa amma yanzu ai baya yaci wallahi ba kuma ze taba maida kamar ki ba In Allah ya yarda"

Nidai "hmmmm" kawai nake ce mata dan har a sannan tunanina yana kan Yusuf ne, so nake na tambayeta ko sunyiwa Yusuf zancen amma sena dake, kai dole ma yasan da maganar nan qilan wani dalilin ya sakashi qin yi mun zancen dan haka zan saurara na gani zuwa wani lokaci.

Se qarfe bakwai na Magriba Anty Hadiza suka tafi bayan Alhaji qarami sun dawo gidan ya sakeyi mun nasiha tareda jan kunnen na kula da kaina na kuma kare mutunchi na a duk abinda zanyi.

Yusuf be zo ba be kuma kirani a waya ba, nima sena rabu dashi nasan dai baze wuce qila zuwa gobe yazo daukar Ma'u ba tunda litinin akwai makaranta dukda bansan a ina take karatun ba.

A bakin Farida da taje gidan su dakko abu naji Bashir bashida lafiya, ko me ya same shi oho nidai haka na kwanta ba tareda na sake bi takan maganar ba a dalilin haka ma ranar har yan biyu a nan gidan suka kwana.

BASHIR
Yana kallon motar Yusuf har ta bace masa kafin ya dafe kansa daya sara da hannu daya ya daga qafafunsa da sukayi sanyi ya wuce gida, a tsaye ya tarar da Amirah ta riqe qugu tana zazzagawq Su Aliyu da suka hada PS anan palour suna game su kuwa babu wanda ya ko daga kai ya kalleta abinda yake gabansu kawai sukeyi tana jin shigowar Bashir din ta juya cike da masifa tace masa

"Gara daka zo kai tunda Ubansu ne zasuji maganar ka. Idan banda iskanci da wulaqanci gardawa dasu zasu zo su zauna mun a palour harda wani qarin dorin dosano da suka samo sannan ina musu magana sun mayar dani kamar wata mahaukaciya sunqi kulani ai idan uwarsu ce bazasuyi mata haka ba".

"Amirah ki na gaya miki ki dena zagar musu uwa koh? Amma idan baki bari ba in sun rama karki kuskura kice zaki kawo mun qara, ki barsu suyi sabgarsu.

A sati sau nawa suke zama a gidan da har ze zama abin magana dan yau daya sun zauna a palour zaki zo kinawa mutane tashin hankali, dan Allah ki kyakeni na huta" Bashir ya fada kafin ya rabeta ya wuce, dakinsa ya shiga ya bude first aid box dinsa yana neman paracetamol dan sosai kansa yake masa ciwo amma be samu ba.

Palour ya sake komawa ya kwalawa Aliyu kira, Aliyun ya ajiye pad din game din ya tashi yaje ya same shi a zaune bakin gado ya dage kai da hannaye biyu.

"Aliyu idan kuna da paracetamol a dakin ku kawo mun idan kuma babu ga kudi nan ka dauka mota kaje pharmacy din tsallake ka siyo mun maganin ciwon kai" Bashir ya fada dakyar dan idan yayi magana ji yake kamar ana sara masa abu akansa.

Abin Da da uba duk yanda Aliyu yake jin zafinsa ganin yana yin da yake ciki seda ya sanyaya masa jiki, cikeda tausayi ya dauki muqullin motar Bashir din dan basu da paracetamol din suma, be dauki kudin daya nuna masa ba ya juya ya fita.

Baffan Abuja yacewa yazo ya rakashi nan da nan suka tafi, hana da kudi cikin wanda Bashir din yake basu ko Ma'u wani lokacin a ciki ya hado masa magungunan ya tsaya a wani gurin siyar da Abinci ya siyo masa sakwara da miyar Egusi da wani gashin nama da akeyi a kusa da gurin dan ya lura be ci wani abun kirki dazu ba kuma Antyn su batayi girki ba suka hado komai kafin suka dawo gida.

Sosai Bashir yaji dadin Abincin, yana ci yana sakawa Aliyu da yayi tsaye a gurin Albarka. Seda yayi nak yasha maganin ya kwanta kafin Aliyu ya barshi ya fita, yana bude qofa suka ci karo da Amirah zata shiga se yayi saurin tareta da cewa

"Bashi da lafiya ki barshi ya huta"

"Idan naqi fa ubana se ayi yaya?"

"Nidai na gaya miki ki barshi ya huta idan ba haka ba ai baki manta gamon mu sau biyu ba idan aka sake na uku se kin gane kurenki, sena cire miki haqori in yaso naga da bakin da zaki ringa yiwa mutane hayaniya a gida, tunda kika zo kin mayar mana da gida kamar kasuwa mu bamu saba ba" Aliyun ya fada yana sake daure fuska sosai.

Seta ganshi kamar Bashir dan kwabo da kwabo haka yake da Bashir har kuwa halin be baro ba sedai abinda ba'a rasa ba da kuma banbancin kwaba daga gurin uwa da suka samu, kwafa tayi dan tana tsoron Allah tana tsoron yaron nan bashida mutunci, na farko ya fasa mata goshi na biyu kunne tasan idan ta matsa dagasken yana iya sauke mata haqora kuma yaci bulus tunda ubansa babu matakin da ze dauka
Seta juya dakinta tana ci gaba da zage zage shima ya wuce gurin game dinsu ba tareda ya kulata ba.
Chapter 104 · 0% Book details